EPISODE 11

287 15 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭😭♥️*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

_Labari mai tab'a zuciya❣️_

Shafi na 11

Jabir kuwa fitowa yayi daga d'akinsa a fusace ya nufi d'akin Aliyu ya shiga bugawa da k'arfinsa yana huci, Aliyu wanda yake kwance a kan d'aya daga cikin kujerun falon nasa yana ji yayi banza sai ma kunna t.v da yayi ya kai tashar Arewa 24 inda ya tarar suna film d'in *Rud'in zuciya* duk da kasancewar shi ba ma'abocin kallon indian film ba ne amman yau dan ya musgunawa Jabir ya k'unna, kiran layin Abba ya shiga yii ringing d'aya biyu Abba ya d'aga "Assalamu alaikum aminci Allah ya k'ara tabbata a gareka yarona" wani irin murmushi yayi wanda yake d'auke da tsantsar jin dadi "Wa'alakumussalam Abbana kai ma haka, ya dubai d'in Abba yaushe zaka dawo ina son yin magana da kai kuma gaskiya maganar ba zai yiyu muyi ta waya ba" ya k'arasa magana cikin wani irin yanayi na bakin ciki, Abba tunda ya ji Aliyu ya ce akwai maganar da zasu yi yasan maganar tana da matuk'ar muhimmanci dan haka bai yi niyyar dawowa kwanan nan ba amman ya cewa Aliyu "Insha Allahu zuwa jibi zan dawo, amman kowa lafiya dai ko" Aliyu ya kasa d'aurewa hawaye ne ya shiga zubo masa ya share da hannunsa cikin muryar kuka ya ce "Abba Jabir ne, Jabir yana zubar mana da mutunci Abba  Jabir ya lalata rayuwar marainiyar Allah yarinyar da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciyarsa shi da Mami, Abba labarin yana da tsayi Abba dan Allah ka dawo gobe gidan nan yana shirin tarwatsewa, Mami, Nihal da Jabir gaba d'aya sun had'u sun lalata rayuwar yarinya, Abba in takaice maka Nihal yanzu yau kwananta uku bata gidan nan wai saurayinta ne yazo ya d'auketa suka fita" ya k'arasa magana yana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro, Abba kuwa sakin wayar yayi bayan ya gama jin duk bayanin Aliyu yanzu haka Asiya ta mayar masa da gida, ai kuwa babu shiri yasa aka yi masa visa zai biyo jirgin k'arfe biyar na yamma dan bazai ma bari ya kwana ba, Aliyu ya katse kiran sannan ya shiga kok'arin goge hawayensa.

Masu karatu na san zaku so kuji shin a ina Aliyu yaji ta'asar da Jabir ya yi wa Khadijatullahi, ba'a gurin kowa ya ji ba Shahida ce ta fad'a masa komai, domin lokacin da ya shigo gidan ya tarar da ita tana kuka da sauri ya k'arasa kusa da ita yana tambayarta menene, anan take ta zai yana masa komai da komai ta dora da cewa "Yaya Aliyu ina tsoron abin da Yaya Jabir ya yi wa Khadijatullahi ya faru a kai na ko Nihal saboda kasan ance duk abin da ka yi wa d'an wani to kai ma sai an yi wa naka, Yaya Aliyu kuma abin takaicin Mami da sanin ta Yaya Jabir yake yin komai amman bata tab'a hanashi duk abin da yake yi ganin dai-dai take yi masa" kuka yake yi sosai amman haka ya dake ya shiga rarrashin k'anwar tasa da kalamai masu dad'i sannan ya nufi d'akin Jabir d'in.

Jabir kuwa da ya ga Aliyu bashi da niyyar bud'e kofar ya koma nashi d'akin, ya zauna wayarsa ya zaro a aljihu ya kira number Teemarh kamar jiransa take ya kirawo ko ringing wayar bata yi ba Teemarh ta d'aga tare da cewa "Hello baby" Jabir cikin yanayin damuwa ya ce "Ina son kizo gida yanzun nan" ya fad'a tare da kashe wayar, murmushi Teemarh tayi sannan ta shiga wanka ta fito d'aure da d'an k'aramin towel ta shirya cikin wata 'yar yaloluwar rigar bacci wacce iya karta rabin cinyarta gaba d'aya rabin k'irjinta duk a bud'e yake shara-shara ce wacce ana iya ganin bra da pant d'in da ta saka wannan riga dai zan iya cewa da ita gwara babu, ko d'an kwali bata saka, ta baza gashin dokin da ta saka a kanta ya sauka har gadon bayanta, ta d'auki wata 'yar k'aramar jaka.

Haka ta fito tana taku d'ay-d'ay ta nufi baki titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen gidansu Jabir suka d'auki hanya, suna isa ta sauka ta biya mai adaidaita kud'insa ta nufi gate d'in gidan ta shiga kwan'kwasawa mai gadi ya bud'e mata kofar 'yar k'aramar gate d'in dan daman Jabir ya sanar dashi zai yi bak'uwa, haka ta shiga gidan tana wani rangaji daman gidan ba yau ta saba zuwansa ba dan haka ta san ko ina a gidan, Babban falo ta shiga ta tarar babu kowa kai tsaye d'akin Jabir ta nufa tana tura kofar ta ga a bud'e take dan haka ta shiga tana girgiza ko ina na jikinta, a kan gado ta tarar dashi a kwance, ta nufi gadon tana zuwa ta hau kanshi tana sumbatarsa, duk da irin yadda yake cikin bak'in ciki sai da yaji zuciyarsa tayi wasai sabida yasan Teemarh zata bashi jin dadi, haka ya murgina Teemarh ta koma k'asa shi kuma ya hau kanta ya shiga kissing d'inta tare da zame rigar jikinta, ya shiga tsotsar ko ina na jikinta (ni kuma 'yar mutanan zazzau nace Allah ya kyauta Jabir anji kunya anyi asarar rayuwa) haka dai sukai ta shek'e ayar su.

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now