EPISODE 18

274 14 0
                                        

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭🔱⚜️❣️*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

_Labari mai tab'a zuciya❣️_

*Alk'alami yafi takobi❤️*

Shafi na 18

"Nihal kamar yadda nasa aka shaida muku an d'aura aurenki yanzun nan to haka yake shiyasa ma nazo tare da mijinki domin ku tafi tare dashi" Amman yayi maganar cikin sanyayaryiyar muryarsa.

Hajiya Asiya tana kuka ta ce "haba Abban Jabir a ina aka tab'a yin haka, ka aurar da yarinya ba tare da ka sanar da ita ba, kuma maimakon ka bari ta fito da zab'in ranta kawai sai ka aura mata wannan matsiyacin" Mami ta k'arasa maganar cike da bak'in cikin mijin nata.

Alhaji Mansur ya ji matuk'ar zafin yadda ta ci mutuncin Salis d'in abin yayi matuk'ar k'ona masa rai amman ya da ke tare da cewa "Ai da ba'a san asalin balbala ba da sai ta ce daga madina take" yayi maganar yana harararta, Salis ma ya ji matuk'ar bak'in cikin yadda Hajiya Asiyan ta ce masa matsiyaci, amman zai tabbatar mata da cewa shi d'in matsiyaci ne a kan 'yarta, sai kuma yayi wani murmushi da ban san ma'anarshi ba.

Hajiya Asiya kuwa mutuwar zaune tayi jin abin da mijin nata ya ce mata tun da take dashi bai tab'a yi mata gorin cewa ita 'yar talakawa ce ba sai yau, tsoronta d'aya kada yaranta su gane cewa ita 'yar talakawa ce dan kuwa idan suka gane ba za ta tab'a yafewa Alhaji Mansur ba, ganin babu wanda ya fahimci abin da Abba ya ke nufi yasa ta sauke ajiyar zuciya a b'oye, tare da godewa Allah.

Muryar Alhaji Mansur ce ta dawo da Nihal daga dogon tunanin da take yi fuskarta shab'e-shab'e da hawaye, "Ke Nihal tashi taje ki shirya ki zo ku tafi domin k'afarki k'afar mijinki" haka Nihal ta mik'e jira na kok'arin d'ibanta ta fara tafiya tana dafa bango, Salis ya bi ta da kallo yana ra ya abubuwa da yawa a zuciyarsa, fuskarsa kuma har yanzu kunshe take da wannan murmushin nashi.

Nihal tana shiga d'akinta tayi saurin shiryawa dan tasan halin Abbanta idan ta dad'e sai ya shigo har d'akin yayi mata dukan tsiya, cikin wata atamfa coffe brown ko mai bata shafa ba ta yafa mayafi ta fito, Salis ya mik'e suka yi sallama da Abba da Aliyu ya saka Nihal a gaba suka nufi gurin da yayi parking d'in motarsa, ya bud'e mata murfin motar ta shiga wajen mai zaman banza, sannan ya mayar ya rufe ya zagaya mazaunin driver sai da ya kalleta ya ga fuskar nan babu alamar murmushi ta had'e fuskar nan kamar bata tab'a murmushi a duniya ba.

Salis yayi wani gajeran murmushi sannan ya ja motar mai gadi ya bud'e gate d'in gidan suka fita ya nufi gidansa gudu yake sosai a kan titin har suka isa gidansa, masha Allah gaskiya gidan ya had'u domin kuwa an zubda naira sosai wajen gina gidan, Nihal dai kallon gate d'in gidan take yi har mai gadi ya bud'e gate d'in gidan sannan suka shiga, a parking space yayi parking sannan ya fito ya bud'e mata murfin motar ta fito, hannunta ya kama da sauri ta shiga kok'arin kwacewa amman inaaa ta kasa saboda ya rik'e hannun nata sosai ta yadda ba za ta iya kwacewa ba, babu yadda ta iya haka ta barshi suka jera a tare suka shiga cikin madaidaicin falon, wata shirgegiyar mata ta gani a falon ga wani yaro shima k'ato gaba d'ayansu daga matar har yaron sun ba wa Nihal tsoro jikinta ya fara rawa.

Talatu tana ganinsu ta mik'e dakyar fuskarta a murtuke ta fara magana cikin bala'i da masifa "to ma ci amana ka yaudareni wallahi Allah ya isa tsakanina da kai kuma wallahi sai na ga mai wannan shegiyar yarinyar ta fini dashi da har zaka aurota a matsayin matarka" nan ta nufo inda Nihal take gadan-gadan, Nihal kuwa ganin ta nufota ta k'ank'ame Salis tana cewa "Dan Allah kayi mata magana ni bana so" Salis ya rumgumeta sosai sannan ya kalli Talatu wacce ta kai hannunta zata jayo Nihal cikin tsawa ya ce "ke Talatu ki shiga hankalinki idan ba so kike yanzun nan nayi k'asa-k'asa da ke ba" yayi maganar yana nuna ta da yatsa.

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now