*😭😭ĐÅŔĘŃ ÅÙŔĘŃÅ💔😭*
'''Łàbàŕį màį ťàbą žùçįÿą'''*Łábàŕį đà ŕûbùťáwą*
*Ńå*
*'Ÿåŕ mùťąń żàźźąù Ńââńâŕh M Śhâ'ábâń (Đįjąŕťÿÿ Łovę)*
08122188717*Follow me on instagram*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1vzbjbvm85fw3&utm_content=k2qerlb
*Follow me on facebook*
https://www.facebook.com/naanerh.mshaaban.3*ku nuna min soyayyarku ta hanyar yin join d'in k'ungiyar wambai writer's association na facebook👇🏽*
https://www.facebook.com/groups/342151527397807/?ref=share*Eid Mubarak 💞✨ Fans Ina yi muku barka da sallah da fatan an ci nama lafiya, aci nama dai a hankali kar azo a dinga ce min Dijartyy a kawo filajin🤣*
Shafi na 39
"Ruhina wallahi ba haka ba ne kai ma kasan ka na da matuk'ar muhimmanci gurina ina sonka ina tsananin k'aunarka Amman tunda ka ce haka insha Allahu zan dinga ajiye duk abin da nake ina kula da kai" Safwan ya ce "To shikenan tunda kin ce haka Ruhina Ina sonki nima fiye da yadda ki ke sona" Murmushi Safna tayi sannan ta ce "To yanzu ka huce ko Ruhina" Kai ya gyad'a alamar eh, tayi kissing d'insa a kunci tare da cewa "Shiyasa nake sonka mijina, to yanzu tashi muje ka yi wanka" Harararta yayi ya ce "Kiyi min wanka dai" Safna ta ce "to shikenan tashi muje nayi maka wanka" Tashi yayi suka shiga d'akin Safwan d'in, toilet suka shiga tare su ka yi wanka sannan suka fito kayan bacci suka saka sannan suka kwanta bacci.
_Yau fa kuyi hak'uri ba zan yi typing mai tsayi ba saboda zan je na ci naman sallah🤣_
*'BANGAREN KHADIJATULLAH DA ALIYU💔💃*
Yau an tashi da ruwan saman tun asuba ake yi sai wajen k'arfe 11:00am na safe aka tsaya Khadijatullah ta fito tsakar gida ta tsaya bata da wani buri irin ta ga Aliyu ya fito ta kalleshi ta ji dad'i a zuciyarta, Amatullahi ce ta fito daga d'aki tana kallon Khadijatullah fuskarta kunshe da murmushi dafa Khadijatullah tayi ta ce "Dijan Yaya Aliyu meya faru?","Bakomai Bestyna me ki ka gani kike tambayata?" Amatullahi ta ce "Kawai dai na ga Mata ta fito tana jiran mijinta ya fito" Harararta Khadijatullah tayi sannan ta shige falon Dan ta San indai ta tsaya to Amatullahi sai ta k'ureta, Amatullahi ta bi bayanta tana yin dariya ciki².
Aliyu kuwa bacci yayi tayi dan sai wajen 11:45am ya tashi ya shiga wanka ya shirya cikin wani yadi mai tsada green colour, ya fito ya nufi falo domin ya gaishe da Hajiya Mama kuma ya ga sahibarsa, Yana shiga ya tarar da Hajiya Mama zaune a kan kujera tana kallon labarai ita kad'ai ce "Assalamu alaikum" Hajiya Mama ta d'ago tana murmushi tare da amsa masa sallamar ta sa "Wa'alaikassalam" Zama yayi a k'asa wajen k'afafuwanta "Ina kwana Hajiyata","Lafiya k'alau d'an albarka ka tashi lafiya" Aliyu ya ce "Lafiya alhamdulillah Ina su Amatullahi ko sun tafi makaranta ne?" Hajiya Mama ta ce "A'a yau ai lahadi ba su je ba suna cikin d'akinsu" Aliyu ya ce "Ohh haka ne fa" Daga nan suka zaune suna yin hirarsu irin ta jika da Kaka.
Khadijatullah wacce tunda Aliyu yayi sallama take son ta fito Amman ganin idanuwan Amatullahi a kanta yasa ta share rumgume take da Affan a hannunta gaba d'aya hankalinta Yana wajen Aliyu, mik'ewa tayi ta nufi hanyar da zata sadata da falon taji muryar Amatullahi tana cewa "Ina za ki je kuma bayan muna hira","Zan je gurin Hajiya Mama" Ba ta jira abin da za ta ce ba ta fita da sauri.
Shahida tayi murmushi ta ce "Sister kin ga Allah ya amshi addu'armu sister ta fara son Yaya Aliyu Haidar" Amatullahi ta ce "Hakane kam dan d'azu ma jiransa ta fita yi a waje shine na je na fatattakota" Dariya Shahida tayi sosai sannan ta ce "Kaii Sister ki barta su soye abin su mana ke kuwa" ita ma dariyar tayi ta ce "To na barsu Sister Shahida" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu ta duniya.
Khadijatullah tana fita su ka yi ido biyu da Aliyu murmushi ya sakar mata, nan ta ji wani irin dad'i ya tsarga mata cikin jijiyoyin jikinta, zuciyarta kuwa ta cika da farin ciki, Zama tayi a kan kujera tare da sunkuyar da kanta "Sannu da hutawa Hajiya" Ta fad'a kanta a sunkuye "Yawwa Khadijatullah ya babana har yanzu bacci ya ke yi?","A'a ya tashi idonsa biyu" Hajiya Mama ta tashi tare da zuwa gurin da Khadijatullah take zaune ta karb'i Affan d'in sannan ta shige bedroom d'inta, Shuru falon ya d'auka na tsawon mintina 10 babu Wanda yayi magana a cikin su Aliyu ya kafeta da kyawawan idanuwansa Yana k'ara jin k'aunarta na shiga zuciyarsa, Khadijatullah ta ce "Ina kwana" Murmushi yayi sannan ya amsa "Lafiya alhamdulillah Gimbiyar Mata yau Kuma rowar kyakkyawar fuskar nan ake min ba'a d'ago a kalleni ba","A'a ba rowa nake maka ba" Tayi maganar cike da jin kunyarsa, Amatullahi da Shahida ne suka fito tare da zama kusa da Khadijatullah "Muma ba za'ayi ba mu ba, mun zo a koya mana soyayya" Amatullahi tayi maganar tana kallon Khadijatullah.
Aliyu ya ce "Kun zo dai kawai ku takura mana, muna cikin soyayyarmu, idan soyayya ku ke son koya kowaccenku tayi zuciya ta samo saurayi mana gauraye kawai bamashinshini" Yayi maganar Yana dariya, Shahida ta ce "Laaa Yaya Aliyu Haidar mu ne gaurayen? Gaskiya ka taro match" Amatullahi ta ce "Fad'a masa dai dan kuwa ya taro babban match" Aliyu ya ce "Ahh abin na d'an sauk'i ni da nake da messi, please ku tashi ki bamu waje kun ji darling sisters" Tashi su ka yi Amatullahi ta ce"To zamu ba ku guri ku zanta Amman fa ba mu hak'ura ba" Aliyu ya ce "To na ji" Fita su ka yi tsakar gida suka zauna a kan taburma, Khadijatullah suna fita ta d'ago kai ta kalli Aliyu sannan ta ce "Kaii Yaya Aliyu Amatullahi rigimarta tayi yawa na san ita ta giggib'o Sister suka fito" Dariya yayi sosai sannan ya ce "Bar ni da su ai na fuskanci takura mana suke son su fara yi" Murmushi tayi ba tare da ta ce masa komai ba, nan Aliyu ya shiga kashe Khadijatullah da kalaman soyayya masu ratsa zuciya da jinin jiki.
_Ni kuma na ce Bari na bar ku haka Masoya na rankaya gidan Nihal da Salis iyayen soyayya🤣💃_
*'BANGAREN SALIS DA NIHAL💕💖*
Kwance take a jikinsa tana ta zuba masa shagwab'a iri-iri, shi kuma sai lallab'ata ya ke yi kamar wata kwai "Babyna ni gaskiya ba zan yarda ba, sai mun je tare Allah ba za ka bar ni a gida ba idan kuwa ka fita wallahi kuka zan tayi Kuma har ka dawo ba zan daina ba" Salis ya ce "Haba babyna so kike zuciyata ta buga, tunda haka ne to ni na hak'ura da fitar ma tunda daman yamma tayi" Murmushi Nihal tayi tare da cewa "Da gaske ka ke babyna" Salis ya ce "Eh mana Baby Nafisa kuma Baby Nihal Kuma Babyn baby" Dariya tayi sosai ta ce "Sweetheart duk ni kad'ai wannan sunan, to nagode sosai Babyn baby, can't love you less" D'aukarta yayi kamar wata jaririya suka shige bedroom suka rufe kofa.
_ni kuma er sa ido na ce sai na bi su na ga me za su yi Amman kuma sun kulle kofar da key🤣sai na yanke shawarar kawai nayi gidan Teemarh da Jabir😂_
*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂💖*
Teemarh tana kwance tana jiran dawowar Jabir ganin har k'arfe 12pm na dare bai dawo ba, ta kifa kanta da guiyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita, dan ta san Jabir yana chan yana shek'e ayarsa da yammata dan kuma hausawa sun ce Mai hali baya fasa halinsa, ji tayi an dafata da sauri ta d'ago rinannun idanuwanta ta zubawa Wanda ya dafatan Jabir ne da sauri ta ture hannunsa tare da juyar da fuskarta jefe ta cigaba da yin kukanta, Jabir kuwa duk da cewar baya son Teemarh Amman sai da ya ji hankalinsa ya tashi Dan ya San dalilin kukan na ta ba zai huce na rashin dawowarsa da wuri ba.
Zama yayi kusa da ita tare da kok'arin jiyo da fuskarta, Amman tak'i yarda sai tureshi ta ke yi da ya gaji ya mik'e tsaye tare da d'aukarta cak sannan ya koma ya zauna a kan kujerar Yana rumgume da ita a jikinsa, Teemarh tai-tayi ta kwace Amman ta kasa tana kuka ta fara magana "Tunda ka nuna min ba ka k'aunata kuma ka tsaneni kawai ka rabu da ni ka sakeni na koma gidanmu" Tayi maganar tana cigaba da tureshi, Jabir ya k'ara k'ank'ameta sosai a jikinsa yana cewa "Haba Darling wane dak'ik'in ne ya fad'a miki na tsaneki kuma ba na sonki da har ki ke cewa na sakeki ai darling ni da ke mutukaraba babu mai rabamu dan ko mutuwa ma tare da za mutu da ke please ki tsaya ki saurareni kin ji","Me zan saurara daga bakinka na san club ka je gurin yammatanka ka fad'a min me na rageka dashi ko kuma me suka fini dashi, kyau ko kuma surar jikin ko Kuma......" Bakinta ya toshe mata "Ba su fiki da komai ba darling kuma wallahi ba Wai na je club Dan"........"Dakata Jabir ba na son jin komai daga bakinka".
Da k'arfi ta fisge jikinta daga na shi ta fad'a kan gado tare da rushewa da wani irin kuka Mai cin rai, Jabir ya tashi ya koma kan gado Yana cewa "Darling ki daina kukan nan haka Dan Allah kinji babyn Jabir"
Cikin zafin nama Teemarh ta mik'e daga kwancen da take tana cewa...............
_Lefin dad'i k'arewa😂🙏Afwan fans zan je na zaga kun san kwana biyu fa babu kanta🤣🤣ku kawo min filajin😂_
*Please🙏*
*Share👏🏽👏🏽*
*'Yar mutanan zazzau ce💔*