EPISODE 31

251 12 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA💕💕💕💕💕💕💕*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanarh M Sha'aban💕*

_Labari mai tab'a zuciya💕_

*Alk'alami yafi takobi⚔️*

Shafi na 31

"Dija me jaririn nan yayi miki, dan manzon Allah karki hukuntashi a kan laifin da ba na saba, ki sani fa shi yaro ne k'arami bai san meyafaru a tsakaninki da Yaya Jabir ba, ida da ace yaron nan zai girma a bashi labarin irin abin da Yayana yayi miki to wallahi sai ya fi ki shiga damuwa, tunda an wulak'anta masa mahaifiyarsa, dan Allah Dija ki karb'eshi ki shayar dashi kar ya mutu". Ya k'arasa maganar cikin yanayin tashin hankali zuciyarsa cike da bak'in cikin Halin da Khadijatullahi take cikin yanzu musamman da ya ga hawaye na zubowa daga idonta duk sai ya ji ya tsani duniyar da abin da ke cikinta, domin kuwa ya tsani ya ga tana kuka.

Karb'ar yaron yayi daga hannun Hajiya Mama ya mik'a mata, tare da cewa "Dan Allah ki tausaya masa ki bashi abinci kar ya mutu","ba na son shi" Amin da ace kenan tana kuka, "to na ji bakya sonshi, ina son ki shayar da yaron nan na wata bakwai ni kuma nayi miki alk'awarin ki fad'a min komai kike so zan yi miki shi" Kallonsa tayi tare da d'an tsagaitawa da kukan na ta "da gaske", kai ya gyad'a mata alamar "eh".

"Ina son Jabir ya wulak'anta, ina son yayi mutuwar da ko gawarsa ba za'a iya ganewa ba, sai ana tattaro naman jikinsa saboda irin yadda ya ragargaje kuma..............." Saukar marin da Aunty Murja tayi mata ne, yasa ta rik'e gurin kuma ta kasa k'arasa abin da take son ta fad'a kuka ta saka tare da yunk'urin tashi Aunty Murja ta hankad'ata ta koma ta zauna ta karbi yaron daga hannun Aliyu ta dora mata a cinyarta "ga shi nan idan kin ga dama karki shayar dashi, tunda ke kwata-kwara baki da hankali ki je ki yi duk abin da zaki yi dan kin ga an zauna ana lallab'aki to dan manzon Allah karki shayar dashi ki barshi ya mutu shashasha kawai mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta fita ta zauna a kan taburma a tsakar gida wani irin haushin Khadijatullahi take ji, saboda irin maganganun da tayi a gaban 'yan uwan Jabir d'in.

Amatullahi ta kalleta tare da cewa "Ai kin huta tunda har kin sa Aunty Murja fushi saboda wannan bak'ar zuciyar ta ki ai sai ki yi ta yi, dan Annabi tsabar tsanar da kike yi wa Jabir ki kashe jaririn idan kin kashe shi, shi ba asararsa ba ce, tun da bai san ma kina yi ba kuma ko yau jariri ya mutu ko a jikinsa, amman ki yi abin da kika ga dama tun da haka kika zab'arwa kanki".

Ita ma Amatullahi fita tayi kusa da Aunty Murja ta zauna tana raya abubuwa da yawa a ranta, tana son d'aukarwa bestyn ta ta fansar abin da Jabir yayi mata dan yanzu ma shirin da take yi kenan, amman yau bestyn ta ta taba ta haushi sosai, saboda Amatullahi ranta yana matuk'ar son jaririn dan har suna ta bashi Affan dan da haka take kiranshi.

Khadijatullahi kuwa kukanta ya k'ara sauti tana kallon Aliyu shi ma d'in ita yake kallo, yana durkushe a gabanta, "ka ce musu zan shayar dasu su yi hak'uri ba zan k'ara ba","to idan kina son na fad'a musu to ki shayar dashi yanzun nan dan na fad'a musu, kuma na basu hak'uri, kin ga sai kuka yake yi" Aliyu ya fad'a idanuwansa na cikin na ta.

Kallon jaririn take yi wanda sai tsala kuka yake yi ta saka shi a cikin hijabinta sannan ta shiga shayar dashi, shuru Affan yayi yana tsotsar abincinsa, Hajiya Mama,Nihal,Shahida da Aliyu ajiyar zuciya suka sauke tare da godewa Allah da Khadijatullahi yau ta shayar da Affan.

Tashi Aliyu yayi gurinsu Aunty Murja yake basu hak'uri kuma ya fad'a musu Khadijatullahi yanzu haka tana shayar da Affan ne, sun ji dad'i sosai suka tashi suka shiga d'akin Khadijatullahi tana ganinsu ta saka kuka tana cewa "dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min na dena" Zama Amatullahi tayi kusa da ita tare da rumgumeta ta ce "Ai yanzu komai ya huce indai zaki dinga kular mana da Affan d'inmu babu wanda zai dinga jin kanmu","Hakane kam indai kina so mu shirya to ki kula da Affan amman wallahi na k'ara jin kina tsangwamar yaron ko kina cewa bakya sonshi to wallahi idan na tafi ba za ki sake ganina ba" Aunty Murja ta fad'a fuskarta babu alamun wasa.

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now