*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😰😰😰😰😰😰😰😰*
_Daga alk'alamin✍🏾_
*'yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban**Wattpad@Naanarh2021*
_Labari mai tab'a zuciya_
Shafi na 6
Malam Kalla tunda Alhaji ya tafi ya zauna yayi shuru tabbas yayi matuk'ar farin ciki da har Alhaji Mansur ya ga d'iyarsa ya nuna yana sonta, Amman yaso ace daga d'aya daga cikin 'yan uwan Asiya ya gani ya ce yana so ba Asiya ba, domin Asiya sam bata dace da Alhaji Mansur ba, Macece mai girman kai da nuna isa bata ganin kowa da mutunci hatta shi da yake mahaifinta bata ganinsa da mutunci gashi uwa uba bata da kamun kai kwata-kwata, amman bazai so ace shi da kanshi ya aibata 'yarsa ta cikinsa ba, shiyasa bai nunawa Alhaji Mansur komai ba, kila idan Allah yayi ta sanadiyar Auren da zata yi ta shiryu ta dena duk abin da take yii, a haka dai ya yi ta tunane-tunanansa har a kai sallar magriba ya tashi ya nufi masallaci, anan idarwa ya dawo gida kai tsaye d'akin mahaifiyar Asiya ya nufa, zaune ya tarar da Asiya a kan 'yar yaloluwar taburmar d'akin tana taunar cingum tana danna waya, sallama yayi ya shiga d'akin amman Asiya ko d'agowa ta k'allesa ba tayi ba, baran tana ta amsa sallamar, sai mahaifiyar Asiyar ce wacce take tankad'an garin masara ta amsa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa, ya amsa da yawwa sannan ya samu guri ya zauna, ya fara koro bayani.
"Alhamdulillahi! Alhaji Mansur wanda yake zuwa gurina shine yau yazo min da maganar da ta sakani cikin farin ciki", cikin murna da farin ciki Inna ta ce "Wace magana ce wannan malam", "Wace yayi yana son Asiya zai aureta" ai kafin Malam Kalla ya k'arasa maganar Asiya ta mik'e tsaye cike da farin ciki, daman ta dad'e tana fatan Allah ubangiji ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta domin kuwa tunda taga yana zuwa takanas yana yiwa mahaifinta alheri ta san ba k'aramin Attajiri bane shiyasa duk inda ta ganshi take tsugunawa har k'asa ta gaishe sa, gaba d'aya taji ta fara kyankyamin d'akin nasu ta fara magana cikin rashin girmamawa "Ai daman nasan zance yana sona domin na had'a dukkan abubuwan da ko shugaban k'asa ne ya ganni sai ya ce yana sona, daman na sha fad'a muku ni ba matar talakawa bace ai yanzu kun fara ganin gaskiyar al'amarin, kuma wannan gidan bai dace ace nii Asiya irin yadda nake da kyau ace ina zama a cikinsa ba, na de kusan na fita daga cikinsa na rabu da k'aya, ba zan sake gangancin k'ara shigowa ba". ta k'arasa maganar tare da fita daga gidan da sauri tana toshe hanci (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace daga baya kenan😂).
Wani irin kuka Inna ta fara yi tana cewa "na shiga uku ni Indo ya ubangiji meyasa ka jarabceni da yarinyar da bata ganin mutuncinmu ni da mahaifinta", cikin muryar rarrashi Malam ya shiga bata hak'uri, har ya samu tayi shuru, Malam Kalla da Indo aure gida aka yi musu kasancewar iyayensu sun yaya da k'anine, tun daga ranar da ya aureta yake nuna mata soyayya har kawo yau da suka haifi 'ya'ya hud'u dashi kuma duka mata Asiya ce babba sai mai bi mata Hauwa,Hafsa, Hajara sai kuma k'aramarsu Na'ima, sam Malam Kalla baya k'aunar ganin bacin ran matar tashi ko kuma ganinta cikin damuwa shiyasa sam yake jin zafin 'yar tasu Asiya saboda kusan kullum sai ta saka Indo hawaye.
'bangaren Asiya kuwa tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, a wani k'aton super market ya sauketa daman ta akwai ragowar kud'in da ta d'auka a jakar Inna naira 200 ta bashi ta nufi super market d'in, tana zuwa bakin kofar shiga super market d'in masu gadi suka hanata shiga, anan take ta k'ara jin haushin Mahaifiyarta da bata tsaya ta auri mai kud'i ba ta auri wannan matsiyacin Malamin, ta san yanzu da sun ganta da kaya mai tsada basu isa sun hanata shiga ba,amman kuma da ta tuna gurin wanda tazo kuma zata aura anan ba da dad'ewa ba, sai ta ji wani farin ciki ya lullub'eta, "Hmm da kun san wanda zan aura ba zaku tsayar dani,ku hanani shiga ba", d'aya daga cikin masu gadin ya ce "to mu ina ruwanmu da wanda zaki aura" Asiya ta bud'e baki zata yi magana kenan ta hango Alhaji Mansur ya nufo kofar fita daga super market d'in, cikin farin ciki da jin dad'in ganinshi ta shiga gyara mayafin dake jikinta, Alhaji Mansur yana fitowa idanuwansa suka sauka a kan masoyiyar tasa a nan take wani farin ciki ya lullub'esa "Asiya!" ya kirawo sunanta cikin wata iriyar murya,wacce take d'auke da wani irin salo, "Na'am Alhaji" tayi maganar cikin yauk'i da yanga, "Me kika zo yi anan" murmushi tayi tare da cewa "Bakomai" tayi maganar a takaice, "To shikenan muje in kai ki gida ko?" yayi maganar tare da yin gaba, ta bisa a baya kamar wata gela (ni kuwa 'yar mutanan zazzau naje Asiya ko kunya baki ji ba🤔).
