*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭😭😭*
_Daga Alk'alamin_
~*Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*~_Labari mai tab'a zuciya❣️_
Shafi na 12
Hajiya Asiya ta mik'e tsaye jikinta har rawa yake "shikenan yau ta faru ta k'are kashinta ya bushe" ta fad'a a zuciyarta Jabir kuwa da sauri ya ture Teemarh daga jikinshi jikinsa na b'ari, ita kuwa Teemarh ko a jikinta sai ma gyara jikinta da take yi, Abba kuwa yana zuwa ya d'auke Hajiya Asiya da wani wawan mari hagu da dama ji kake tas! tas!! tas!!! Sai da ya yi mata mari yafi goma sannan ya kama wuyanta ya shak'e shi sosai dan har ta fara kok'arin shid'ewa, Alhaji Mansur bashi da saurin fushi amman idan har ka sake yayi fushi to ka shiga uku domin bai iya fushi ba, Jabir cikin rawar murya ya ce "Abba karka kasheta Mami ce fa" ai bai san sanda yayi wurgi da Hajiya Asiya ba taje ta bugu da hannun kujera ta fad'i kasa sumammiya, Alhaji Mansur ya koma kan Jabir ya shiga dukanshi ta ko ina komai ya d'auka maka masa yake, Shahida ce ta fito daga d'akinta da gudu dan jin hayaniya a falon ganin Mami a k'asa Abba kuma yana d'aukar komai yazo masa a hannu yana makawa Jabir yasa ta kwalla wani irin ihu dai-dai lokacin Nihal ta shigo gidan cikin shigarta wacce sai ka rantse ba musulma ba ce, ai kuwa Aliyu yayi kanta da duka tana ihu ya gwara kanta a jikin bangon d'akin ta fad'i kasa kanta yana fitar da jini amman Aliyu bai kyaleta ba haka yayi ta dukanta kamar Allah ya aikoshi, Shahida ta rasa ya ya zata yi da ranta duk ta bi ta rud'e ruwa ta d'auko a fridge mai sanyi ta shek'awa Mami, ta farka a jijice tana kuka, Shahida ta koma gurin Abba tana rokonshi da ya dena dukan Jabir domin kuwa duk ya farfasa masa jiki ko ina na jikinsa jini yake fitarwa, da kyar ta samu Abba ya bar Jabir ta rik'eshi tana bashi hak'uri, Teemarh da taga gidan ya hargitse ta nufi hanyar fita da sauri domin kuwa tana tsoron kar kuma su juyo kanta, Abba cikin kakkausar murya ya tsayar da ita "Ke tsaya anan" tsayawa Teemarh tayi jikinta na rawa domin kuwa ta ji tsoron irin dukan da ya yiwa Jabir d'in, Shahida kuwa gurin Aliyu ta nufa "Yaya Aliyu dan Allah kayi hak'uri ka kyaleta please darling brother" tayi maganar cikin kuka, Aliyu ya je ya nufi kan kujera ya zauna zuciyarsa cike da bak'in ciki, da kyar Shahida ta iya d'aga Nihal dan kuwa Nihal ta gama galabaita bata iya tsotsi da jikinta numfashin ma dakyar take iya fitarwa, kusa da Mami ta zaunar da ita, ita ma ta zauna Abba kuwa yana tsaye cikin muryar da take nunawa yana tsantsar bakin cikin ya fara magana "nagode da irin yadda kuka mayar min da gida, gidan karuwai, amman ku sani daga yau ba zaku sake yin gangancin mayar min da gida na karuwai ba, ya nuna Jabir da yatsa sannan ya ce "nayi nadamar haihuwarka kuma nasan duk irin tarbiyyar da kake kai a yanzu uwarka ce ta dora ka a kai, dan haka nan da wata d'aya za'a d'aura aurenka da wannan yarinyar" ya nuna Teemarh da yatsa, wani irin farin ciki ne ya lillib'e Teemarh Jabir d'inta zai zama mallakinta, Jabir kuwa gabansa ne yayi mugun fad'uwar cikin muryar tashin hankali ya ce "Abbah dan Allah dan manzon Allah kayi hak'uri Teemarh ce fa, wallahi ba zan iya aurenta ba karuwa ce ta gama zubar da mutuncinta, duk wani d'an iska na garin nan babu wanda bai santa a mace ba, ni na yarda ka aura min duk wadda kaga dama amman dan Allah ban da Teemarh".
Teemarh ta kalli Jabir tana cike da mamakin kalamansa yau Jabir ne yake kiranta karuwa kuma yake cewa ba zai aureta ba, bayan shine mutum na farko da ya fara saninta a 'ya mace cikin muryar kuka ta fara magana "Lallai Jabir tabbas na yarda da cewa kai d'in macuci ne mayaudari ne kai har kana da bakin da zaka kirani da karuwa bayan kai ne ka fara lalata min rayuwa Jabir wallahi kai ba mutum bane kai shad'an ne, ko shad'an ba zai tab'a aika irin wannan abin ba" cikin tsawa Abba ya dakatar da ita "Ke ya isa haka, kai kuma d'an uwarka aure kamar anyi an gama". Fita Teemarh tayi daga gidan tana kuka mai ban tausayi, Jabir ya nufi d'akinsa zuciyarsa cike da tashin hankali tabbas zai bi ko wacce iriyar hanya domin ya ga bai auri Teemarh ba, Abba ya juyo kan Nihal yana nunata da yatsa "kema d'an uwarki ki shirya aure zan miki domin ba zaki jawo min magana ba shegiya 'yar gidan gantalalliya" yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi d'akinsa Aliyu da Shahida ma kowannan su ya koma d'akinsa aka bar Mami da Nihal, Nihal ta rumgume Mami tana kuka tana son tayi magana amman ta kasa, haka dai suka zauna su kad'ai a falon kowannan su cike yake da tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyar.
