*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA⚜️🔱😭*
_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanarh M Sha'aban💓*_Labari mai tab'a zuciya🌹_
_Manzon Allah tsira da amincin Allah su k'ara tabbata a gareshi ya ce "Kyakkyawar magana sadaka ce" To dan haka idan ba za ka fad'i kyakkyawar magana a kan littafina ba dan Allah ki/ka dai na karantawa😌_
*Alk'alami yafi takobi⚔️*
Shafi na 25
"Ba na buk'atar jin komai daga bakinku nagode sosai, kun ji nasan irin zaman da zan yi da ku" Tana gama fad'ar haka ta juya zata fita Amatullahi ta rik'eta sosai tana cewa "Wallahi ba inda zaki je, nasan a kan bikin Aunty Murja da ba'a fad'a miki ba shiyasa kike fushi, to ki tsaya ki saurareni dan Allah Hafsa wallahi! wallahi!! wallahi!!! Kin ji na rantse miki ko, mu kan mu ba mu san da bikin ba, sai da muka zo gidan Hajiya Mama sannan" Fizge hannun Amatullahi tayi daga jikinta ranta a b'ace ta ce "daman baku yi niyyar na zo ba, tunda ranar ma a school babu yadda ban yi da ku ba, a kan ku shiga mota a kai ku gida ku ka k'i, kuma lokacin da ku ka hau adaidaita Yaya Safwan ya bi hanyar da ku ka bi, sai gani na yi kun bii hanyar gida anan na tabbatar kawai daman bakwa buk'atar cigaba da mu'amalarmu".
Khadijatullahi jikinta yayi sanyi dan kuwa ta san bata kyautawa k'awarta ta ba domin ita ce da laifi Amatullahi babu ruwanta nan, rik'e hannun Hafsan tayi lokacin da ta juya zata fita, ta juyo da niyyar fizgewa sai ta ga Khadijatullahi ce kuma tana tsoron karta fizge ta je ta fad'i tunda cikinta yanzu ya tsufa sosai ya kai wata takwas, "me zaki ce min ke kuma?" Hafsa ta fad'a cike da masifa, "ki yi hak'uri dan Allah wallahi ba wai da niyya mu ka yi miki haka ba, kuma Amatullahi kwata-kwata ba ta da laifi ni ce nake da laifin dan mana k'aunar abin da zai sake had'a ni da wani namijin na tsane su, ba na son ganinsu, amman bikin Aunty Murja wallahi kamar yadda besty ta ce ba mu san dashi ba mu ma sai da muka zo ake fad'a mana, kuma lokacin ya ri ga ya k'ure shiyasa ki yi hak'uri".
Hafsa tayi shuru tabbas ita ma ranar sai da ta raya wannan abin a zuciyarta cewa Khadijatullahi ba ta son ganin maza shiyasa ta k'i shiga motar "Shikenan ya huce" Hafsa ta fad'a tana murmushi, murmushin su ma suka yi gaba d'ayansu.
Aliyu ne ya shigo gidan idanuwansa a kan Khadijatullahi duk ya ji abin da suka fad'a zuciyarsa ta shiga bugawa magana Khadijatullahi ta girgiza shi ba ma shi kad'ai ba har da su Hajiya Mama domin kuwa sun san Jabir shi ne silar da yasa Khadijatullahi ta tsani maza, "Assalamu alaikum" Ya fad'a har lokacin idanuwansa na kan Khadijatullahi, amman ita tun da ya shigo ta kawar da kanta domin kuwa wata iriyar muguwar tsanar Aliyun take ji saboda tsananin kamannin Jabir da take gani a fuskar Aliyun ji take kamar Jabir d'in ne.
Suka amsa masa sallamar amman ban da Khadijatullahi d'akin Hajiya Maman ta shige tayi kwanciyarta, "ko me ya kawo shi nan, banza kawai" Tayi maganar zuciyarta kamar zata fashe saboda tsanar maza da tayi mata katutu a cikinta.
Hafsa da Amatullahi kuwa k'arasa suka yi suka zauna Hafsa ta gaisar da Hajiya Mama cike da girmamawa Aliyu ma ya gaishe da ita ya zauna kusa da ita suna yin hirarsu irinta jika da kaka, Hafsa kuwa hira suka shiga yi su da Shahida,Nihal da Amatullahi, zuciyar Amatullahi ta karkata a kan ta je ta ga wace wainar ake toyawa a gidansu domin kuwa ba ta k'aunar ace Lado da Inna Larai sun shirya, tashi tayi tana cewa "Sisters zan je na dawo yanzun nan","ina zaki je besty" Hafsa ta tambayeta.
"Ginin da na fara yi ne nake tsoron kada ya ruguje" Hafsa ta gane abin da Amatullahi take nufi dan haka ta fashe da dariya tana fad'i "gaskiya ne besty, gwanda ki je ki duba shi kar ya ruguje duk aikinki ya dawo baya" Khadijatullahi da take cikin d'aki tana jin su ita ma dariyar take yi sosai har suna iya jin dariyar Hafsa ta ce "Ahhh besty ke ma dole ki yi dariya, tana tsoron kar ya ruguje aikinta ya dawo ba, kin san fa besty akwai ta da iya tsara gini mai kyau","Ai kuwa dai kam" cewar Khadijatullahi.