*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😰💓💓💓💓💓💓*
_Daga alk'alamin✍🏾_
*'yar mutanan zazzagawa Nanah M Sha'aban**Wattpad@Naanarh2021*
_Labari mai tab'a zuciya_
Shafi na 5
"Aunty Murja gidansu Jabir naje domin kuwa in sheda musu da cikin da ke jikin Khadijatullahi ba zai yi ace ga mari ga kuma tsinka jaka ba, dole su d'auki dawainiyyar babyn har ta haihu, anan ta fad'a musu duk yadda suka yi daga farko har k'arshe", Aunty Murja tayi shuru kawai tana kallon Amatullahi har ta gama yi musu bayani, sannan ta nisa ta ce "A gaskiya ban san da wane irin baki zan gode miki ba, ke d'in ta daban ce, amman daga yanzu karki k'ara zuwa gidan saboda kin san halin Jabir tantirin d'an iska ne, dan Allah kinji k'anwata k'arki k'ara zuwa tunda dai kin riga kin je kin sheda musu hakan ma yayi".
"To Aunty Murja,ba zan sake zuwa gidan ba" tayi maganar cikin ladabi. kama hannun Khadijatullahi wacce hawaye sai ambaliya suke a fuskarta, ta shiga goge mata cikin muryar rarrashi ta fara magana "ki yi hak'uri kinji besty, bai kamata ki damu kan ki a kan wannan cikin ba, tunda dai ta hanyar aure kika same shi, nasan dai dole ki ji zafi da bak'in cikin samin cikin saboda irin abin da a kai miki A daren Aurenki". Da kallo kawai Khadijatullahi ta bi ta ba tare da ta ce mata komai ba, zamewa tayi ta kwanta a kan gadon ta rufe idonta zuciyarta na cigaba da k'una, Amatullahi ta kafeta da ido cike da tausayawa, har hawaye na kok'arin zubo mata, amman tayi saurin share hawayen dan kar Aunty Murja ta gani, jin Muryar Aunty Murja tayi tana cewa "Amatullahi ya kamata ki tafi gida tunda kin ga dare yayi k'arfe 9pm yanzu, in yaso gobe sai ki dawo" girgiza kai Amatullahi tayi tana cewa "A'a sam Aunty Murja ba zan iya tafiya gida ba, anan zan kwana dan Allah karki ce in tafi ko na tafi ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba", dafata Aunty Murja tayi cikin so da k'aunar yarinyar ta ce "Haba Amatullahi kina gani fa mun taho dake asibiti ba tare da kin je kin sanar a gida ba, kin ga bai kamata a ce kin kwana ba, kar hankalin iyayenki ya tashi basu san inda kike ba", "girgiza kai tayi a karo na biyu ta ce "waye zan damu idan bai ganni ba, Abbana ne kawai kuma baya gari yayi tafi ba yanzu zai dawo ba, kin san dai irin zaman da nake da step mother tunda Mamana ta mutu, ni yanzu ban da kowa daga Abbana sai kuma ku da nake ganinku tamkar 'yan uwana" ta k'arasa maganar cikin muryar kuka.
Babu yadda Aunty Murja ta iya dole ta kyale Amatullahi domin ta kwana a gurinsu, Amatullahi ta zame ta kwanta, kanta na kusa da k'afafuwan Khadijatullahi ita kuma Aunty Murja daman tana zaune a kan kujerar roba dan haka ta k'ara gyara zamanta domin ta ji dad'in baccin, har sukai bacci idan Khadijatullahi biyu domin kuwa ita ba bacci take ba kawai rufe idonta tayi, tashi tayi zaune tare da d'aga hannayenta biyu sama hawaye na zuba daga idanuwanta ta fara jerowa Jabir mugayen Addu'o'i "ya Allah kaga abin da azzalumin bawanka yayi min, ya Allah na rok'eka kayi min muguwar sakayya, ya Allah kasa Jabir yayi mutuwar wulak'anci, ya Allah ka tarwatsa masa duk wani farin cikinsa ka maye gurin binsa da bakin ciki, bakin cikin da zai dauwama a cikinsa har izuwa ranar tashin alk'ima, ya Allah na rok'eka kafin Jabir ya mutu ka d'ora masa cutar da kowa zai dinga gurinsa ya zama abin k'yamata ga jama'a" sai kuma ta fashe da kuka mara sauti tare k'ank'ame jikinta guri d'aya, ta d'auki kusan mintina goma tana kuka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.
*B'ANGAREN GIDANSU JABIR*
Kwance yayi a kan tafkeken gadonsa wanda mutane goma sha biyar ma zasu iya kwanciya ba tare da yayi musu kad'an ba, maganar da Amatullahi tayi masa ne ta tsaya masa take ta yawo a kunnansa "yarinyar da ka wulak'anka ka tozarta yanzu tana da ciki" bai san meyasa duk a maganganun da Amatullahi tayi masa ba wannan ta tsaye masa a rai, duk da cewa ba wai Khadijatullahi ce kawai ya tab'awa ciki ba, mata da yawa yayi musu ciki wad'anda ma bazai tab'a arga adadin su ba, amman wasu daga cikin matan su suke kawo kansu wasu kuma ta k'arfi yake yi musu, amman bai tab'a damuwa ba, amman gashi yau a kan cikin Khadijatullahi yayi matuk'ar damuwa har ya kasa yin bacci, wani dogon tsaki ya ja tare da cewa "koma dai menene bazan tab'a yarda cikina ne ba, domin ni bazan had'a zuri'a da 'yar gidan matsiyata ba" a haka dai ya rufe idanuwansa yana cigaba da saka abubuwa da yawa a ransa har bacci b'arawo yayi awan gaba dashi.
*Wanene Jabir?*
Jabir babban d'a ne ga Alhaji Mansur jikamshi wanda ya kasance shine minister mai fetur na k'asa nigeria, mahaifiyarsa hajiya Asiya 'yar wani malami ce wanda ya kasance yana koyar da almajirai karatu sun had'u ne ta sanadiyar mahaifinnata Malam kalla domin Alhaji Mansur idan ya samu lokaci yana shigowa unguwar tasu ya yiwa Malam kalla alheri da kuma almajiran da yake koyarwa, ranar nan yazo gurin Malam kalla sai ga Asiya ta fito daga cikin gidan sanye take da d'an k'aramin mayafi tsugunna har k'asa ta gaishesa cikin fara'a da sakin fuska ya amsa mata sannan ta fita zuwa aike da mahaifiyar ta tayi mata, haka ya tashi ya tafi gida tun daga ranar ya nemi nutsuwarsa ya rasa domin kuwa ya kamu da tsananin son Asiya da ya ga yana neman cutuwa dai haka ya shirya ya nufi unguwarsu Asiya domin ya sami babanta Malam kalla ya sheda masa abin da yake faruwa ya ji ko anyi mata miji.
Yana isa kofar gidan Malam Kalla ya fito daga cikin motar kamar yadda ya saba yaje har cikin rumfar da Malam Kalla yake koyar da Almajirai karatu ya zauna bayan sun gaisa ne.
Alhaji Mansur ya fara magana da cewa "daman Malam na ga 'yar wajen ka ce nace to bari in zo naji ko anyi mata miji ne, dan ni har ga Allah ina sonta da Aure ne a yanzu idan har ba'ayi mata miji ba ma zuwa nan da wata biyu ma nake son ayi biki" Alhaji Mansur yayi maganar cike da girmamawa, wani irin farin ciki ne ya kama Malam Kalla tabbas yayi matuk'ar farin cikin jin wannan furucin daga gurin Alhaji Mansur d'in domin kuwa Alhaji mansur mutum ne da kowane uba zai so ace 'yarsa ta aure sa" dan haka Malam Kalla ya fara magana cikin tsananin farin ciki "Alhamdulillahi Allah na gode maka a gaskiya Alhaji ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba domjn kuwa nasan kai d'in mutum ne na gari amman ban san wa ka gani ka ke so daga cikin yaran nawa ba?".
Cikin jin dad'in yabon da Malam Kalla yayi masa ya ce "Wacce ta fito ranar da muke zaune ta gaisar da ni ta fita da mayafi", "Ohhhh Asiya kenan" Malam Kalla ya fad'a domin kuwa yasan kaf cikin 'ya'yansa ita kad'ai ce take saka mayafi sauran duka hijabi suke sakawa.
"Eh ita nake nufi" Alhaji Mansur ya ce cikin Murmushin jin dad'i, Malam Kalla ya ce "A gaskiya Asiya ba'ayi mata miji ba, amman dai ban sani ba ko ita akwai wanda take so, ina son ka bani lokaci zuwa gobe domin in zauna da ita duk yadsa mukai da ita zaka ji insha Allahu". "To Malam insha Allahu goben zan dawo kamar dai-dai wannan lokacin", "To Allah ya kaimu" Malam Kalla ya fad'a da murmushi a kan fuskarsa, Alhaji Mansur bayan sun d'an yi hira sannan ya tashi ya ajiyewa Malam Kalla band'ir d'in kud'i ya rabawa almajirai kud'i sukai masa godiya ya tafi zuwa gidansa*Anan zan tsaya sai ku dakace ni anjima insha Allahu indai naga comments mai yawa zaku ji ni d'auke da sabon posting yawan comments yawan typing*
*Please🙏🏽*
*Share*
*Comments*
*Vote*_Daga alk'alamin 'yar mutanan zazzagawa_