EPISODE 22

203 12 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😰💔*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

_Labari mai tab'a zuciya❣️_

*Alk'alami yafi takobi🚴🏽‍♀️*

*Shafi na 22*

"Amincin Allah ya k'ara tabbata a gareki ma'abociyar nutsuwa da hankali kyakkyawar Matata wacce nake saka ran a cikin wannan satin zan fara tunanin samun 'ya'yana daga gareki".

Murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da Kai, Amman kalmar da ta tsaya mata ita ce da Alhaji Mansur d'in ya ce a cikin wannan satin zai fara saka ran samun 'ya'ya, to shine ta rasa gane meyake nufi.

'yar k'aramar kujerar k'arfe ya d'auko ya ajiye kusa da ita ya zauna, da sauri ta kallesa domin kuwa gurin da rana sosai "ka tashi daga nan akwai rana sosai, karka sami matsala","A'a na k'i" ya fad'a yana mak'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro, abin ya ba wa Aunty Murja dariya sosai, tsayawa yayi Yana kallonta tare da cewa "Murjanatu dariyarki tana saka ni nishad'i fi ye da yadda bakya tunani".

Kallonsa ta yi sosai ta ce "Kai ne ai ka ke ba ni dariyar, nagode sosai Kuma......" Sai kuma tayi shuru tare da yin wasa da zoben hannunta, Alhaji Mansur ya k'ura Mata ido tare da cewa "Kuma me?","Bakomai"ta bashi amsa har lokacin tana wasa da zoben hannunta, "ba za ki fad'a min ba ko?", Kai ta girgiza Masa alamar "A'a".

Mik'ewa yayi fuskarsa ta chanza zuwa yanayin fushi ya nufi hanyar waje, da sauri Aunty Murja ta bi bayansa a gabansa ta tsaya tana cewa "Dan Allah ka yi hak'uri","to fad'a min kuma me?" Aunty Murja ta ce "Daman godiya kawai zan maka" ta fad'a dan ba za ta iya fad'a masa abin da ke ranta ba, tana jin tsananin kunyarsa.

"Shikenan nagode miki sosai, kuma nasan matsayina a gurinki tunda kin k'i fad'a min kin nuna min ban kai matsayin da zan san abin da ke ranki ba" Yana gama fad'ar haka ya huce ya fita motarsa ya shiga ya ja ya bar unguwar, Aunty Murja tsugunnawa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka gaba d'aya haushin kanta take jii a kan meyasa ba ta fad'a masa ba, har ta bari yayi fushi da ita.

Hajiya Mama kuwa duk abin da suka yi tana jin su, domin kuwa tana cikin toilet ne ta shiga kama ruwa kuma tsakanin toilet d'in da inda suke babu nisa, murmushi tayi sannan ta koma d'aki ba tare da ta bari Aunty Murjan ta ganta ba, a zuciyarta tana cewa "sai yanzu Mansur zaka san zakai aure".

Ita kuwa Aunty Murja haka ta gama shan kukanta sannan ta tashi ta k'arasa wanke-wanken ta kifesu a kwanbo sannan ta shiga d'akin Hajiya Mama ta yi Mata sallama ta fito ta nufi gida zuciyarta a cunkushe.

              *POLY🚴🏽‍♀️🏦*

Zaune suke su uku kamar kullum komai nasu iri d'aya abin gwanin ban sha'awa, Hafsa tana ba su labarin yadda suka yi da Yaya Safwan, Amatullahi tayi murmushi tare da cewa "Ahhh Lallai lovers ina ta ya ki murna k'awata, ki ce  mun kusan shan biki" murmushi Hafsa tayi tare da cewa "insha Allahu" Khadijatullah ta ce "Nima ina ta ya ki murna k'awar arzik'i","Nagode muku sosai k'awayen arzik'i" Hafsa ta fad'a tana murmushin jin dad'i haka dai sukai ta hirarsu abin burgewa gaba d'aya makarantar suna burgesu dan wasu ma sunyi tunanin 'yan uku ne, babu wanda yayi tunanin ya iyayensu d'aya ba, sai da aka koma aji sannan suka tashi domin komawa ajinsu.

Wajen k'arfe 6:00pm dai-dai aka tashi suka fito Yaya Safwan Hafsa ta hango ta saki wani irin murmushi sannan ta ce "yau fa, Yayana ne ya zo d'aukarmu" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "gaskiya Yaya Safwan yana ji da Amaryarsa sosai" dariya Hafsa tayi sosai tare da cewa "ai dole ya ji da Amrish d'insa, ku taho mu tafi" Khadijatullahi ta ce "A'a zamu hau adaidaita Aunty Murja ta aikemu" babu yadda Hafsa ba tayi ba a kan su taho in ya so sai su biya wajen da Aunty Murja ta aikensu daga nan su kai su gida, amman Khadijatullahi ta kafe a kan Aunty Murja ta aikesu kuma gurin da nisa, haka Hafsa ta hak'ura ta tafi zuciyarta babu dad'i.

Amatullahi kuwa mamaki ne ya isheta ita dai ta san babu inda Aunty Murja ta aikesu, amman kuma Khadijatullahi ta ce ta aikesu, haka dai suka fita suka nemi adaidaita suka shiga, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi sosai sannan ta ce "ina Aunty Murja ta aikemu?" Khadijatullahi ta kalleta tare da cewa "ba ko ina" Amatullahi ta ce "to meyasa ki ka cewa Hafsa Aunty Murja ta aikemu","Saboda ba na son ko gaisuwa ta k'ara had'a ni da wani namijin, na tsani maza wallahi ji nake kamar na kashesu" shuru Amatullahi tayi daman ta san za'a rina, shi kuwa mai adaidaita tsoro ya kamashi "to anya wannan yarinyar lafiyarta k'alau kuwa" ya fad'a a zuciyarsa haka dai yayi ta mamaki har ya kai su kofar gida suka sauka Khadijatullahi tayi gaba Amatullahi ta tsaya domin biyansa kud'insa.

Haka ta bi bayan Khadijatullahi suka shiga gidan da sallama Aunty Murja suka tarar kallo d'aya zakai mata kasan tana cikin damuwa zama suka yi kusa da ita suna tambayarta "me yake damunta" ta ce "bakomai" wannan karan basu takura mata ba domin kuwa kowannan su zuciyarsa cike take da damuwa.

*'BANGAREN NIHAL😹🚴🏽‍♀️*

Hajiya Asiya haka ta tattara Nihal ta nufi gida da itaba tare da Salis ya sani ba, Nihal ba ta san k'udurin Mamin ba dan duk a tunaninta sun fad'awa Salis d'in zata yi jinya a gida ne idan ta warke sai ta koma, dan da Alhaji Mansur ya dawo ya ga Nihal d'in yake tambayar meya sameta, Hajiya Asiya ta bashi labarin k'arya da gaskiya ta fad'a masa, da ya tambaya an fad'awa Salis d'in za'a taho da ita gida, Mami ta ce Eh an fad'a masa, Alhaji Mansur bai zurfafa bincike ba, domin duk ya d'auka da sanin Salis d'in.

Kwanan Nihal biyar a gidansu sai ga Salis ya zo gidan domin jin shuru Nihal ba ta dawo ba, Nihal ta fito raka wasu k'awayenta ta hango Salis d'in da sauri ta k'arasa gurin da yake tana murmushi, shi kuma ya had'e fuska, Mamaki ta shiga yi "Yaya Salis me ya faru?" Harararta yayi sannan ya ce "ban sani ba, tunda ke kwata-kwata bakya tausayina","Ayya sorry Yayana, tuba nake ba zan sake ba" Salis ya ce "babu abin da zaki ce min tunda baki fad'a min zaki dawo gida ba, kuma gashi kwananki uku" ido Nihal ta zaro tare da cewa "wai daman Mami ba ta fad'a maka ba ta ce mana ta fad'a maka zan dawo gida har sai nayi wata d'aya zan koma" Mamaki ya kama Salis ya ce "ni d'in ne na fad'i haka, to wallahi Mami ba ta kirani ba" Shuru Nihal tayi na wani lokaci sannan ta ce "kayi hak'uri Yaya wallahi......" Dakatar da ita yayi yana murmishi "haba Sweetheart bakomai wallahi, yanzu ki je ki shirya ki zo mu tafi gida" ta ce "to shikenan" ta juya ta nufi gidan, d'akinta ta nufa ta hijabinta ta d'auka sannan ta fito kallonta suke cike da mamaki Shahida ta ce "Otherhalf ina zaki je?","Yaya Salis ne yake jirana zamu tafi" Mami ta mik'e cikin fushi tare da cewa "babu inda zaki je, kin dawo kenan" Abba ya kalleta cike da mamaki sannan ya ce "ba Salis d'in ya ce sai nan da wata d'aya ba fasawa yayi ne" Nihal ta ce "Abba Yaya Salis bashi da masaniya a kan wannan zance Mami ce ta fad'a yanzu yake fad'a min, wai na taho gida ba'a fad'a masa ba" Abba ya ce "daman baki fad'a masa ba Nihal" Nihal ta ce "Abba ba laifina ba ne Mami ce ta ce min ta fad'a masa kuma ta kwacen waya ni nayi tunanin d gaske take yi, ashe sharri tayi masa" Wani irin wawan mari Mami ta d'auke ta dashi tana cewa "Wani k'aton banza zaki fifita a kai na to wallahi ba zaki koma ba, shegiya wacce ba ta san ciwon kanta ba" Abba kuwa cikim fushi ya tashi ya nufi inda Mamin take ya zabga mata mari yana cewa "to sai mu gani, tunda ke baki da hankali, ke Nihal wuce ki bi mijinki ku tafi gida" Nihal ta ce "to Abba" ta fita da sauri tana kuka tana zuwa gurin Salis yake tambayarta "menene take kuka?" ta fad'a masa komai da komai nan ya shiga rarrashinta sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya koma mazaunin driver ya ja mota suka bar gidan.

*BAYAN KWANA BIYU*

A yau ne aka d'aura auren Alhaji Mansur da Aunty Murja wanda aka biya sadaki naira dubu dari biyar kwata-kwata Aunty Murja ba ta da masaniya a kan auren ta zo gidan Hajiya Mama tana yi aiki ta gama wanke-wankr ta fara shara har ta kusan gama sharar sai ga Alhaji Mansur ya shigo gidan, da sauri Aunty Murja ta d'ago saboda jin kamshin turararsa wata iriyar nannanyan ajiuar zuciya ta sauke wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta rabon da ta ganshi tayi kusan kwana biyar amman ji take kamar tayi shekara biyar ba ta ganshi ba a fili ta ce..................🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️🚴🏽‍♀️😹

Anan zan tsaya yau banda chaji😰

*Please👏🏽👏🏽*

*Share👏🏽👏🏽⚜️*
*Comments🔱*

*'yar mutanan zazzau ce🔱⚜️❤️🚴🏽‍♀️*

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now