EPISODE 20

272 11 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭😭💔🔱⚜️*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

~*Alk'alami yafi takobi*~

Shafi na 20

Alhaji Mansur yana isa gidan Hajiya Mama yayi parking d'in motarsa ya shiga gidan bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" babu kowa a tsakar gidan dan haka ya nufi d'akin Hajiya Mama ya shiga d'akin da sallama Aunty Murja ya gani zaune tana karatun wani littafi mai suna *Magajin masarauta* wanda *Murjanatu bintu Al'amin ce ta rubutashi* da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da ita zuciyar Alhaji Mansur ta shiga bugawa da k'arfi gaba d'aya ya shagala da kallo Aunty Murja ita kuma ganin irin kallon da yake mata duk gaba d'aya ta rikice ta kasa amsa sallamar da yayi sunkuyar da kanta k'asa tayi tana wasa da littafin da yake hannunta, Hajiya Mama ce ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya tana kallon irin yadda d'an nata yake kallon Aunty Murja yana murmushi ko kifta idanuwansa ba ya yi, wani irin murmushin su na manya tayi tare da godewa Allah daman tana son ace d'an nata ya ga Aunty Murja ya ce yana sonta, kuma daman tana son ta yi masa magana a kan ya aureta, domin kuwa ta san zai more da mata kuma 'ya'yansa zasu taso cikin tarbiyya.

Gyaran murya tayi Alhaji Mansur ya d'ago yana sosa kai tare da cewa "Hajiya ashe daman kina nan nayi tunanin ai bakya nan" harara ta watsa masa tare da cewa "To yau kuma da sabon salon da ka zo kenan, ka tab'a ganin ka zo gidan nan ba ka same ni ba" murmushi yayi tare da neman guri ya zauna yana cewa "A'a Hajiya ai nayi tunanin ko suna ki ka je", "A'a dambe na je ba suna ba" wannan maganar da Hajiya Mama ta yi ba k'aramar ba wa Aunty Murja dariya ta yi ba har ta kasa b'oye dariyar sai da ta yi ta a fili, Alhaji Mansur ya kalli yadda Aunty Murjan take dariya, ya k'ara jin ta shiga ransa domin ita kanta dariyar ta ta abin tsayawa a kalla ce "Murjanatu kema maganar Hajiya ta baki dariya kenan" ya fad'a yana kallonta, Aunty Murja ta yi mamaki domin jin Alhaji Mansur ya fad'i sunanta "to a ina yasan sunana?" ta fad'a a zuciyarta.

Alhaji Mansur ranar da ya fara ganin Aunty Murja, ya ji Hajiya Mama ta kira ta da Murjanatu shikenan shima ya rik'e sunan, Kallonsa Aunty Murja ta yi sannan ta ce "Eh".

Hajiya Mama ta samu guri ta zauna tana cewa "to ai sai kuyi ta dariyar, idan kun zare na kai ku dawanau" dariya Alhaji Mansur ya yi sannan ya ce "To mun dena Hajiya. yau fa zuwan nawa na musamman ne, na zo neman wani abu mai muhimmanci ne ban sani ba ko zan dace na same shi ya zama mallakina".

Hajiya Mama duk da cewa ta san inda zancen sa ya dosa, amman sai ta nuna masa ba ta gane ma yake nufi ba ta ce "Wane irin abu ne wannan mai muhimmanci?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli gurin da Aunty Murja take zaune suka had'a ido a karo na biyu, gabanta ne ta ji ya fad'i gaba d'aya ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tashi ta yi sannan ta ce "Hajiya bari inje tsakar gida na k'arasa tankad'en na san yanzu ruwan ya tafasa" Hajiya ta ce "to shikenan" fita tayi da sauri ta zauna a tsakar gidan tana tankad'en, Alhaji Mansur kuwa Aunty Murja tana fita ya juyo yana kallon Hajiya Mama yana cewa "Hajiya Mama kin san dai irin zaman da nake da Asiya, gaba d'aya ta lalata min tarbiyyar yara Shahida da Aliyu ne kad'ai suka fita zakka, kuma uwa uba Asiya sam bata k'aunar 'yan uwana,Hajiya Mama ina buk'atar na k'ara aure tunda dai ina da halin da zan iya rik'e mace sama da d'aya, kuma ina son na auri Murjanatu idan ba'ayi mata miji ba domin na yaba da halayenta"

Murmushi Hajiya Mama ta yi sannan ta ce "Alhamdulillahi daman ina da burin na ga ance yau kai ne zaka auri Murjanatu domin yarinyar tana da hankali sosai, kuma gaskiya ba na tunanin anyi mata miji saboda a yadda ta ba ni labari iyayensu sun mutu kuma ita kad'ai ce take kula da 'yan uwanta ita suke kallo a matsayin uwa kuma yayarsu" Alhaji Mansur ya ji matuk'ar dad'i ya ce "to yanzu Hajiya ya ya za'ai ina son nan da sati uku masu zuwa a d'aura auren saboda ba na son a ja wani dogon lokaci" Hajiya Mama ta ce "to ai sai ka bari muji ta bakinta ko?" Alhaji Mansur ya ce "Hakane kam Hajiya Mama" Hajiya Mama ta kira sunan Aunty Murja, ta amsa tare da ajiye tankad'en ta shigo d'akin har lokacin zuciyarta bata dena bugawa ba, zama ta yi a kujerar da ta tashi tare da sunkuyar da kanta tana cewa "Gani Hajiya" Hajiya Mama ta ce "Mansur ne ya zo min da wata magana wacce ta saka ni cikin tsananin farin ciki, da ina da dama da tun kafin ya rufe bakinsa zan basa abin da ya ke buk'ata amman ban da wannan damar shiyasa na ce bari in kirawo ki domin muji ta bakinki, Mansur yana so ya aureki kuma baya so a ja lokaci mai tsayi" Aunty Murja ta d'ago da sauri suka had'a ido da Alhaji Mansur wata iriyar kunya duk ta lillib'eta ta saka kanta a kan cinyarta tare da jan hijabinta ya rufe mata fuska, Hajiya da Alhaji Mansur murmushi kawai suka yi, Hajiya ta mik'e ta shiga bedroom domin ta basu guri su yi magana.

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now