*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭😭❤️*
_Daga Alk'alamin✍🏾_
~*Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*~_Labari mai tab'a zuciya❣️_
*Wannan shafin na ku ne, ma'abota karatun littattafai na,ina matuk'ar farin cikin yadda kuke jin dad'in littafin nan daren aurena na gode muku sosai🙏🏽*
*Gaisuwa ta musamman ga Ummu juwairyya (Jabir😂) Maman Afra (Nihal😂) Jamila Aliyu (Amatullahi😂) sai kuma continue discussion😉*
Shafi na 10
Da gudu Lado ya fita daga d'akin Amatullahi yana zabga ihu kamar zai zauce, Amatullahi wacce take tsaye a kan gadonta ta shek'e da wata irinyar dariya tare da cewa "An gaya maka ni d'in ta wasa ce, da ka tsaya hannunnaka zan cire gaba d'aya d'an iskan banza". A tsakar gida Lado ya tarar da Inna larai tana jiran fitowarsa zuciyarta cike da farin cikin d'annata zai d'aukar mata fansa, jin ihun Lado da tayi ne yasa hankalinta ya tashi gashi kuma tana tsoron shiga d'akin Amatullahi saboda tana tsoron abin da zai biyo baya gashi daman bata gama jinyar fuskarta ba, da gudu Lado ya k'araso gabanta har yana ban gaje ta yana fad'ar "inna 'yar ta'adda ce Amatullahi 'yar daba ce" ya fad'a a rud'e hannunsa yana fitar da jini kamar da bakin k'warya, Inna a gigice ta ce "me tayi maka Lado?" Lado ya ce "Inna ta sare ni a hannuna, kalli ki gani" da kyar Inna ta iya bud'e idonta domin tun ranar da Amatullahi ta dannata a cikin kaskon mai ta dena gani sosai, kuka Inna larai ta saka tana magana cikin sarkewar murya "gaskiya yarinyar nan ta cika tantiriya,bari ubanta yazo wallahi bazan iya zama da ita ba, ko ni ko ita wallahi" ta k'arasa maganar tare da shigewa d'akinta tana kuka shi kuma Lado ya fita zuwa *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* domin a duba shi.
*Wace ce Amatullahi?*
Mahaifin Amatullahi Malam Shu'aibu d'an asalin garin kano ne yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado mahaifiyar Amatullahi Asma'u 'yar abokin Malam Shu'aibu ce wanda shima ya kasance yana da rufin asirinsa, Malam Shu'aibu ya dad'e yana tsananin son Asma'u amman ya kasa fad'awa mahaifinta Malam Abbakar saboda a ganinsa kar ayi mata dole dan ya san indai ya fad'awa Malam Abbakar to zai amince ne kuma shi sam baya son ya auri Asma'u ba'a son ranta ba, haka dai ya cigaba da dakon soyayyar Asma'u a cikin zuciyarsa, ranar da bazai tab'a mantawa da ita ba domin a ranar ne burinsa ya cika na auran Asma'u, Malam Abbakar ne ya aiko har gida a kan yana nemansa a gidansa, cike da tashin hankali Malam Shu'aibu ya nufi gidan aminin nasa saboda shi a tunaninsa kodai wani abun ne ya faru a gidan, yana zuwa aka yi masa iso har cikin falon gidan da sallama ya k'arasa ya shiga falon, lokaci d'aya kuma ya shiga cikin matsanancin mamaki ganin gaba d'aya 'yan gidan a falon gidan ga kuma Malam liman da kuma mai unguwa Malam Tanko, bayan sun gaisa ne Malam Shu'aibu ya zauna a kan kujera, Malam Abbakar bayan yayi sallama tare da yin wasu addu'o'i sannan ya fara koro bayanin abin da yasa ya tara su gaba d'ayansu, "Malam liman da ranka ya dad'e mai unguwa abin da yasa na tara ku anan dan ku zame mana shaida nii Abubakar na bawa Abokina kuma aminina Malam Shu'aibu auren Asma'u, kuma ina so a yanzu ba sai anjima ba a d'aura musu aure, kuma nayi wannan shawarar ne tare da amincewar Asma'u ba wai dole nayi mata ba" wani irin farin ciki ne ya lullub'e Malam Shu'aibu ya dinga tunanin wai mafarki yake yi ne ko kuwa da idonsa biyu ashe akwai ranar da burina zai cika na auren muradina Asma'ul Husna, yana cikin tunanin ne ya ji muryar Malam liman yana yi masa Allah ya sanya alkhairi daga nan suka tashi shi da mai unguwa suka fita nan, Malam Abbakar ya tashi daga gurin da yake da dawo kusa da aminin nasa "Ina yi muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya ya ba ku zuri'a d'ayyiba, na san zaki yi mamakin abin da yasa na had'a auranka da Asma'u nayi hakane ba dan komai ba saboda bana son irin yadda kake zaune babu wacce zata dinga kula da kai, ina yi muku fatan Alkhairi zata iya d'aukar matarka ka tafi da ita domin ta ri ga da ta shirya", kallonsa Malam Shu'aibu yake cike da tsantsar son Malam Abbakar ya ce "ban san ma da wasu irin kalmomi zan yi amfani dasu ba wajen gode maka nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi". Haka suka d'an tab'a hira Malam Shu'aibu ya tashi da niyyar tafi gida Malam Abbakar ya cewa Asma'u da ta tashi ta bishi, haka ta tashi tana kukan rabu da 'yan uwanta ta bi mijinta Malam Shu'aibu mahaifiyarta tana biye da ita da k'aton akwatin kayanta Allah sarki, motar Malam Abbakar suka shiga aka saka akwatin a boot driver ya ja su zuwa gidansu Malam Shu'aibu, suna zuwa driver ya shigar musu da akwatin sannan sukai sallama suka shiga gidan tare Asma'u ta rufe fuskarta da mayafi, suna shiga Inna Labara mahaifiyar Malam Shu'aibu ta tare su fuskarta d'auke da mamaki "Shu'aibu kai da wace?" cike da jin kunya ya ce "Inna Asma'u ce 'yar gidan Abbakar, nan Inna ta shiga fara'a ta ja Asma'u suka je suka zauna a kan taburma, shima ya d'auko taburma ya ajiye a kusa dasu Malam Shu'aibu ya fad'awa Inna duk abin da ya faru, wata iriyar gud'a inna tayi sannan ta shiga sakawa Malam Abbakar Albarka tashi tayi ta gyara musu wani d'an k'aramin ta d'auki akwatin Asma'u ta kai d'akin, abinci ta zubowa Asma'u ta ci sosai, tun daga ranar Malam Shu'aibu ya cigaba da nunawa Asma'u soyayya da tsantsar k'auna har Allah ya bata ciki wanda ba'a gane shi ba har sai da cikin ya kai wata hud'u murna gurin Malam Shu'aibu ba'a magana, haka ya cigaba da bata kyakkyawan kulawa ta musamman har Allah ya sauketa lafiya ta haifi 'yarta mace a gida a wata ranar litinin, ranar suna aka sakawa yarinya suna Amatullahi haka gidan ya cika damk'am da 'yan uwa da abokan arzik'i sai wajen k'arfe 10:00pm na dare sannan aka watse aka bar Asma'u daga ita sai Inna da yarinyarta Amatullahi, Amatullahi ta taso cikin gata saboda Malam Shu'aibu ya d'auki son duniya ya dorawa Amatullahi hatta yaye shi ya yayeta duk inda zai je da ita yake zuwa, Asma'u kuma bata k'ara samun ciki ba har sai da Amatullahi ta kai shekara 14 a duniya wannan cikin yazo mata da laulayi har yayi sanadiyar mutuwarta Allah sarki Malam Shu'aibu yayi kukan rashin matarsa mai ladabi da sanin ya kamata bashi kad'ai ba har Inna ma tayi kukan rashin Asma'u Malam Abbakar ne ya shiga rarrashin Malam Shu'aibu tare da yi masa nasiha mai ratsa zuciya, a ranar da Asma'u ta cika shekara d'aya da rasuwa, Inna Laraba Mahaifiyar Malam Shu'aibu ta koma ga Allah, tashin hankali ya k'ara aurar Malam Shu'aibu daman gashi bai gama fita daga cikin damuwar rashin matarsa ba, ya rasa abin da yake yi masa dad'i haka ya cigaba da rayuwa daga shi sai Amatullahi a gidan duk inda zashi tana nanik'e dashi, ranar da Inna tayi arba'in Malam Abbakar yazo masa da maganar auren wata bazawara 'yar abokinsa Larai, Malam Shu'aibu ya amince saboda daman yana buk'atar wacce zata dinga kular masa da Amatullahi, haka Malam Abbakar ya shige gaba aka d'aura auren Malam Shu'aibu da Larai, ya gyara gidan da suke zaune aka k'ara d'akuna, ka kawo Amarya Larai d'akinta tare da yaronta Lado, tun da Larai ta ga irin son da Malam Shu'aibu yake yiwa Amatullahi ta d'auki tsanar duniya ita da d'anta suka dorawa Amatullahi suka fara takura mata amman sai suka ga abin yafi k'arfin su saboda Amatullahi ba k'aramar 'yar bala'i ba ce dan komai sukai mata sai ta rama bata tab'a barinsu, Allah ya had'a Amatullahi da wata 'yar layin su Khadijatullahi suka kulla aminci kullum Amatullahi tana gidansu Khadijatullahi idan Khadijatullahi ta ga lokacin zuwa Amatullahi yayi bata zo ba haka zata d'auki hijabi taje gidan ta ga lafiya haka suka cigaba da rayuwa cikin so da k'aunar junansu, Inna Larai kuwa bakin ciki kamar zata yi hauka ganin tayi shekara biyar a gidan Malam Shu'aibu amman ko b'ari bata tab'a yi ba kuma tana tsananin jin bakin cikin irin yadda Malam Shu'aibu yake nuna damuwarsa a kan 'yar tasa kuma kullum cikin yi mata siyayyar tsire yake mata, shiyasa kullum ita ma take k'ara jin tsanar Amatullahi da kuma bakin cikin rashin samun cikin da bata yi ba.
*Wannan shine takaitatcen tarihin Amatullahi, yanzu zan dora labarinmu*
Yau ya kama su Amatullahi zasu fara zuwa makaranta, Amatullahi ta tattaro kayan da zata saka tazo gidan su Khadijatullahi domin ta shirya a gidan, kayan iri d'aya suka saka komai nasu iri d'aya sun yi kyau sosai, haka suka fita daga gidan zuciyoyinsu cike da farin ciki, Khadijatullahi ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki sosai mara misaltuwa, haka suka yiwa Aunty Murja sallama tayi musu addu'o'i ta samun nasara, suka kama hanyarsu ta zuwa poly, 'bangare d'aya suka cike gaba d'ayansu wato law, suna isa cikin makarantar suka tarar ana shirin shiga lecture bayan sun tambayi ina ne ajinsu aka nuna musu suka nufi ajin cikin farin ciki da annashuwa, suka shiga ajin bakinsu d'auke da sallama wasu daga cikin 'yan ajin suka amsa musu, suka nemi guri a gaba suka zauna suna yin hirarsu har Malami ya shigo kowa yayi shuru aka shiga lecture.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*
*Anan zan tsaya sai ku dakace ni a gobe in Allah ya yarda yawan comments yawan typing*
*Godiya mara adadi gareku fans d'in daren aurena Allah ya biyaku da gidan Aljanna🙏🏽❣️*
*Please🙏🏽*
*Share*
*Comments**'Yar mutanan zazzau ce❣️💃🏼✍🏾*