EPISODE 14

275 12 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭🔱⚜️❤️🌸*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
~*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*~

_Labari mai tab'a zuciya❣️_

*Queen Nasmarh my fata-fata🔱⚜️ina godiya da irin yadda kike nuna min kulawa nagode sosai wallahi i love you😂❤️⚜️🔱🌸*

*Mommyna Hajara b sarki da kuma Abbakar Abbana nagode muku sosai wallahi da kulawa🌸❣️*

Shafi na 14

                                 *Washe gari🌸⚜️*

Inna Larai ce zaune ita da Lado sun gama had'awa Amatullahi mak'irci gurin mahaifinta Malam Shu'aibu a kan cewa tana fita yawo kuma idan ta tafi makaranta ba ta dawowa sai chan dare wajen k'arfe goma za'a zo ayi parking d'in mota a sauketa a kofar gida, hankalin Malam Shu'aibu ya tashi dan haka ya buga sammako da dawo gidansa, ko da ya dawo ya tambaya ina Amatullahi suka ce tana cikin d'akinta, ya nufi d'akin yana kwad'a mata kira da sauri ta fito cikin wata doguwar rigar abaya plum colour ta yafa mayafin abayar rik'e da jakarta ta zuwa makaranta tayi kyau sosai sai kamshi take yi murmushi tayi ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Abbanta, abin da ya bawa su Innah Larai mamaki sai suka ga Malam Shu'aibu yayi murmushi ya amsa gaisuwar da tayi yayi mata umarni da ta tashi tsaye ta mik'e, anan ya shiga tambayarta "Mamana meyasa idan kin je makaranta bakya dawowa da wuri sai goma na dare kuma ajiye ki ake yi a mota, kuma kika watsa Larai mai a fuska ita da Lado" cikin mamaki ta ce "Abbana ni kuma wallahi Abba kullum da wuri nake dawowa kuma ni da Khadijatullahi muke dawowa a adaidaita, kasan dai ba na kula kowane saurayi kai ma shaidata ne bare har in shiga motarsa wallahi zan iya dafa al'kur'ani ban tab'a shiga motar kowa ba kuma ban tab'a kai wa goma na dare a waje ba kuma Innah Larai da Lado sune suka ja duk abin da nayi musu anan ta fad'a masa duk abin da ya faru" ta k'arasa maganar tana kuka,  anan Malam Shu'aibu ya shiga rarrashin 'yar tasa har tayi shuru ya kama hannunta suka yi hanyar waje, Amatullahi idanuwanta a kan su Inna Larai da fuskokinsu suka chanza saboda basu yi nasarar had'a uba da 'yar ba tasan tabbas sune suka had'a mata mak'ircin nan kuma wallahi ba za ta kyalesu ba sai ta rama (ni kuwa 'yar mutanan zazzau na ce su inna larai an taro match🤣) haka suka fita daga gidan mahaifinta na rik'e da hannunta a kofar gida suka tsaya mahaifina ta ya kalleta cike da so da k'auna "Mamana kiyi hak'uri nasan kina hak'uri zama dasu Larai daman nasan ni ba halinki ba ne, amman nasan yadda zan shawo kan abin" hannu ya zura a aljihu ta d'auko 2k (dubu biyu) ya mik'a mata sannan ya cigaba da magana "gashi nan kiyi amfani dashi dan ba lallai ki dawo ki same ni ba, zan koma chan companyn namu yanzu ma jirana ake yi" Amatullahi ta karb'a tare da yi masa godiya, ta nufi gidansu Khadijatullahi zuciyarta fal farin ciki domin kuwa taji dad'i da Abbana ta ya ce zai koma wannan zai bata damar had'a musu nata mak'irci amman kuma ita ba k'arya zata musu ba, a kan abin da suke aikatawa a gidan zata yi musu basu san dawa suke zancen ba ne, da wannan tunanin ta k'arasa gidansu Khadijatullahi ta tarar ita ma har ta gama shiryawa doguwar rigar abayar tasa komai iri d'aya haka suka yi wa Aunty Murja sallama suka nufi hanyar fita daga gidan.

Suna fitowa suka yi sa'a ga wani mai adaidaita zai fita daga layin suka tsayar dashi suka shiga Amatullahi ta ce "Baba poly zaka kai mu ta gadon k'aya" kasancewar mai adaidaitar tsoho ne, shiyasa ta ce masa Baba, ya amsa mata da "to" suna isa Khadijatullahi ta bud'e jakarta ta d'auko naira d'ari biyar wacce ita kenan da ita zata mik'awa mai adaidatan Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "to Hajiyata ai sai ki bari in biya ko?" ta fad'a tana mik'awa mai adaidatan naira d'ari biyar tunda daman a haka ake kawo su makarantar, suka shiga makarantar suna zuwa suka tarar da Hafsa har tazo abin da ya basu mamaki shine abayar da Hafsa ta saka komai iri d'aya da tasu babu abin da ya bambanta k'arasawa gurinta suka yi Amatullahi ta ce "Besty Hafseyy yau fa kinsa mun shiga mamaki sosai" murmushi tayi ta ce "Saboda kayan da nasa irin naku ko?" Khadijatullahi ta ce "Wallahi kuwa komai irin d'aya" Hafsa ta ce "ba abin mamaki ba ne ai, saboda tun jiya da muka je gidanku na ga abayar Khadijatullahi a kan gado kawai naji jikina ya bani ita zaku saka yau sai na k'are mata kallo Allah yasa naga kwalliyar jikin abayar duk da cewa ba duk na gani ba, shine muna tafiya na tsaya na saya a wani super market, murmushi suka yi gaba d'ayansu sannan suka nufi hanyar ajinsu domin an kusan fara lecture, basu dad'e da shiga ba Malam ya shigo suka fara lectures.

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now