EPISODE 8

281 17 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA❤️❤️❤️❤️❤️*

_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

*Wattpad@Naanarh2021*

Assalamu alaikum 'yan uwana barkanmu da safiyar jumma'a Allah ubangiji ya bamu albarkar da ke cikinta Amin, Masoyana Ina son kusani a duk inda kuke Naanah tana sonku sosai Kuma ba za ta tab'a d'ena sonku ba har jumma'ar da Bata da Asabar❤️ Jumma'at Mubarak🕌

_Labari Mai tab'a zuciya_

Shafi na 8

Jabir ya d'auki kusan mintina 30 yana buga kofar tare da kiran sunan Aliyu amman shuru babu alamar za'a bud'e kofar kamar ance ya lek'a window sai ya ga kofar baya a bud'e take anan take ya ce "Mami kofar bayan d'akin Aliyu a bud'e take ko dai ya bar gidan nan ne" yayi maganar cike d tashin hankali, da sauri Mami ta mike ta zagaya suka bita a baya d'akin ta shiga ta shiga duba ko ina a d'akin amman babu Aliyu babu alamar sa, hakan yayi matuk'ar tayarwa da Hajiya Asiya hankali domin Aliyu bai tab'a fita ba tare da ya sanar da ita ba "to kodai Aliyu barin gidan yayi ya koma dubai" anan take ta zubai a kan gadon tare da dora hannu a kai, ta fashe da wani wahalallen kuka, Jabir kuwa wayarsa ya zaro a aljihu ya shiga kiran number Aliyu, amman a kashe, fita yayi da sauri bai zame ko ina ba sai wajen da aka tanada domin ajiye motoci, ya shiga d'aya daga cikin jerin motocin wacce ta kasance ta hajiya Asiya ce amman yaran nata suna d'aukar motar idan zasu fita, gidan kakarsu Hajiya Mama ya nufa domin duba Aliyun ko yana nan, yana zuwa ko sallama bai yi ba ya shiga kai tsaye, falon Hajiya Mama ya shiga ya tarar da ita tana kallo ta kishin gid'a a kan kujera, babu gaisuwa babu sallama Jabir ya ce "Hajiya Mama Aliyu yazo gidan nan kuwa" a zabure Hajiya Mama ta tashi har tana kok'arin fad'uwa, domin ko motsin shigowarsa bata ji ba, cike da bak'in cikin irin rashin tarbiyyar da Jabir bashi da ita ta rufe shi da fad'a "Kai wai meyasa baka da hankali ne kawai ka shigowa mutanan gidan zek'ek'e kamar wani bayahude, Aliyu da Shahida k'annanka ne amman sun fika hankali domin inda sune ba zasu tab'a shigowa ba tare da sunyi sallama ba, kuma suna shigowa kafin su fad'i abin da ya kawo su sai sun gaishe ni tukunna, daman wannan me kama da arnan bakin titin halinku d'aya" tana nufin Nihal domin haka take ce mata.

Jabir ya ji haushin maganganun Hajiya Mama dan sunyi matuk'ar kona masa rai, koda ya ga alamar Aliyu baya gidan ya ja tsaki sannan ya fita daga gidan a fusace yana jin Hajiya Mama tana cewa "uwarka ka yiwa tsaki mara tarbiyya kawai". Haka ya shiga motarsa ya ja ta sa k'arfi sai huci yake kamar wanda yaje dambe, kai tsaye club ya nufa, yana zuwa bai shiga cikin club d'in ba ya huce hostel d'in d'akinsa ya huce ya bud'e ya shiga, fridge ya nufa ya bud'e ya d'auko giya ya balle murfinta cikin zafin nama ya shiga kwank'wad'arta har sai da ya shanye gaba d'aya, haka ya k'arasa kan gadon yana tangad'in ya fad'a gadon, yana kwanciya wani amai ya taho masa ya mik'e dakyar da niyyar ya shiga toilet ya zube a kan carpet ya shiga kwara wani irin bak'in amai, sai da ya gama sannan ya mik'e ya koma kan gadon bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Alhamdulillahi jikinta yayi sauk'i dan har tana yin hira sama-sama dasu Aunty Murja, ganin yadda jikin nata yayi sauk'i ne doctor Halima ta rubuta musu takardar sallama, suka koma gida suka cigaba da lura da Khadijatullahi, b'angaren Inna larai kuwa tunda Amatullahi tayi mata wannan aika-aikar ta fita ta shiga kurma ihu da neman taimako tayi sa'a kuwa d'anta lado ya shigo gidan yaga yanayin da take ciki dan har fuskarta ta fara sabulewa, a gigice ya k'arasa gurin da take a bage yana tambayarta "Inna meyafara wa yayi miki wannan aika-aikan" cikin rawar muryar ta bud'e bakj dakyar ta ce "Ama....Amatullahi ce lado ka taimkeni ka kaini asibiti" lado kuwa ransa ya b'aci matuk'a "wato rashin mutunci Amatullahi har ya kai ga ta illatawa mahaifiyarsa fuska" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuwa ya ce "Wallahi wallahi na  rantse miki da girman Allah Inna kamar yadda Amatullahi ta kona miki fuska wallahi nima sai na kona mata", (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace lado kayi sauri ka kai mahaifiyarka asibiti kar fuskar ta rub'e domin kuwa Amatullahi ba kanwar lasa bace dai-dai take da kai😂🤸🏽‍♀️).

Haka Lado ya d'auki mahaifiyarsa a hannunsa ya nufi waje yayi sa'a yana fita ya tarar da abokinsa Tanimu a cikin motarsa da alama fita zai yi, Lado ya tsayar dashi da sauri, Tanimu ya tsaya Lado ya saka mahaifiyarsa sannan shima ya shiga, yana cewa "Tanimu dan Allah kaimu asibiti mafi kusa damu wallahi wannan shegiyar yarinyar ce ta hankad'a Inna cikin mai", cikin nuna damuwarsa Tanimu ya ce "Subhanallahi gari yaya haka ta faru" tsaki Lado ya ja cike da takaici ya ce "to wannan hatsabibiyar yarinyar ma har a tambaya garin yaya hakan ta faru, wallahi wannan yarinyar idan bata yi wasa ba siyar da ita zan yi kowa ya huta", dariya ce taso  ta kwacewa Tanimu amman ya had'iye a zuciyarsa yana cewa "Kai banda abin ka Lado ai wannan yarinyar wallahi bata siyu ba dan duk wanda ya siyeta ya siyi jafa'i dan da kansa zai dawo da ita ya ce ya fasa". Abin da yasa Tanimu ya ce haka akwai wata rana da kanwarsa taje ta tsokani Amatullahi har gida Amatullahi taje ta zagesu gaba d'aya tare da cewa Innarsu "bata iya bada tarbiyya ba", Wani asibiti mai suna *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* suka tsaya Lado ya fita da Innarsa ya shiga asibitin yana kiran "nurse! nurse!! nurse!!" Nurses kusan biyar ne suka fito suna tura gadon da ake dora marasa lafiya, Lado ya dora Innarsa ya taimakawa nurses d'in wajen tura innar sukai d'akin tiyata da ita (Allah sarki Inna larai anji bala😂😆). Haka su Tanimu suka zauna har tsawon awa d'aya babu wanda ya fito domin sanar dasu halin da Inna Laran take ciki, Tanimu ya kalli abokin nasa ya ce "Abokina zanje gurin Mama saboda zan kai ta unguwa kuma na barta tana ta jirana" Lado ya sauke ajiyar zuciya ya ce "to Abokina babu komai dan Allah ka mik'a min gaisuwata gurin Mama", "Insha Allahu" Tanimu ya fad'a tare da nufar kofar fita daga asibitin, Lado ya zabga tagumi zuciyarsa cike da tsanar Amatullahi, da kuma d'aukar fansar abin da tayi wa Innarsa.

*'BANGAREN JABIR*

Jabir bai tashi daga baccin ba sai wajen k'arfe uku, ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan wasu kyawawan yammata guda uku kowaccensu sanye take cikin kananun kaya riga da wando, wani kayatatcen murmushi yayi tare da kirawo sunansu "Leemsha, summy,Ammi" kowaccen su ta amsa da "Na'am sweety". Jawo su yayi jikinsa yana shafasu suma suna mai dar masa martani (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace na shiga uku Jabir sai kace bursuru🙆🏼‍♀️),"Leemsha wacce ta kwanta a kan k'irjinsa tana tana kissing d'in lips d'insa ta ce "Sweetheart meyafaru da kai ne, dan naga kabar kofa a bud'e kuma nasan indai kazo kabar kofa a bud'e kana cikin damuwa ne"

Cikin wata iriyar murya mai wani irin salo mai d'aukar hankali ya ce "Wallahi wata tsohuwar banza ce ta b'ata min rai", Leemsha kuwa bata k'ara cewa komai ba, suka shiga yin bad'alarsu.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Yanzu Khadijatullahi ta fara sakin jikinta kuma ta rage yin koke-kokenta Amman kuma kullum ne babu ranar banza sai tayi wa Jabir mugayen addu'o'i tare da tsine masa, Amatullahi kuwa tunda ta koma gida taga babu kowa tayi wata shegiyar dariya tare da cewa "Yau asibiti yayi d'iba kenan, ai Inna Larai kad'an kika gani indai zaki dinga zagin iyayena zan cigaba da baki wahala wallahi".

Yau kamar kullum suna zaune Amatullahi ta ce"Aunty Murja ya kamata mu fara shirye-shiryen makaranta domin nan da Sati d'aya insha Allahu zamu fara lecture" Khadijatullahi ta kalli Amatullahi domin kuwa ita har ta manta da sun sami admision ta ce "Amatullahi ni na hak'ura da zuwa makarantar kawai ke ki tafi" nan da nan hawaye ya fara zuba daga idon Amatullahi cikin muryar kuka ta fara magana da cewa "kina tunanin zan iya zuwa makaranta ba tare da ke ba, tun muna yara muke tare komai namu tare muke yinsa tun daga primary har zuwa yau babu abin da nake iyawa ba tare da ke ba yanzu kuma ina murna zamu fara zuwa makaranta zamu cigaba da kasancewa tare shine rana tsaka zaki ce min ba zaki je ba ai shikenan nagode sosai" tana gama fad'ar haka ta tashj ta fita daga gidan da saurinta tana kuka, hankalin Khadijatullahi ya tashi mik'ewa tayi ta d'auki hijabi ta saka duk sa cewa bata jin dad'in jikinnata haka ta bi Amatullahi domin ta bata hak'uri, Aunty Murja ta bisu da kallo tabbas k'awancen nasu yana matuk'ar burgeta "Allah ubangiji ya barku tare har abada". Ta fad'a a fili tana murmushi...

*Anan zan tsaya sai ku dakace ni gobe in Allah ya yarda ina k'aunarku sosai wallahi❤️ kuna min comments sosai ku cigaba da yi min comments nima na cigaba da yi muku typing mai tsayi❤️❤️ kuma dan Allah duk da nasan kuna sharing ku cigaba da yi min hakan zai sakani cikin farin ciki sosai❤️❤️*

*Please🙏🏽*

*Share*
*Comments*

*'Yar mutanan zazzau ce❤️❤️*

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now