EPISODE 7

329 19 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA❤️❤️❤️❤️❤️❤️*

_Daga alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*

*Wattpad@Naanarh2021*

_Labari mai tab'a zuciya_

Shafi na 7

Aliyu ne kwance a kan gadon d'akinsa wanda tunda Mami ta mareshi ya shiga ya rufe kansa bai k'ara fitowa ba gashi har safiya tayi kusan k'arfe 10am na safe ko abincin dare bai ciki ba sai ruwa da ya bud'e fridge ya sha kad'an, maganar da d'an uwansa ya fad'a masa ce da yake tambayarsa jiya da yarinyar tazo gidan ta shiga dawo masa "wata yarinya ce da muka yi Auren wucen gadi da ita" shi abin da bai gane ba shine me Jabir yake nufi da auren wucen gadi, shin yayi aure ne ba'a fad'a masa ba kuma da duk alamu indai yayi auren da gaske to Abbansu ma bai san yayi ba, dan inda ya sani zai fad'a masa, da ya ga zai tak'ura kansa da tambayoyin da bashi da amsa ya watsar dashi,sannan ya tashi ya shige toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata had'addiyar shadda marun colour, kyau iya kyau ya riga da yayi ya fesa turare sannan ya fita ta kofar baya domin kuwa baya k'aunar ganin kowa daga cikin 'yan uwan nasa da mahaifiyarsa,motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya ja motar ya nufi gidan Abokinsa Musbahu.

*'BANGAREN KHADIJATULLAH*

Tun da ta tashi take kwarara amai daman gashi babu komai a cikin nata dan haka aman ma dakyar dake yinsa duk ta gama galabaita, Aunty Murja ce taje ta kirawo doctor Halima saboda ganin amai yak'i tsayawa, koda doctor Halima tazo ta ga yanayin da take, allura tayi mata wacce zata tsayar da aman ko minti 5 ba'ayi ba aman ya tsaya, kwantawa tayi tare da jero ajiyar zuciya, suna yi mata sannu tana amsa musu da kai doctor Halima ta ce "karku bata abinci yanzu ku bari sai wajen 12am sai a bata tea mai zafi tunda kun ga yanzu k'arfe 10:30am na safe" suka amsa da "to insha Allahu, zamu kiyaye" daga nan doctor Halima ta fita ta koma office d'inta, Amatullahi ta kalli Aunty Murja ta ce "Aunty Murja bari inje gida daga nan na taho mana da abincin da zamu ci" murmushi Aunty Murja tayi sannan ta ce "To Amatullahi" ta shi tayi sannan ta ce mata "Sai na dawo", "A dawo lafiya" Aunty Murja ta fad'a fuskarta d'auke da murmushi, fita Amatullahi tayi da saurinta tana fita daga asibitin ta dad'e a bakin titi duk mai adaidaitar da zata gani a cike yake da mutane, ta tafiya tayi domin ta ga idan ta tsaya ba zata samu masu adaidaita ba, Ai kuwa tayi sa'a ta hango wani mai adaidaita babu kowa a cikinsa da sauri ta tsayar dashi ta shiga tare da yi masa kwatancen gidansu, sai da mai adaidaitan ya kai ta har kofar gida sannan ta biyasa ta shiga gidan bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Inna larai wacce take gaban murhu tana had'a wutar girki tayi mata wani irin kallon k'ask'anci ita ma Amatullahi ta mai dan mata da martanin kallon nata,ba tare da ta amsa sallamar ba ta ce "to 'yar gantali ina kika je kika kwana saboda tsabar rashin kamun kai irin naki da wannan shegiyar uwar taki bata koya miki tarbiyya ba har ki je ki kwana a wani wajen koda yake naji ance dangin nata gaba d'aya 'yan bariki ne anyi gadon tsiya" tayi maganar tana d'ora tukunyar ruwan kokon da zata yi, fusata iya fusata Amatullahi ta riga da tayi,tana raye a gabanta a zagi mahaifiyarta kuma har ace danginta 'yan bariki ne ace bata d'auki mataki ba "Lallai yau akwai bala'i" ta fad'a a cikin zuciyarta, wucewa d'akinta tayi wanka tayi ta chanza kayan jikinta sannan ta fito, lokacin har Inna larai ta gama dama kokon tana soya kosai, wani irin murmushin mugunta Amatullahi tayi sannan taje ta zauna a kan 'yar k'aramar kujerar k'arfe ta dora k'afa daya kan d'aya, cikin jin haushin Amatullahi Inna larai ta ce "Wai ke rashin tarbiyyar taki har ta kai ina aiki ba zaki zo ki k'arb'a ba, koda yake ba laifinki bane laifin wannan k'anjamamman uban naki ne, daga anyi magana sai ya ce ke marainiya ce to uban waye ba marayan ba" magana take cikin fushi, ita dai Amatullahi ba ce komai ba sai murmushi take domin kuwa yau zata koyawa Inna larai hankali "daga yau ba zaki sake bud'ar baki da niyyar zagin iyayena ba, sai nayi miki abin da zaki fi wata d'aya kina jinya baki warke ba" Amatullahi ta fad'a tana 'yar dariyar mugunta sai da ta gama soya kosan gaba d'aya Amatullahi ta tafi gadan-gadan ta hankad'a Inna larai ta fad'a kan wannan man da ta gama suyar kosai gaba d'aya man ya kelayo mata a fuskarta, Amatullahi ta d'auki wannan koko da kosan ta fita domin komawa asibitin tana fita ta bata samu mai adaidaita ba har sai da taje bakin titi ta shiga tace masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaitan ya amsa da "to hajiya" suna isa bakin asibitin nasarawa Amatullahi ta ga Aunty Murja ta fito daga cikin asibitin bayan ta sallami mai adaidaitan ta nufo gurin da Aunty Murjan take da sauri tana cewa "Aunty Murja ina zaki?" k'arb'ar bokitin kokon tayi tare da cewa "Liptom da sugar na fito na siya domin a had'awa Khadijatullahi ta sha, kamar yadda doctor tace naga sha biyun takusa, Amatullahi ta mik'awa Aunty Murja bokitin kosan sannan ta ce "Kawo naje na siyo, ki koma ciki Khadijatullahi tana buk'atar wani a kusa da ita bai kamata mu dinga tafiya muna barinta ita kad'ai ba, Aunty Murja ta k'arbi bokitin kosan sannan ta bata kud'in da fad'a mata abubuwan da suke buk'ata da zata siyo, Amatullahi ta nufi shagon da yake jikin asibitin domin siyo kayan da Aunty Murja ta fad'a mata, ita kuwa Aunty Murja ta koma cikin asibitin, Amatullahi tana gama siyayyar ta nufi cikin asibitin d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi ta nufa ta shiga da sallama, suka amsa mata ta k'arasa ta bawa Aunty Murja siyayyar da tayi sannan ta koma gurin da Khadijatullahi take kwance ta d'agota ta taimaka mata ta zauna sannan ita ma ta zauna Aunty Murja ta had'a mata tea ta mik'owa Amatullahi ta ce "Gashi bata ta sha", k'arb'a Amatullahi tayi ta shiga bawa Khadijatullah tea d'in sai da ta koshi ta ture kofin daga bakinta Amatullahi ta ce "Kin koshi ne" kai ta gyad'a mata alamar "Eh" Amatullahi ta ajiye kofin a kan d'an k'aramin teburin da yake d'akin ta sauka k'asa domin ta zuba musu koko da kosan ita da Aunty Murja su ci, Aunty Murja sauka k'asan tayi ita ma tare da cewa "Kin ga tsaya muci a faranti d'aya ba sai kin raba ba" Amatullahi ta ce "to" suna ci suna hira har suka gama abin gwanin ban sha'awa.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Zaune suke a kan dinning table suna yin breakfast Mami ta kalli Jabir tare da cewa "Aliyu ya fito kuwa" tab'e baki Jabir yayi tare da cewa "tun jiya da ya shiga d'aki bai fito ba har yanzu" dafe k'irji Mami tayi tare da cewa "na shiga uku Aliyu na" da sauri ta nufi bangaren Aliyu har tana tuntub'e, rufa mata baya sukai gaba d'ayansu, Mami tana zuwa ta shiga bugun kofar tana kiran sunan Aliyu, "Aliyu! Aliyu!! Aliyu!!!" Amman shuru zub'ewa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka "Wayyo Aliyu na ka bud'e kofar dan Allah kayi hak'uri" Shahida da Nihal suka zauna kusa da Mamin suna rarrashinta Jabir kuwa cikin zafin rai ya shiga buga kofar kamar zai k'arya "Aliyu ka bud'e kofar nan idan ka bari na k'arya kofar nan ba zaka ji da dad'i ba".

"Aliyu ka bud'e kofar nan nace maka"...........

*Anan zan tsaya sai ku dakace ni gobe insha Allahu yawan comments yawan typing*

*Ina matuk'ar godiya da irin comments d'in da kuke yi min thanks alots dan Allah ku dinga yi min sharing pls🙏🏽*

*Please🙏🏽*

*share*
*comments*

*'yar mutanan zazzau ce💓💓💓*

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now