EPISODE 13

257 14 0
                                    

*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭😭❤️*

_Daga Alk'alamin_
~*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban*~

_Labari mai tab'a zuciya❣️_

Shafi na 13

"Kamar yadda kika sani sunana Khadijatullahi Abbakar Mai yak'i iyayenmu mu biyu suka haifa daga ni sai Aunty Murja wacce ta kasance yayata kuma mahaifiyata, Mahaifina Abbakar mai yak'i yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado domin yana tafiye tafiye zuwa wasu garuruwar ya saro shanuwa ya dawo ya siyar dasu anan garin kano, wannan abin ne yasa gaba d'aya 'yan uwansa suka tsaneshi duk da cewa ciki d'aya suka fito da su, suke nuna mana tsana sosai har ya kasance bama zuwa gurinsu, mahaifiyar babbana da mahaifinsa sun rasu tun kafin babbana ya yi aure sakamakon gobarar da suka yi a gidan cikin dare gaba d'aya suka k'one, ranar wata lahadi ranar da bazan tab'a mantawa da ita babbana ya yi tafiya zuwa zaria domin saro shanuwa, sai gawarsa aka kawo mana ya rasu sakamakon hatsarin da suka yi motar da su babbana suke ciki wata gingimari ta daki motar babu wanda ya rayu dan har driver mutuwa ya yi, lokacin da innarmu ta ga gawar babbana ta yanke jiki ta fad'i ko da muka kai ta asibiti aka shiga da ita emergency room muna nan zaune sai aka fito da ita fuskarta a lillib'e da sauri na k'arasa gurin likitan jikina na rawa nake tambayarsa meyasa suka rufewa innata fuska, ku yi hak'uri domin Allah ya karb'i abinsa abin da likitan suka ce mana kenan, nan Aunty Murja ta fasa ihu ta zube a k'asa tana rusa kuka, nima naje kusa da ita na k'ank'ameta ina kuka, haka muka dawo gida mak'obtanmu suka shigo aka yiwa inna da babba wanka aka kai su makwancinsu na gaskiya, haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya muna zaune a gidanmu daga ni sai Aunty Murja duk duniyar tayi mana zafi" A dai-dai nan Khadijatullahi ta tsaya saboda jin k'arar kad'ai k'ararrawar komawa aji "to bari in tsaya anan idan mun fito lokaci bai k'ure ba sai in cigaba idan kuma lokaci ya k'ure gobe idan Allah ya kaimu sai in k'arasa miki" Khadijatullahi tayi maganar cikin muryar kuka.

Hafsa ta ce "Ko lokaci ya k'ure ma sai in bi ku har gida dan yau sai naji labarinki gaba d'aya sannan zan tafi gida" tayi maganar ita ma hawaye na kok'arin zubo mata share hawayen tayi sannan ta matsa kusa da Khadijatullahi ta kama hannunta ita da Amatullahi suka tashi suka nufi ajin zuciyoyinsu cike da bakin ciki.

Wajen k'arfe shida suka tashi daga makarantar suka fito bakin gate Hafsa ta kirawo Mommy a waya ta ce mata yau ba zata samu dawowa da wuri da zata biya gidansu Khadijatullahi da yake Mommy ta san labarin su Khadijatullahi dan haka ta ce to shikenan bakomai, mai adaidaita suka tara ya kai su har kofar gida Hafsa ta biya kud'in, suka shiga gidansu Khadijatullahi amman abin mamaki basu tarar da Aunty Murja ba, Khadijatullahi ta ce "To ina Auntyna taje" Amatullahi ta ce "haba besty kila taje wani gurin ne" haka suka zazzauna a kan taburmar Hafsa ta ce "wallahi har na k'agu in k'arasa jin labarinki" wani murmushi mai ciwo Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Yanzu kuwa zaki ji labarina gaba d'aya" Khadijatullahi ta fad'a cikin wani irin yanayi sannan ta fara magana.

"ranar wata jumma'a muna zaune a tsakar gida ni da Aunty Murja lokacin kwanan su babbana hamsin da mutuwa sai ga Kawu Sani ya shigo gidan ko sallama babu mun yi mamaki sosai da ganinsa domin tunda su babbana suka mutu babu wanda yazo daga cikin 'yan uwansa wani matashin saurayi ne wanda kana kallonsa zaka san naira ta zauna wasu k'ananun kaya ne a jikinsa wanda ni a ganina dasu gwara babu, yake biye dashi a baya su Kawu lawan da Kawu Sanusi suna biye dashi a baya mik'ewa muka yi tsaye muna musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa mana daga cikinsu sai ma kallon k'ask'anci da suke bin mu dashi, gaba d'aya na tsargu da irin kallon da wannan saurayin yake min, Aunty Murja ta nufi d'aki da niyyar d'auko taburma ta shimfid'a musu Kawu Sani ya dakatar da ita da cewa Ke Murja ina zaki je Aunty Murja ta ce taburma zan d'auko muku cikin tsawa ya ce ba zama ne ya kawo mu ba, mun zo ne mu sanar da ku cewar mun yiwa Khadijatullahi miji nan da sati d'aya za'a d'aura auren kuma ba kowane mijin ba sai wannan ya nuna wannan saurayi tare da cewa sunanshi Jabir ya ga Khadijatullahi yazo har gurinmu ya nuna yana son ya aureta, wani irin ihu na kwalla tare da cewa dan Allah Kawu kayi min rai wallahi bana son shi baka ganshi ba kalli kayan da ya saka fa, wani irin zafaffan mari Kawu Lawan ya wanke ni dashi wanda har sai da na rasa ganina na 'yan mintinue, da sauri Aunty Murja ta jawoni ta rumgumeni tare da dafe kan kuncina inda Kawu Lawan ya mareni, dan ubanki bakin ciki zaki yi mana shagiya mai mugun hali irin na ubanta, kai Jabir gata nan ko yau kake so a d'aura aure zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari, wani irin shu'umin murmushi yayi sannan ya kalleni muka had'a ido ya kanne min ido d'aya, su Kawu Sani suka fita amman shi Jabir bai fita ba sai wani irin kallo da yake min wanda kana ganinsa zaka san na cikakkun 'yan bariki ne matsowa ya yi daf dani yana kok'arin kama min hannu nayi saurin komawa bayan Aunty Murja murmushi ya yi sannan ya ce dijarh kenan son kud'in wad'annan matsiyatan Kawun naki yayi yawa dan haka ki sani yanzu ina zuwa na sakar musu kud'i nace a yanzu nake son a d'aura mana aure da gudu zasu yarda kuma karki wani damu indai hannunki ne nan da sati d'aya zan yi duk abin da nake so a jikinki nasan dai kin san abin da nake nufi zan d'and'ani zumarki duk da cewa Auren wucin gadi zamu yi yana gama fad'ar haka ya fita daga gidan na rik'e Aunty Murja ina kuka sosai kamar raina zai fita, zaunar da ni tayi tare da rumgumeni a jikinta cikin muryar kuka nake ce mata Aunty Murja na shiga uku dan Allah ki yi duk yadda zaki yi kar in auri wannan d'an iskan, ita ma cikin kuka ta ce ba za ta iya hana auren nan ba saboda indai tayi yunkurin rama auren hakan zai iya jawo mana babbar matsala muna cikin wannan yanayin sai ga Amatullahi ta shigo nan na zai yana masa komai ita ma ta shiga yin kuka, haka dai muka kasance cikin tashin hankali har sati ya zagayo, da misalin k'arfe 10 na dare sai ga su Kawu Sani da Jabir kamar dai yadda suka zo ranar farko da yake lokacin zafi ne mun yi shimfid'a a tsakar gida muna shirin kwanciya da sauri na tashi ta koma bayan Aunty Murja jikina na rawa, Kawu Sani ya ce to kamar yadda muka zo muka sanar da ku satin da ya wuce za'a d'aura auren Khadijatullahi da Jabir to yau an d'aura kuma yanzu yazo tafiya da matar sa ne, kuka na saka mai had'e da ihu Amman haka Kawu Sani ya finciko ni daga bayan Aunty Murja ya tura ni gurin Jabir kamar jira yake ya kama hannuna ya rik'eshi sosai sannan ya nufi kofar fita, haka muka fita daga gidan ina tirjewa har muka isa gurin motarsa ya bud'e ya turani ya rufe motar ya koma mazaunin driver ya shiga ya ja motar mun yi tafiyar kusan awa biyu har muka isa wani babban gida gate mai gadi ya bud'e gidan a wajen da aka tana da dan yin parking yayi parking d'in motar ya bud'e motar ya fito ya zagayo inda nake a bayan motar ya bud'e ya jayo ni, yana jana ina tirjewa har muka isa wata kofa wacce ta sadamu da wani tafkeken falo kai tsaye wani babban bedroom ya nufa dani ya wurgani kan gadon sannan ya cire kayan jikinshi ya rage daga shi sai gajeran wando dakyar na iya tashi saboda yadda ya wurgani kan gadon sai da na bugu da bakin gadon haka Jabir yayo kai na ganin haka yasa na shiga kok'arin kare kai na ina d'aukar duk abin da yazo min hannuna ina wuraga mishi, tsayawa Jabir yayi cak ganin haka yasa na dena jifanshi ina nuna shi da yatsa ina cewa karka matso kusa dani, murmushi yayi tare da fad'awa kan gadon ya bage yana kallona, juyawar da zan yi in mayar da kwalbar da na d'auka kawai naji Jabir ya jawo ni na fad'a kan gado ya hau kai na yana murmushin mugunta yana cewa kinga ai kin shigo hannuna sai yadda nayi dake zan ci in more sosai yayi maganar yana kanne min ido, tureshi na shiga kok'arin yi ina kuka amman ina Jabir ya riga da ya sakar min nauyinsa gaba d'aya, Jabir bai d'aga ni ba har sai da ya rabani da budurcina, haka ya tashi ya shiga toilet yayi kusan mintune goma sannan ya fito d'aure da towel har sai da ya gama shiryawa sannan ya nufo gurin da nake kwance ya miko min wata farar takarda yana murmushi, zaki iya tafiya gidan ubanki, tashi nayi dakyar hawaye na bin kuncina na bud'e takardar _Ni Jabir Mansur jikamshi na sake ki saki uku_ abin da aka rubuta a takardar kenan wani irin kuka na saki ina kallonsa haka na saka kayana kamar jira yake in gama saka kayana ya dinga ja na har sai da muka fito farfajiyar gidan sannan ya ce bari in turo miki 'yan rakiya domin su rakaki har gida ko, ya zagaya bayan gida sai gashi da wasu karnuka sun kai guda biyar manya manya sai haushi suke nan karnukan nan suka nufo inda nake da mike dakyar domin tsiratar da kai na na shiga guda mai gadi ya bud'e min kofa da sauri na fita haka ina gudu karnukan nan suna bi na gashi dare yayi kowanne gida na huce a rufe ya ke babu kowa a unguwar daga ni sai wad'annan karnukan,har Allah ya kawo min wani mutum yazo wucewa a mashin ganin yadda nake gudu karnuka na bi na ya ce in hau mashin d'in haka na hau mashin d'in dakyar ya ja mashin d'in da gudu sai da muka yi nisa sannan yake tambayata daga ina nake? Ina kuka na sanar dashi komai ya tausaya min sosai dan haka sai da ya kai ni har kofar gida nayi masa godiya na k'arasa gidan, ina tura kofar na tarar a bud'e take na shiga gidan a inda muka bar Aunty Murja a nan na same ta na fad'a kanta ina kuka nan ta d'ago ni tana tambayata meyafaru cikin daren nan yanzu kusan k'arfe 2 kika dawo? na fad'a mata duk abin da Jabir yayi min ta rumgume ni tana kuka tana cewa ashe Auren wucin gadin da ya ce zaku yi wannan yake nufi Allah ya isa tsakaninmu dashi".

Khadijatullahi ta kalli Hafsa wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "Hafsa wannan shine labarin abin da Jabir yayi min, wanda ba zan tab'a mantawa dashi ba har abada" Hafsa cikin kuka ta ce "lallai Jabir ya cika zazzalumi,mugu,macuci kuma insha Allahu, Allah sai ya saka miki abin da suka yi shi da su Kawu Sani" Amatullahi wacce take kusa da Khadijatullahi tana kuka ta ce "Ai su Kawu Sani tun ranar da suka zo suka gama yin rashin mutunci Jabir ya tafi da Khadijatullahi suna fita suka had'u da 'yan fashi a hanya suka harbesu babu wanda ya rayu a cikinsu" Hafsa ta ce "Ai daman duk wanda ya zalinci wani Allah ba zai tab'a barin shi ba" sun jima suna zaune kowannan su zuciyarsa fal da bakin ciki had'i da tsanar duk wani namiji, a haka Aunty Murja tayi sallama ta shigo d'akin suka amsa mata Hafsa ta gaisheta "Ina wuni Aunty Murja" ta amsa mata cikin sakin fuska "Lafiya k'alau Hafsa ko?" Hafsa tayi murmushi ta ce "Eh" zama tayi a bakin gadon d'akin tana kallonsu "Hafsa wato saka ki suka yi a gaba suna kukan nasu da suka saba kenan" Murmushin yak'e kawai Hafsa tayi, kiran Mommy ya shigo wayarta tayi sallama Mommy ta amsa sannan ta ce "ga driver nan na turo shi zai zo gidansu Khadijatullahi ya d'auke ki" Hafsa ta ce "to Mommy" Daga nan suka kashe wayar wajen k'arfe 8:00 na dare driver ya aiko a kira Hafsa tayi wa Aunty Murja sallama su Khadijatullahi suka rakata wajen motar sannan suka dawo Amatullahi ita ma tayi wa Aunty Murja Sallama Khadijatullahi ta tashi zata rakata ta hanata ta ce "Haba besty bakomai kawai ki zauna ki huta" daga nan ta fita zuwa gida.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Kwance yake a kan gadonsa yana ta juyi abin duniya ya taru yayi masa yawa yasan Abba sare baya tab'a yin magana biyu, anan take wata dabara ta fad'o masa, wani irin tsalle yayi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi "tabbas wannan dabarar tayi kuma ita kad'ai ce zan yi nak'i auren Teemarh". Komawa yayi ya kwanta wani irin bacci mai dadi ya tafi dashi......

To fa shin wannan wata dabara Jabir ya samu da har yake murna haka hmmm akwai babbar cakwakiya ku dai ku biyoni A gobe idan Allah ya kaimu domin jin yadda zata kaya.

Ina mik'a sakon godiyata gareku masoyana ina k'aunar ku sosai taku a kullum a koda yaushe Khadija muhd Sha'aban.

*Please🙏🏽*

*Share*
*Comments*

*'Yar mutanan zazzau ce❤️❤️*

DAREN AURENAWhere stories live. Discover now