*🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸DAREN AURENA😭💔⚜️🔱*
_Daga Alk'alamin✍🏾_
*'Yar mutanan zazzagawa Naanah M Sha'aban🌸*_Labari mai tab'a zuciya❤️_
*Alk'alami yafi takobi🚴🏽♀️*
Shafi na 23
"Sannu da zuwa, dan Allah ka yi hak'uri" tayi maganar kamar za ta yi kuka, k'arasawa kusa da ita yayi yana murmushi jikinsa ya jawota ya rumgumeta, da sauri ta fizge jikinta daga cikin nasa bakinta na rawa ta ce "Hakan bai da ce ba, saboda ni ba muharramarka ba ce, ba za ka samu damar min irin haka ba har sai an d'aura mana aure" Murmushi ya kuma yi a karo na biyu sannan ya ce "Ai kin san ban tab'a yi miki irin haka ba, saboda nasan ke ba muharramata ba ce, amman yanzu ina da damar yin komai a kan ki, dan haka karki haka ni".
Shuru Aunty Murja tayi tana cewa "ban fahimci me kake nufi ba, dan Allah ka fahimtar da ni" jawota yayi jikinsa wannan karon bata yi yunk'urin hanashi ba,wayarsa ya d'auko ya kunna vedio da ya saka a ka yi a d'aurin aure ya ba ta a hannunta tana kalla, muryar liman ta ji yana cewa "An d'aura auren Alhaji Mansur jikamshi da Murjanatu Abbakar mai yak'i a kan sadaki naira dubu dari biyar" da sauri ta d'ago tana kallonsa tana cewa "wai da gaske ne, ba mafarki na ke ba an d'aura aurena da kai, idan har mafarki na ke yi zan so ace na dauwama cikin mafarkin nan ba tare da na farka ba" Sumbatarta yayi a goshi sannan ya ce "da gaske ne ba mafarki kike yi ba Amaryata, amman ni har yanzu ina fushi da ke sosai wallahi" idanuwanta suka ciko da kwalla ta ce "ka yi hak'uri","ni ba zan hak'ura ba, kawai ki fad'a min kuma me?" idanuwanta ta rufe a hankali ta ce "kuma ina sonka sosai" wani irin farin ciki ne ya kama shi ji yake kamar anyi masa albishir da gidan aljanna "nima ina sonki Murjanatu" ya fad'a cikin wani irin yanayin farin ciki.
Muryar Hajiya Mama suka ji tana kiranta da sauri ta bud'e ido tana kok'arin zame jikinta domin zuwa kiran Hajiya Mama, amman Alhaji Mansur ya k'i barinta ta je domin ya rumgumeta sosai a jikinsa "Dan Allah ka bar ni naje kiran da Hajiya take min","idan kina so na cika ki,ki je to ki fad'a min wani suna zaki dinga fad'a min, dan na fuskanci bakya son kirana da kowane irin suna" Aunty Murja ta yi shuru cike da jin kunya a zuciyarta tana cewa "lallai wannan mutumin na fuskanci d'an soyayya ne, ga rigima iri-iri a cikinsa" Amman a fili ba ta iya cewa komai ba, jin alamar Hajiya Mama tana kok'arin fitowa daga d'akin ta ce "Yaya zan dinga cewa maka" tayi maganar da sauri tana juya bayanta tana kallon falon dan ba ta son Hajiya Mama ta fito ta gansu a haka.
"To naji har a gaban kowa haka zaki dinga ce min?" Ta gyad'a kai alamar "eh" cika ta tayi dai-dai lokacin Hajiya Mama ta fito daga d'aki ganinsu a tsaye yasa tayi murmushi "Ashe Amaryar tana gurin Angonta shiyasa nayi ta kiranki na ji shuru" Aunty Murja kunya duk ta kama ta kamar ta nutse a k'asa, tsintsiyar ta tsugunna za ta d'auka domin ta cigaba da shara Hajiya Mama ta kira sunanta "Murjanatu ki bar sharar nan zan k'arasa ki zo ki shiga bayan gida ki yi wanka ki zo ki shirya anjima za'a yi walima","To" abin da Aunty Murja ta ce kenan sannan ta huce d'akin domin ta yi wanka kamar yadda Hajiya Mama ta ce mata.
Shi kuwa Alhaji Mansur a tsakar gidan ya shimfid'a taburma suka zauna da Hajiya Mama suna hirarsu ta d'a da uwa, su Amatullahi da Khadijatullahi ne suka yi sallama domin yau sun ji Aunty Murjan ta dad'e sosai ba ta dawo ba shiyasa suka biyo bayanta "Lale da zuwa 'yan tagwaye wato yau kun ji auntyn ta ku shuru ba ta dawo ba ko?" Hajiya Mama tayi tunanin Amatullahi da Khadijatullahi 'yan biyu ne shiyasa take ce musu tagwaye"Eh Hajiya mun ga har yanzu k'arfe sha biyu na rana kuma idan ta koma tana dawowa k'arfe biyu shiyasa muka zo mu taimaka mata da aikin" Amatullahi ta fad'a sannan suka tsugunna suka gaishe da Hajiya Mama da Alhaji Mansur.
Suka amsa fuskarsu cike da fara'a Hajiya Mama ta dora da cewa "Ai kuwa daga yau tare da ku zamu dinga zama domin kuwa Auntynku yau an d'aura mata aure anjima kad'an za'ayi walima tana d'aki wanka take yi" Khadijatullahi ta d'ago da sauri tana mamaki "An d'aura mata aure kuma?","Eh Khadija" Hajiya Mama ta bata amsa a takaice, Amatullahi kuwa murna ce ta isheta "Kai Hajiya Mama amman na ji dad'i ya kamata na yi miki kyautar goro" Amatullahi ta fad'a tana murmushi, duk da yanayin da Khadijatullahi take ciki domin tsoro take kar ayi wa Aunty Murjan abin da Jabir yayi mata a daren aurensu sai da maganar Amatullahi ta bata da dariya ta ce "Hajiya karki yarda so take ta mayar da ke tsohuwa kuma fa tasan kin fi ta jii da kuruciya" Alhaji Mansur dariya yayi sosai sannan ya ce "Lallai 'yan k'annan nan na wa sai na zane ku Hajiyan ku ke yi wa tsiya haka" Hajiya Mama ta ce "Kyalesu ai Allah ya kawo mu, zasu fara yi min tsiya" Gaba d'ayansu dariya suka yi sosai.
![](https://img.wattpad.com/cover/282976445-288-k987421.jpg)