🌺🌺🌺🌺🌺🌺
NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺STORY & WRITTEN
By
MeenerhFollow me👉on wattpad @meenerh551
For
Comments
Vote
ShareBismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏
Free book
📄 page 27&28"Iyyeh lallae ma yaya yusuf dinnan kae km meye ruwanka aciki" dariya haydar yayi yace yess sae autar ammi iya wuya muna tare, ban mu kashe, tafawa sukayi had'i da yiwa yaya yusuf gwalo, baki Yusuf ya riqe yace ehh lallae fa zarah abinnaki gaba yakeyi irin wannan watsi hk? Gsky kun watsani agaban baqaqen larabawa.
Karima ce yarinyar baba uwani ta qaraso garesu tace Alhaji yace ku ake jira a dinning za'ayi breakfast, Yusuf ne yace ok gamunan zuwa. Sallama sukayi cikin palourn yayinda na hango wannnan dattijon daya sauka a jirgi sati biyu da suka wuce. Yana zaune akan kujerar dake dinning din palourn, gefenshi na dama wata matashiyar dattijowa ce fara tass, kyakykyawa da ita wacce bazata wuce 40yrs ba, daya gefenshin km wata matashiyace wacce a qiyaste bazata kae wannan ta gefen damar tashi ba, ita km chocolate colour ce, itama da kyanta babu laefi, sae wasu 'yanmata guda 2, daya bazata wuce 22yrs ba, km kana ganinta kasan d'iyar wannan matashiyar farar dattijuwarce, sae wata ita km bazata wuce shekaru 16 ba a duniya, namiji guda dayane a gurin mae suna sadeeq.
Qarasowa dinning arean sukayi, yayinda wannan dattijon yayi murmushi yana mae janyowa kujera r dake kusadashi yace zo my angel ki zauna kusada dadynki, qarasowa zarah tayi tana murmushi tace yauwa dadyna, tsuka safnah tayi wacce ta d'auki hnklin mutanen dake zaune a wannan gurin, Yusuf ne ya dago kae yace keeee safnah da waye kike wannan tsukan iyeehhh? Shiru bata kulashi ba, kee ba magana nake miki ba ya fad'a a harzuqe kasancewar yanada zuciya, dady ne ya d'aga mishi hannu yace Yusuf rabu da ita idan mun gama breakfast ta sameni a palourna. Kowa a gurin shiru yy, saeda aka d'auki kmr mintuna 3, sannan momy tace kae Yusuf meye damuwanka da tsukan datayi kaene kafi kowa kunne ne a gurin, ko mu bamuji bane sae kae? Haba momy ae wannan raenin hnkl ne, waye sa'anta agurinnan ae dama nas.....dady ne yace Yusuf !! Shiru yy sbd ya gane abinda mahaefinnashi yake nufi.
Byn sun gama brkfst dinne dady ya nufi part dinshi yayinda safnah ta mara mishi baya domin zw amsa kiran dayayi mata dazu, zamanshi kenan akan wata lifiyayyiyar kujera 3seater, saega safnah tayi sallama amsa mata yayi sannan tayiwa kanta matsugunni akan wani chinisee carpet, tace dady gani, shiru yayi baece komae ba saeda ya dauki tsawon mintuna goma ya dauka ba tareda yace komae ba, sae dg bisani ya kalleta
, sannan yace ''safnahh" saeda hantar cikinta ta kad'a sannan tace na'am dady, shin inaso ki fad'amin waye kikewa tsaki dazu? Shiru tayi, bazaki bani amsa ba? Inda-inda ta farayi sannan tace dama fa--- dama fa, dama me? Ya fad'a a tsawace, tace dady bada kowa nake b...bata qarasa ba kawae saejin saukar mari tayi agefen fuskarta kafin ta sake wani kwakwkwaran motsi taji an qaramata wani a d'ayan side din, kin raenamin wayo ni sa'an wasankine zakicemin bada kowa kike ba? Toh dg yau ya zama na farko ya zama na qarshe banson nasakeji ko ganin kinyi wani abu makamancin wannan aenasan da waye kike, hk fa ranar dana dawo ma ina ganinki kina harararta kina magana qasa-qasa kawae rabuwa dake nayi she abinnaki harya kae ki fara yiwa mutane tsaki acikin manya? Toh bude kunnuwanki da kyau kijini dg ke har wacce take zugaki kinawa mutane abinda bae daceba duk zanyi maganinku tashi ki fice ki bani guri shashashar yarinya kawae. Da sauri ta tashi ta fice a palourn tana zuwa part din mahaefiyarta kawae ta fara kuka, tashi tayi tace meya faru km, bata kulata ba illa wucewa d'akinta tayi ta kwanta akan gado ta fara kuka kmr wacce akayiwa mutuwa, momy ce ta qaraso cikin dakin hnkl tashe take cewa kee safnah wannan wanne irin iskanci ne hk kinaji ina miki mgn amma kinyi banza dani. Tashi tayi tace momy ynz akan waccar shegiyar yarinyar dady zae mareni hrd wani ya cemin karna sake shiga harkanshi...nan dae ta fad'awa momy qarya da gsky. Momy ce tace lallae Alhaji yana neman tashin hnkl cikin gidannan bari naje na sameshi, ficewa tayi a d'akin fuuuuu.. Safnah tanata qwala mata kira amma taqi kulata, hannu ta sanya akanta tace shikenan nashiga uku.Ko sallama bb kawae sae ganin momy nayi a palourn dady, cikin bala'i ta fara magana tace yanzun dadynsu safnah kak.......wata irin gigicecciyar tsawa dady ya daka mata wacce har saeda momy ta kusa sakin fitsari tsabar firgici don rabonta dataji dady yayi irin wannan tsawar harta manta. Nasan menene ya kawoki sbd hk fice ki bani guri, ita km kice mata ta shirya had'uwa dani. Sad'af- sad'af momy taja jikinta ta fice a palourn don tayi mugun tsorata da yanayinsa don tasan yanada zafi sosae amma saeka taboshi gashi da wani irin kwarjini, wnda a halinda ake ciki yanzu bazata iya tunkararshi ba.
WANENE DADY??
Alhaji Muhammad Tafeedah shine asalin sunan mahaefinshi, asalinsa dan cikin garin kaduna ne, Allah ya azurtashi da arziqin shanu, gonaki, da sauran dabbobi, yanada mata biyu Fatima wacce ake kirada zara'u da Karima, Zara'u itace uwargida tanada yara guda uku Babban d'anta sunanshi Abubakar, sae mae bimasa Auwal, sae qanwarsu mae suna Aisha ana kiranta da shatu. Bayan ita ta haefi 'yan biyu amma basuzo da rae ba dg su km bata sake haehuwa ba.
Sae dayar matarshi Mae suna Karima wacce itace amarya itama tanada yara 3, Fiddausi, Naseeru sae mukhtar.Wannan familyn sun taso cikin soyayya da km gata, saede inda matsalar take an samu rashin jituwa tsakanin yaran karima guda biyu wato Fiddausi da km Naseeru da km yaran Zara'u sam basa qaunarsu ko kadan, hkn ya samo asaline dg hudubarda mahaefiyarsu take musu, amma duk da hkn ita Zara'u takan nusar dasu cewar duk min tsanani da tsagwama kada su kuskura su rabu da 'yan uwansu kasancewarta Mae ilimi 'yar gidan dattawa.
Alhaji Muhammad Tafeeda baeyi karatun boko ba, amma yanada ilimin Arabiyya sosae domin shi dalibine a tsangayar mlm sani, wnd yayi suna sosae wajen koyarda karatun Al-qur'ani da sauran littatafan addini, yayi saukar qur'ani sau biyu a wajenshi, wnd dg bisani ya nuna yanason diyar wajenshi wato Zara'u, km yayi na'am da d'abi'unshi shiyasa ya bashi aurenta, dadin dadawa km sunason junansu sosae.
Kasancewar baeyi karatun boko ba ya sanya yaranshi a private Mae tsada domin su samu karatun zamani sosae. Yayinda Abubakar yafi kowa hazaqa acikinsu sbd ganin jajircewarshi ne ya sanya mahaefinshi ya kaeshi qasar America inda ya karanci Accounting, wanda hakan ba qaramar tsana ya sake janyo mishi ba a wajen 'yan uwansa. Byn ya kammala degree dinshi na farko saeya samu lecturing a jami'ar dayayi degreen, km hukumar makarantar ta bashi schoolarship nayin masters har PhD aciki, kasancewarshi Mae hazaqa. Ya dauki a qalla shekaru 3 yana koyarwa acikin jami'ar, byn ya kammala PhD dinsane mahaefinshi ya umarceshi daya dawo gida Nigeria domin ya taemaki qasar shi bawae ya zauna a wata qasar ba, ba don sunso ba suka kyaleshi ya koma Nigeria din.
Bb wani 'bata lokaci dg dawowarshi ya samu offer a Bayero University Kano( BUK) Wanda ananne Allah ya hadashi da Maryam d'iyar Alhaji Aminu Dan gske, shahararren attajiri Wanda ake lissafoshi acikin jerin gwanon masu arziqi a qasar nan. Ba'a tsaya wani 'bata lokaci ba mahaefin maryam ya bashi aurenta kasancewar ya ganshi yanada nutsuwa, zunyi auren soyayya abinsu, sun dauki a qalla shekaru 5 basu samu haehuwa ba, dg bisani ya sakeyin aure. Ya auri Bilkisu qanwar abokinshi Alhj mustapha bayan aurensu da watanni 4 bilkusu ta samu ciki zokaga murna wajen abubakar itama maryam tayi farinciki sosae.
Kwanaki nata tafiya har cikin bilkisu ya cika wata 8, ba qaramin tausaya mata maryam takeyiba kasancewar cikin yana wahalarda ita sosae, ana cikin hk kwatsamm sae maryam tayi........✍ ✍
More comments
More post😘Cmmnts naku shine zae qaramin qarfin gwiwa😍 idan kunason typing mae yawa da km cgb kunayin comments sosae.
Vote comments & share pls🙏
Meenerh ce ✍
YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Historische Romanelabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...