page 33&34

9 1 0
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
        NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺



STORY & WRITTEN
             By
         Meenerh

Bismillahir rahmanirrahim

Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa 🙏




Free book
📄 page 33&34


Tafe suke itada yarinyar tata sunzo daff da fitane umman najmah ta tsinkayo muryar inna laure tana "cewa yauwa bismillah garin Allah km ya waye yanzu za'a fara yawon tazubar din kenan" ita dae umman najmah murmushi tayi batayi niyyar kulataba saeda taji inna laure ta qara volume din muryarta tana cewa  ahaka dae za'a qare ana yawon karuwanci god'ae-god'ae ko kunya ba'aji? Kodan dama mutuminda ya fito a barikin mahauk......sauran kalmomin sun maqalewa inna laure a maqogoronta ne lokacinda taji an kaemata wata irin wawar cafka a wuyanta,aka shaqe wuyanta sannan aka haye ruwan cikinta aka fara jibgarta.

Qaqarin amae inna laure ta farayi tana burburwa, sakamakon shaqemata wuyada maman najmah tayi, tana cewa nice karuwar koh toh yau zakiga yanda ake karuwanci acikin gidannan sala_sala, ae dama na fadamiki kin kaeni bango bazan sake ragamiki ba ko kadan, shekarata nawa agidannan amma kullum cikin haquri nake dake, toh wlh kinyi kadan ke wacece? Me kike taqama dashi, idan banda qaddara miye zae hadani dake, batun mahaukaciya km wannan kene za'a tambaya ba wani ba.

Wani irin karkarwa jikin maman najmah ya farayi, kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta wani irin wawan naushi ta kaewa bakin inna laure habawa nanda nan jini yace salamu alaykum.

Ganin tana shirin sake kae mata wani dukan ne ya sanya najmah kurma ihu, sannan tayikan mahaefiyarta tana cewa umma don Allah ki kyaleta wayyo Allah, "amma inaaa!!!! Umman najmah kam tayi nisa batajin kira" wani naushin takae mata acikinta, wani irin fitsarin azaba inna laure ta saki tareda fasa wani irin ihu wanda yayi daedae da shigowar baban najmah.

Subhanallah zaenab miye kikeyi haka? Kinsan me kikayi haka kw? Ya qarashe maganar yana mae d'agamata murya.

Sakinta maman najmah tayi sannan ta miqe tsaye ta koma ta jingina da katangar zauren gidan tana sauqe ajiyar zuciya, da wani irin numfarfashi kmr wanda tayi gudun fanfalaqi.

Hnkl tashe baban najmah yake yiwa inna laure mgn, yana cewa laure! Laure!!!! Ki tashi innalillahi, zaenab kinga irinta koh. Gabadaya ya rikice.

Wani irin murmushi maman najmah tayi wanda ake kiransa da yafi kuka ciwo sannan tace Allah sarki rayuwa, yanzu mlm duk cin zalinda akemin acikin gidannan baka gani, babu irin kalar wulaqancin da ba'amin agidannan, akan idonka fa kwanaki tayiwa najmah dukanda ya kusan kasheta amma me? Shin ka tambayi dalilinta na dukamin yarinya? Ko km ka taba tambayarmu cewar munci abinci, yaya lafiyarmu take? Qarewa fa saeda muka shafe tsawon  kwanaki uku a asibiti ko inda hankalinmu yake bamusani ba, amma ko zuwa dubamu bakayi ba, sannan bayan dawowarmu ku ya jiki bata hadamu dakae ba, hasalima nunawa kayi bakasanda zamanmu acikin gidan ba balle musaka ran wani abun, toh don Allah inaso ka fadamin shin wannan adalcine ko km rashin adalci? Ta qarishe tana mae sakin wani marayan kuka, sannan tace wlh Aliyu nayi danasanin aurenka a rayuwata.

Tashi maman najmah tayi sannan ta kama hannun yarinyarta tace "nidae nasani wlh Allah shine shedata km shine gatana.

Sae magana ta qarshe itace dg yau kar wanda ya sake shiga rayuwata data yarinyata tunda kowa acikin gidannan ya ajiyemu a kwandon shara, ko don anga ba nanne gidan ubanta ba shiyasa kowa zae dinga yiwa mutane wulaqancin dayaga dama? Harni wae za'a kirada karuwa? Toh shikenan inshallah dg yau zan fita cikin rayuwarku bazaku sake ganinmu ba balle ku samu damar yimana wulaqancin da kuka sabayimana.
Jikin baban najmah ne yayi sanyi sosae.

NAJMAH by meenerhWhere stories live. Discover now