page 29&30

19 1 0
                                        

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
        NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺


STORY & WRITTEN
            By
        Meenerh

Bismillahir rahmanirrahim

Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏

Kuyi haquri kunjini shiru kwana biyu muna bikineh shiyasa.

Free book
📄 page 29&30

Kwanaki nata tafiya har cikin bilkisu ya cika wata takwas 8, ba qaramin tausaya mata maryam takeyiba sakamakon cikin yana wahalarda ita sosae, ana cikin hk kwatsam wata rana maryam suna zaune a palour suna hira da abokiyar zamanta saega wasu jibga-jibgan mata guda biyu sun shigo cikin palourn cikeda mamaki maryam take kallonsu tace su waye nake gani hk? Kmr su sa'a? Murmushi wannan matan sukayi lokacinda suke yiwa kansu mazauni akan kujerun dake palourn, daya daga cikinsu ne tace abinda idonki ya nunamiki. Bilkisu ne ta musu brk da zuwa, sannan ta fara qoqarin tashi domin ta basu guri su gana amma ta kasa sae maryam ne ta taemakamata sannan ta tashi tana shirin yimata rakiya zw part dinta sae tace aa wlh ki barshi kije kiji da baqinki zanje na kwanta na huta.

Kitchen ta wuce domin kawo musu abinda zasu d'an ta'ba, qusqus naga sunayi suna wani yatsine fuska, shiru naga sunyi lokacinda take nufowa palourn.

Bayan sun gaesane sae maryam take cewa ohh shikenan tunda nayi aure ba'a qarajin d'uriyarku koh? Kedae maryam bari cewar sa'a. " nikam maryam"na tambayeki mana? Cewar kaltum, ok inajinki, meye kikeyi har yanzu baki tafi umrah ba? Byn mahaefinki yana dashi sannan ga mijinki babban lecturer amma kin tsaya kina wasa gashi ke ko d'an business dinnan bakiyi. Sa'a ce ta karb'e zancen ta hanyar cewa nimadae gsky abinda nake gani kenan ki duba fa kigani muda bamu kaeki bama amma zuwanmu wajen nawa, kawae ki shirya tunda an kusa tafiya kiyi vissa saemu tafi tare dagacan mu wuce Dubae kema ki fara business wlh ynz zakiga kinyi popular tunda mahaefinki yana dashi kice ya baki jari kona 5million ne zaki fara business. Murmushi maryam tayi tace inshaallah zamu tafi wannan shekarar tareda mae gidan amma yace sae bilkisu ta haehu saemu tafi tare dashi, wani shekarar km saesuje tare sannan abinda ta haefa yayi wayo, km ni miye zanyi da wani business bayan komae mijinmu yana yimana bamu rasa ci da sha ba gsky bazan fara d'orawa kaena abinda zae cazamin brain ba kinga ni saboda haka na tsaya iya degree banson tension da qarancin shekaruna.

Ta'be baki kaltum tayi tace harsae kin jira ta wani haehu? Ae idan kece kikeda cikin ita batadashi bazata wani jira saekin haehu ba, tafiyarta zatayi babu ruwanta. Hmm aeni wlh hajiya kaltum, maryam tana bani mamaki wae duk wannan fadan nata amma ta tsaya har akayi mata kishiya aeni wlh lokacin dana shiga gidan abbansu sudaes tuni nayi yanda nayi na fitarda mamansu yanzu ni kadae nake isata da mulkina son raena acikin gidan, amma kin wani tsaya har amiki kishiya kina zaune surnana ya doyar gaesuwa😏 gashinan ae kina zaune zata haehu ta barki, tana fara haehuwa shikenan duk hankalin mijinki zae koma gareta, daga nan km wukaqanci da gori su biyo baya, idan kinci sa'a ma dangin mijin basu juyamiki bayaba. Ahhtohh fad'amata dae hajiya sa'a tayita zama karta san inda dare yy mata.

Ajiyar zuciya maryam ta sauqe tace toh ni ynz miye abinyi haehuwa dae Allah ne bae kawoba, dukda bana damuwa acan baya amma yanzu kam na fara damuwa sbd nagane matsalar rashin haehuwar daga garenine amma zan cgb d adduah da neman magani.
Kaltum ce tace ynz abinda za'ayi kawae a zubarda cikin inyaso ku zauna duk Ku biyun bb haehuwar. A firgice maryam tace subhanallah haba kaltum nidae gsky bazan iya kisan kae ba, sa'a ce tace ae lokaci ya qure cikin bazae zube ba saede su halaka gabadayansu, amma ga wata idean me zae hana idan ta haehu kije asibiti a baki qwayar hana daukar ciki kina sakamata acikin juice ki tabbatar tanasha shikenan kinga wannan yafi sauqi shiru maryam tayi yayinda ta lula duniyar tunani.

NAJMAH by meenerhWhere stories live. Discover now