page 35&36

8 1 1
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
        NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺


STORY & WRITTEN
            By
        Meenerh

Bismillahir rahmanirrahim

Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa 🙏

Dis page goes to uh💙 Umman Sudaes💙
    &my💙
               💙Son
                    Sudaes💙
Haqiqa ina matuqar💙jin dadin💙yanda kike💙sambadowa💙comments💙
Ina qaunarki irin sosae dinnan💋💙💙

Free book
📄 page 35&36

Kara wayar yayi a kunne, shiru yayi baece komae ba, banji dae me ake cewa cikin wayar ba, kawae sae ganinshi nayi ya tashi daga kwancen dayakeyi with shock naga ya zaro idanu yace "whatttt" sadeeq are u serious kw? Yaushe hkn y faru km bb wnd ya fad'amin?

A d'aya bangaren ne najiyo sadeeq nacewa " wlh fa yaya jiya da safe tayi shirin zw school" byn ta fito dg part dinsu, tazo tsakiyar compound din gidan ta fadi, mu km lokacin munyi mantuwa nida haydar mun dawo kenan kawae muka ganta a kwance"

"Innalillahi shine abinda affan ya fad'i"

Toh ynzn miye akayi mata tana ina?

Eh jiyadae Dr KB yazo ya mata injection, ya rubutu drugs na siyomata, sannan yace kar'a bari ta tashi sae tayi kwana biyu, sbd taji ciwo a qafarta.

Gumi ya sharce, duk d sanyin AC dake cikin d'akin, amma hkn bae hanashi yin gumin ba, domin duk cikin qannensa babu wacce suka shaqu sosae irin zarah,

Hasalima bayi sake musu fuska ko kad'an.

"Yi sauri ka kaewa ammi waya zamuyi mgn" ok sadeeq yace, sannan yayi hanging up na wayar, sannan ya fito dg d'akinshi ya nufi part din ammin.

Tun kafin ya qarasa yake jiyowa wani abu mae kamada ihu.

Cikin hanzarin daya keyine, ya qara da gudu_gudu km sbd sautin kuka d ihun dayake ji.

Yana isowa bedroom din ammin, saeya samu wani dattijo riqeda qafar zarah, wacce ta kumbura tayi sundum kmr me,

Wani irin  gigiceccen ihun azaba zarahn ta sake saki, a daede lokacinda wani abu yayi qara yace qassss!!!

Wayyo ni zara'u!!!!!
Shikenan ya sake karyamin jikata wayyoo Allah na!!!
Inna ce ta qare wannan ihun tareda sakin kuka kmr wata qaramar yarinya.

Alhamdulillah shine abinda wannan dattijon ya fad'i,

Wata irin zufface ta karyowa zarah, tayi sharkaff da ita, kmr wacce aka kwarawa ruwa a fuska.

Idanun sadeeq ne suka ciko da qwalla, cikeda tausayin 'yar qanwar tasa ya qarasa izuwa gadon datake kwancen.

Zaunawa yayi yace sannu angel, Allah ya baki lfy,

Ae lfy kam ta samu da yardar Allah cewar wannan dattijon.

Goge majina da hawaye inna tayi, cikin muryarta wacce ke nuna alamun kuka tace bawan Allah don Allah ka fad'amin gsky karyewa tayi kohh??

Aa baba ba karaya bace, targad'e ta samu km, alhamdulillah an samu qashin ya koma saede kada ku kuskura ku bari ta taka qafar harsae na dawo nanda kwana biyu, zan duba nagani, idan ya kamata ta fara takawar.

Toh ynz bawan Allah nawane kudin aekinnaka? Dattijon ne yace aa baba saena dawo tukunna idan ta samu sauqi, inshaallahu zata samu cewar inna, baba tsohone ya tattara kayanshi yace tohh baba zan wuce saena dawo km, toh mungode sosae d'annan.

NAJMAH by meenerhWhere stories live. Discover now