🌺🌺🌺🌺🌺🌺
NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺STORY & WRITTEN
By
MeenerhBismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏
Free book
📄 page 23&24Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kae duniya shin ina zaki damu ne hk, ynz wannan irin alhakin mahaefiyar yarinyar data dauka ae ya ishetama guziri, wae me mutane suka dauki duniya ne? Shin sun manta da ubangijin da bayayin bacci ne, lallae wannan mata ta cika marar imani, sannan km azzaluma ynz da ace yarinyar ta mutu dagaske fa yaya zatayi? Ae wlh mama ynz ma baza'a kyaleta ba, dole a hadata da hukuma su koya mata hnkl, sbd zuwa nan gaba ba'asan me kuma zatayi musu ba.Gsky kam sam bazae yiwu ba cewar abban khaleed, nusaeba kWA
gidan tausayi harta fara kuka tana cewa abba don Allah kayi adopting na yarinyar idan ta warke wlh sunyi mugun bani tausayi, karki damu nusaeba inshaallah xan dauketa ta dawo gidannan da zama domin inason na inganta mata rayuwa, amma sae iyayenta sun yarda zanyi hkn, ynz dae ke maman khaleed ku kwana da shiri inshaallah gobe da safe kafin na tafi gurin aeki zamuje asibitin domin mu dubosu muga a wanne irin hali suke.
Kae km khaleed haqiqa na yaba maka da yanda ka taemaki wannan bayin Allah hk, gsky naji dadi sosae dakayi wannan aekin alkhayrin, ina alfahari dakae a matsayinka na d'ana na cikina, Allah yy maka albarka.WANENE KHALEED?
Alhaji Ibrahim mae shadda shine asalin sunan mahaefinsa, asalin iyayensa 'yan garin misau ne dake jihar Bauchi, amma ynz suna zaune a cikin kano.
Su uku iyayensu suka haefa km shine babba acikinsu, biyu maza, Ibrahim da Abdullahi sae autarsu mace mae suna Safiyya tana aure a Jos, tanada yara 4, sae Abdullahi shi km yanada mata biyu da yaranshi guda 9, shima yn zaune a kano shi km aekin koyarwa yakeyi a hotoro secondry school.
Sae Abdullahi mahaefinsu khaleed. Sunanda ake mishi inkiya wato (mae shadda) ya farone dg lkcn daya fara kasuwanci a kantin kwari inda yake saeda yadina dg bisani Allah ya bunqasa masa kasuwancinsa ya koma saeda shaddodi, yadina, atamfofi, lesuna da dae sauransu.
Yanada matarshi daya mae suna Murjanatu, Allah ya azurtashi da samun yara guda 8, Khaleed shine babba,sae sadiya wacce ta rasu washe garin sunanta, toh tun daganan saeda ta haefi yara har guda 5, amma Allah baya bar matasu, sae a haehuwarta ta takwas ne Allah ya bar mata yarinyarta mae suna Nusaeba, dg nan km bata sake haehuwa ba.Khaleed matashine mae jini a jika, farine amma ba sosae ba, yanada tsawonshi daedae misali, ga hancinsa har baka, sae idanunsa daedae misali, yanada shekaru 28 a duniya. Byn ya kammala degree dinshi a fannin Engineering ne sae mahaefinshi ya bude mishi qaton shago a kasuwar kantin kwari shima, inda yake saeda zallar lesuna da materials aciki.
Tun lokacinda aka haefi nusaeba, sae iyayenta suka dauki son duniya suka doramata, hk shima yayanta yana matuqar qaunarta sosae, duk abinda takeso shi suke mata, amma fa duk da wannan bae hanasu bata tarbiya mae kyau ba, ynz hk tanada shekaru 18 a duniya, km tana ajinta na qarshe a secondry wato (SSS 3).
Wannan kenan, a takaece dae ynz munsan waye khaleed.
Washe gari da misalin qarfe 10:00 na safe, mahaefiyar su khaleed sun gama kimtsawa itada yaranta da km maegidanta, inda suka dunguma izuwa asibitin dasu najmah suke.
Acikin asibitin kw a halinda ake ciki ynz likitoci sun tabbatarwa da maman najmah cewar d'iyarta tana raye bata mutu, sbd sunga har ynz kmr bata cikin hayyacinta.
Sannan sun tabbatar mata da cewa inshaalla zw gobe ma za'a iya sallamarsu, saede a bisa bincikenda sukayi sun tabbatar da cewar najmah tana dauke da cutar Asthma, wacce a dalilin dukan da inna laure tamata ne ya sanya numfashinta daukewa gabadaya, sbd tafi dukanta a gadon bayanta, sannan rashin samum cin abinci ya janyo ulcer tayi mata mugun kamu, wanda itama ta taka muhimmiyar rawa wajen galabaeta ta.Suna kwance a dakin hutu duk su biyun wanda basufi 3hours da farkawa ba, sae yaya mariya wanda itama bata dade da isowa ba, ta kawo musu koko da kosae sae ruwan lipton, innar deejeh dataga yaya mariyan ta zone saeta tafi gida domin taje tayi musu abinci, tayi wanka sannan ta dauko musu kayanda zasu saka.
Sallama nurse saleema tayi gamida bude kofar dakinda suke kwance, a bayanta km su khaleed ne tareda iyayensa suma suka shigo.
Qarasawa kusada gadon da maman najmah take kwance sukayi, maman khaleed ne tace sannu baewar Allah ya jikin naku? Da sauqi cewar maman najmah, suma su khaleed da nusaeba ya jikin sukayi mata, sannan suka nufi gadon najmah nusaeba ne tace sannu sister ya jiki? Najmah ne tace da sauqi da muryanta da bata fita sosae, qanwata ya jikin? Alhmdllh, Allah ya baku lfy tace amiin mungode kmr kaene wanda ya kaeni chemist rannan koh? Eh nine.
Shiru sukayi duk su ukun yayinda khaleed da nusaeba suka zuba mata ido, suna mae jin tausayinta har cikin ransu.
Nusaeba ne ta katse shirun ta hnyr cewa wlh yaya wannan tana kamada jannart din uncle, kae Nusaeba kinada basira fa sosae nima lkcn dana ganta saeda nayi wannan tunanin, ae kuwa muna komawa gd zan kirata na fada mata nace naga mae kamada ita yau km fa wlh kaga har......shuttup ur mouth nusaeba bakiga batada lfy ba amma sae surutu kike mata cewar mamansu, yaya Mariya ce tace hajiya bb komae quruciya ne kawae.Lkcn da maman su khaleed da maman najmah suka hada ido zuciyarsu ne tayi mugun bugawa da qarfin gske.
Maman najmah ne tayi murmushi tace ayyah baewar Allah saede ban wayeki ba, kafin maman khaleed tayi mgn sae yaya Mariya tace nidae na gane wancan saurayin ta nuna khaleed, murmushi yy sannan ya sake maeda kallonshi ga najmah, yaya Mariya ce tace wannan shine wnd muke baki lbr dazu.
Shine ya kawomu wannan asibitin jiya, gashinan yaron kirki sannu bawan Allah, mungode Allah ya sakamaka da alkhayri, itama maman najmah addu'o'i ta jero masa ya amsa acikin zcyrshi sannan ya juya ya fita domin zw office din doctor domin jin qarin bayani.Byn fitarshi ne sae maman khaleed tace ae itane mahaefiyarsa gacan qanwarsa nusaeba, jiya da daddare byn ya dawo yake sanar mana abinda ya faru, sannan ta sake yimata addu'ah akan Allah ya kiyaye gaba y km basu lfy, da ameen ameen maman najmah ta amsa sannan tace baewar Allah mungode da dawaeniya Allah y biyaku da gdn aljannatul firdausi, murmushi maman khaleed tayi tace wlh bb komae ae yiwa kaene.
Khaleed ne zaune a office din Dr KB, byn sun gaesa ne yake tmbyrshi abinda ke damunsu.
Dr KB ne yace a gsky abokina wannan bayin Allah suna cikin gararin rayuwa wnd idan ba'a samu wnd ya tsaya musu ba komae zae iya faruwa dasu, musamman ita mahaefiyar yrnyar domin mgnr gsky zuciyarta tana cikin hatsari idan ba'a dauki matakin gaggawa ba zata iya kamuwa da ciwon zcy wanda bama fatan hkn ya faru.
Sae ita km yrnyar tana dauke da cutar Asthma da km ulcer amma ita inshaallah idan anbi dokokin da zamu kafa mata toh komae zaezo da sauqi. Saede fa yrnyar tayi mugun buguwa sosae don da kyar muka samu ta farfado amm da ace ba'a kawota asibitin da wuri ba da saede arasata. Ajiyar zcy khaleed yayi yace toh doctor ynz dae bb wata matsalan wannan ne kawae? Eh itane ynz bari na rubuta mk drugs din da zasu dinga using dashi, sae kaje pharmacy ka siyo.Isarshi pharmacyn keda wuya sae kawae yaji......✍ ✍
More comments
More post😘Cmmnts naku shine zae qaramin qarfin gwiwa😍 idan kunason typing mae yawa da km cgb kunayin cmmnts sosae
Vote comments & share pls🙏
Jan hnkl gareku marasa yin cmmnts d km labe😏 very soon zan katafila ta zata fara biyowa ta kanku😎😎 soo idan ears sunji toh body ya.....😎
Meenerh ce ✍

YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Historical Fictionlabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...