🌺🌺🌺🌺🌺🌺
NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺STORY & WRITTEN
By
MeenerhBismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏
Free book
📄 page 15&16I dedicated dis page💜 2 uh my childish friend💜 Nancy💜a best friend ever💜 my love 2 uh is unlimited💜 I soo much love uh💜 unconditionally💜💜
A can gidansu najmah kuwa inna laure ce kwance shame-shame a qasa ko tashi ta kasayi saboda tsabar jibgar data sha a wajen ramatu 'yar daba, sakamakon cin bashin kudinta datayi kuma ta batar kudin a banza ba tareda ta biyata ba, duk wannan abubuwan d suka faru babu wanda ya lura da yanayinda take ciki, saboda tashin hnklin da suka shiga a lokacin.
Baban najmah ne ya shigo gidan kmr wanda aka hankad'oshi yana cewa shin da gaskene labarin danake ji lau...maganarsa ce ta maqale bata qarasa fitowa sakamakon ido biyu d sukayi da inna laure wacce take kwance duk an sabauta mata kamanni
Abubuwa biyu ne suka taru sukayi masa ruddugu akansa,
Na farko shine duk lokacinda yayi niyyar tsawatar mata akan abinda take yiwa abokiyar zamanta da yarinyarta, saeyaji ya kasa yimata magana, sae baya tareda ita sannan abun yake damunshi, tofahh🤔 lallae da alama akwae wani 'boyayyen al'amari, but time will tell.
Na biyu kuwa shine ganinta da yayi a kwance ita kadae, sannan daga dukkan alamu babu kowa acikin gidan
Qarasawa yayi kusa da ita yace meke faruwa ne haka laure, ban saniba ae duk kaene babban munafikin😡 kaene ka janyo komae ta faru aeda baka bar mutane cikin talauci na masifa ba da duk hk bata faru ba.
Muna xamanmu cikin rufin asiri kaje ka kyallara ido ka gano waccar dangin mayun tazo ta mana tatass acikin gida, gashi yanzu ae ka janyomin bala'i😥, har cikin gida ramatu 'yar daba, tazo ta kir'beni gashinan ta barni da tsamin jiki😥 kuma nasan wlh ba kyaleni zatayi ba.
Zaro ido malam Ali yayi😳 yace laure so kike a bankawa gidannan wuta duk mu mutu ko, kinsan halin ramatu 'yar daba kuwa🤔 wanne tsautsayi ya saki karbar bashinta, toh wlh nidae babu ruwana yaseen.
Haba malam ae wlh kayi tsararo ae kaene ka janyo mana wannan bala'in, saboda haka ko wacce irin masifa xamu shiga kaema harda kae acik.....sallamar police ce ta sanya su yin shiru, duk sun tsure kowa sae zare ido yakeyi, inna laure kuwa harda d'an guntun fitsarinta🤣🤣 ni kuwa nace inna laure ae bakiga komae Bama🤣🤣
Likitoci guda uku ne suka rufu akan maman najmah domin ceto rayuwarta, suna iyakacin qoqarinsu wajen ganin ta farfad'o, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, sae ganinta sukayi zumbur ta miqe da sauri tana neman guduwa tana cewa wlh ta kasheta, shikenan ta kash....saeta dafe qirjinta da qarfi sakamakon wani irin azababben zafi daya ziyarceta.
Da sauri wata nurse ta riqota ta kafin ta kwantar da ita harta sake suma, tana kwantar da ita sae Dr kabeer yace gsky wannan duk yanda akayi shock ne ya mata yawa, kuma yake neman sabauta mata brain dinta, nima dae kmr abinda nake gani kenan cewar Dr Noor.
Drip Dr kabeer ya saka mata tare d allurar bacci aciki, sannan yace yanzu zamu iya fita mu barta tunda harmun samu ta d'an farfad'o, nanda 8hours zata iya farkawa, saede kuma matsalar shine dole lokacinda zata farka ya zama akwae wacce suka shaqu da ita sosae.
Yanzu idan na fita zanyiwa wanda suka kawota bayani, Bismillah Dr Noor we can go, nurse saleema u should stay with her, rusunawa tayi sannan tace ok sir.Suna fitowa dg emergency ward din, sae suka ga su khaleed tare da su innar deejeh, sae maman rabi'atu da yaya Mariya kowacce a cikinsu idonta yayi jaa sosae wanda hakan zae nuna maka tabbacin cewar sunyi kuka, Dr Kabeer ne yace waye wanda ya kawo wannan matar da yarinyarta? Sae khaleed yace nine doctor, ok ka biyoni office d'ina.
Bayan sun shiga office dinne sae Dr Kabeer yace d'an samari maganar gsky wannan baewar Allah tana cikin mawuyacin hali wanda by my observation naga kmr shock ne yake neman taba mata brain, sannan km zuciyarta ta kumbura, km BP dinta ya hau sosae.
Dr Bukar ne keta faman gwaje-gwaje a wani room, banda na'urori babu abinda ke motsi sae faman cewa dikkdikkk suke, gumi naga yana sharcewa wanda har yanzu ya kasa ganowa musabbabin abinda.....✍ ✍
More comments
More post😘Cmmnts naku shine zae qaramin qarfin gwiwa😍 idan kunason typing mae yawa d km cgb kunayin cmmnts Mae yawa
Vote comments & share pls🙏
Meenerh ce ✍
![](https://img.wattpad.com/cover/288378065-288-k383029.jpg)
YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Historical Fictionlabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...