🌺🌺🌺🌺🌺🌺
NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺STORY & WITTEN
By
MeenerhBismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏
Free book
📄 page 21&22Da misalin qarfe 8:30 na dare a wani room, naji wani irin sauti mae kamada kuka,shigata keda wuya na samu maman najmah tana kuka tana shirin ficewa a guje, da sauri nurse saleema tare da innar deejeh suka kamota sannan suka zaunar da ita a bakin gadon asibitin, saleema ce tace mama ki riqeta da kyau karta fice, so take ta gudu bari naje na kirawo doctor, da sauri ta bude kofar sannan ta saka key ta nufi office din dr KB.
Sae faman kiciniya take da ita, da kyar da taemakon Allah d km addu'ar datake tofa mata ta samu ta zauna ta dan nutsu tana riqe da hannun maman najmah wacce take kuka amma ba mae sauti sosae ba.
Haba maman najmah kuka fa ba shine abinda zakiyi ba, kiyi mata addu'ah Allah ya tashi kafadunta tanacan a dakin hutu ( resting room), likitocin sun dade suna ta faman ganin sun ceto rayuwarta domin sunce mana suna tunanin bata mutu ba, km alhmadulillah an samu ta farfado sbd hk ki kwantar da hankalinki najmah tana raye bata mutu ba, kinga kema ba lfy ne dake ba karki sake sakawa kanki wani ciwon don Allah kinji, batace mata komae ba.
Bude kofar dakin akayi da sallama suka shigo su uku ne Dr KB, Dr noor sae saleema.sannu mama ya mae jikin? Da sauqi likita, toh Allah ya qara sauqi ameen, mama zaki dan fita zamu canja mata daki tana buqatar hutu, za'ayi mata wata allurar ta tsawon awanni 10, sae gobe zata farka, km muna saka ran cewa zata samu sauqi inshaallah, toh doctor Allah yasa, allura yayi mata sannan ya umarci saleema domin taje ta kirawo sauran 'yan uwanta nurse sae suyi mata transfer xw resting room, OK sir sannan ta fita a hnkl take rufe idonta sakamakon allurar bccn da likitan yayi mata tanada qarfi sosae.
Sallama khaleed yayi a wani palour wanda wata dattijuwa wacce bazata wuce 47yrs ba zaune take akan 2seater, yayinda hnklinta yayi nisa akan TV, amsa sallamar tayi ba tareda ta juyo ba, zama yayi akan carpet din daya malale tsakiyar palourn yace washh Allah! mama brk da dare, yauwa khaleed brk ina ka shiga ne yau hk tun safe daka cemin ka tafi kasuwa baka dawo ba?
Sae dazu da abbanku ya shigo yake cemin yaga shigowarka da azahar ka dawo da machine ka dauki mota da sauri ka fita, ina fata dae lfy?Wlh mama ba lfy ba, subhanallah meya faru? Mama ynz dae akawomin abinci naci tukunna yunwa nakeji yau tun breakfast banci komae ba, wae babanah bazaka daena zama da yunwa ba, kasan dae kanada ulcer amma kake zama da yunwa koh, toh mama ya zanyine busy ne yamin yawa shiyasa, hmm ae shikenan dama ae kaekam run kana qarami bakacin abinci sosae sae kaje kayi tayi idan kayi aure matarka ta huta girki, murmushi kawae yayi yace mama nidae abinci a taemakamin pls, toh naji saekace wanda zakaci da yawa.
Nusaeba! Nusaeba!! Na'am mama, wata budurwa nagani ta shigo palourn wacce bazata wuce 18yrs ba, batada jiki sosae tana sanye da wata pink din doguwar riga na atamfa mae ratsin blue ajiki, sannu da dawowa yaya, yauwa sannu yi sauri ki kawomin abinci pls, toh yaya ta fada da ladabi sannan ta juya ta fita dg palour ta nufi inda kitchen din gidan yake, bayan 4minutes ta dawo palourn dauke da warmers guda biyu, juyawa tayi ta dauko plate da spoon ta ajiye, sannan ta nufi fridge ta dauko wani jug wanda yake dauke da sobo aciki sae pure water guda biyu masu sanyi ta zuba a plate duk ta ajiye a gabansa, bude warmers din tayi tayi serving na shinkafa 'yar dadae da miya wacce taji naman kaji aciki sae cabbage data zuba a gefen plate din sannan ta saka spoon aciki ta tura masa abincin gabansa, sae tace yaya ga sobo nan na maka kae daya mae dadin gaske kae kadae nayiwa ko mama ban bawa ba, murmushi yayi yace madallah da 'yar qanwata ni kadae, itama murmushin tayi.
Bismillah yayi sannan ya fara cin abincin yaci kusan rabi don wanda ya rage acikin plate din baeda yawa, ruwan sanyin ya dauka guda daya ya shanye tass sannan ya tsiyayi sobon a qaramin cup shikam saeda ya shanye cup biyu sannan yayi gyatsa yace alhmdllh.kae qanwata dole na miki kyauta fa irin wannan sobo hk😊 gsky yy dadi sosae sbd hk bani account numberki namiki transfer, da sauri ta bashi accnt number, tana bashi taji qarar message a wayarta dubawarda zatayi kawae taga alert na 5k, wani irin tsallen murna tayi tace yess sae yayana ni kadae Allah dae ya biya, dama kayan kwalliya na sun qare gobe sae naje na siyo wasu.
Aekuwa nine ma zan kaeki super market da kaena sae in dada miki wani kudin ki zabi abinda kikeso cewar wani dattijo dake shigowa cikin palourn, nusaeba ce tace wayyo Allah na dadi kasheni😊 toh ke km mama me zaki bani ta fada tana turo baki irin na sakalae km 'yan auta, bb abinda zan baki mutum sae shegen son kwalliya kmr dawisu, sake zumburo baki tayi sannan tace abba kajiko dama mama bata sona, dry sukayi sae abban nata yace rabu da ita har phone zan canja miki kowacce iri kikeso idan kinyi candy, wani irin ihun murna tayi sannan tace Allah y kaemu lkcn abba, sannan tayiwa maman nata gwalo😜 murmushi tayi tace ya siyamiki companyn waya ma kina yawo dashi ajikinki qarewa.nan ma dariya sukayi sannan abban yace gsky bakiji haushi ba.
Yauwa babanah baka fadamin abinda ya farun ba, eh wlh mama ynz nake shirin fadamiki, ok inajinka, wlh mama dazu ne da safe nida abokina munje gurin mae shayi kawae sae wata yarinya muka gani ta fadi a kusada mu ashe ma suma tayi, muka samu dae ta farado sannan na kaeta chemist din abdul domin ya bata magani saeyace ae ulcer ne yamata chronic ajiki, sae muke tmbynta meyasa ta bari har ulcer tayi mata hk bata fadawa kowa ba, ina iyayenta suke sae tace basuda shi kllm hk suke kwana, nandae na siyomata indomie tasha magani sannan nace ta jirani nazo gida nayi wnk sannan muka tafi gdnsu.
Toh ashe kishiyar mamanta ce take gana musu azaba kala-kala
lkcinda ta fadin ma ashe aekota tayi diban rw wae zatayi kokon siyarwa km batada lfy, shine byn na ajiyeta a gdn nasu na wuce kasuwa.Lokacin dana dawone sae nake ganin mutane sunata gudu suna shiga gdn anata kururuwa, saeda wata yarinya tazo shiga gdn ne nake tmbyrta abinda ke faruwa sae tacemin wae inna lami ko waye ohoo dae na manta sunanta ta kashe najmah, muna cikin hk saega mahaefiyar yarinyar ta fito a gdn aguje kmr wacce ta zare tana cewa ta kasheta kafin ta qarasa ta fadi a qasa shine fa nayi sauri nazo na dauki mota na kaesu asibiti har yrnyar,saede likitoci sunce yrnyar bata mutu ba, amma har ynz mahaefiyartata bata dawo hayyacinta ba, saede byn dawowata ta farfado wlh mama sun bani tausayi suna cikin mawuyacin hali, ya qarashe mgnr da damuwa a fuskarsa.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wae shin duniya ina zaki damu ne hk yanzu ace wannan.....✍ ✍
More comments
More post😘Cmmnts naku shine zae qaramin qarfin gwiwa😍idan kunason typing mae yawa d km cgb, toh ku cgb d sambadowa cmmnts
Vote comments & share pls🙏
Meenerh ce ✍

YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Ficção Históricalabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...