🌺🌺🌺🌺🌺🌺
NAJMAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺STORY & WRITTEN
By
MeenerhBismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine novel dina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa 🙏
Free book
📄page 31&32Tana cikin tafiyarta kawae taji an bangajeta tana juyowa taga salamatu tana harararta sannan tace aekin banza mutum banda yawon iskanci babu abinda ya iya, ae dama inna ta fadamin wannan mae motar dayake zuwa gurinki dakeda uwartaki yawon iskanci kuke zuwa dashi aekin banza agola kawae ta qarashe tana mae dungure mata kae. Tashi tayi tana goge guntun hawayen dake malala daga idonta sannan tayi corner da zata sadata da gidansu deejeh.
Sallama tayi acikin gidansu deejeh lokacinda take wanke-wanken kwanukan da bata samu damar wankesu ba saboda yanzu suna rubuta jarrabawar fita daga aji daya na qaramar secondry. Dagowa deejeh tayi sannan tace wae nikam yau waye nake gani hk cikin gidannan? Qarasowa najmah tayi ta zauna akan kujera sannan tace ina inna take? Ta'be baki deejeh tayi tace wae taje kasuwa bata dade da fita bama. Shiru najmah tayi bata sake cewa komae ba, deejeh dae tana ankare da ita can dae najmah tace deejeh miye agola yake nufi? Ke kuma miyesa kike wannan tambayar? Kawae inason sanine kusan kullum sae salamatu ta fadamin shiyasa nakeson sani. Kam bala'i deejeh ta fad'a lokacinda take cire hannunta acikin ruwan kumfar wanke-wanken datakeyi, kinsan me agola yake nufi kuwa? Toh wanda mamanshi taje dashi gidan wasu dashi, kmr dae wanda ba'a haefeshi ba acikin gidan wasu, Toh deejeh aeni babane ya haefeni, nima dae abinda nagani kenan, lallae najmah kina bani mamaki yanzu 'yar wannan yarinyar kika bari takemiki rashin kunya amma baki kamata kin jibgi banza ba? Sae kace wanda kike tsoronta? Tabb ae wlh danice bata isa tamin wannan raenin wayon ba. Nifa shiyasa yanzu bana zuwa gidanku sosae sbd wlh bazan dauki raenin wayo ba tsabb zan goga bakin yarinya babu abinda ya shalleni.Najmah ce tace wae ke deejeh har yanzu da kike junior dinma baki daena wannan masifar ba? Tabbdi cewar deejeh ae yarinya yanzu duk prefects din makarantarmu tsorona sukeyi tunda wata lukuta tamin bulala biyar wae sbd na makara, aekuwa ana tashi dama nayi target dinta na kamata na jibgi banza shikenan ynz duk daliban makarantar suke tsorona sae lallabani sukeyi. Dariya najmah tayi tace kae qawata Allah y shiryeki.
Deejeh ce tace wae sae yaushe zaki cigaba da karatune? Kiga fa yanzu jss2 zamu shiga amma har yanzu shiru, ajiyar zuciya najmah tayi tace wlh inason cigaba da karatu amma kinsan babu halin zuwa makarantar kwana shiyasa.
Kinsan yaya za'ayi? cewar deejeh, aa! Ki bari idan baffa ya dawo zan tambayeshi ko zae sakaki a makarantarmu ba sae lallae kinje na kwanan ba, tunda kinga nima Allah ya taemakeni baffa ya barni zan cgb d karatun, bari na tashi na tafi cewar najmah "umma tacemin karnayi dare" toh bari na qarashe wanke_wanken saena rakaki, toh bari na tayaki saemufi sauri.
"Assalamu Alaikum ammina"
Shine abinda ya fito acikin wayar dake kare a kunnen ammi, wacce take zaune akan oneseater dake cikin palournta.
Wa'alayka Salam son ya karatun? Alhamdulillah, wanda aka kira da son dinne yace "Nayi missing naki fa ammina sosae" ji nakeyi kmr nayi tsuntsu na dawo Nigeria, hmm son kenan ae nima fa nayi kewarka sosae, gsky ayi_ayi a gama exam dinnan basae kun kar'bi result ba, wannan semestern mu samu ad'an leqomu! Murmushin shi mae sauti yayi yace ae gsky kam nima nayi missing na girkin ammina mae dad'i, itama ammin dariyar tayi sannan tace toh dae yanzu saura kwanaki nawa ka dawo? Uhm i think nxtmonth inshallah, ok Allah ya kaemu, da Ameen ya amsa, sannan yace ina Angel take? Ta'be baki tayi tace tayi bacci ae tun dazu, lahh ammi da wuri haka? Eh ae kasan yanzu suna exams ne shiyasa, ok yanzu a wanne term suke? Third term ne, kice Angel an girma har itane zata shiga jss2 gskyne toh gobe idan Allah ya kaemu ace ta kirani, tohh shikenan. Bye-bye ammi, bye son.Safnah ce ta fito daga d'akinta cikin shirinta na wani less coffee da d'igon milk ajiki, wow gsky tayi kyau babu qarya kunsan yanda coffee yakewa farin mutum kyau, ta dan yafa gyalenta milk a gefen kafada, kafarta kuwa sanye take da wani arnen takalmi mae tsini shima milk da handbag d'inshi, tana tafiyarta qwasqwas tana taunar cewing gum abinta.
zarah ce sae faman sauri takeyi saboda yau tayi late a school, Allah ma ya taemaketa saboda sae 08:00am su shiga exam din, yanzu km kusan qarfe 07:40am. Tazo cikin compound din gidan kenan, kawae batayi auni ba saeji tayi sunyi karo da mutum, babu shiri taji an hankad'eta tayi baya tayi wata irin mummunar fad'uwa.
Qarar data qwalla tayi daedae da ficewar wata mota qirar marcedes baqa acikin gidan.
Dr KB ne tsaye a bakin wani gado wanda yake zagaye da mutane har hud'u, dady, ammi, sadeeq sae Yusuf duk sun zuba uban tagumi.
Rubutu yagama ajikin wata farar takarda, sannan ya miqawa sadeeq ita yace yaje ya nemo wannan magungunan a chemist, karba yayi sannan ya dauki mukullin motarshi ya fice a d'akin.
Dr KB ne yace dady ni zan wuce hospital inada surgery by 12:00noon, na rubuta prescription na yanda zatasha drugs din, na mata allura zatayi bacci sosae, saede gsky kar a barta tayi karambanin tashi harsae tayi kwana biyu sbd qafarta tayi mugun buguwa, Allah ne ya kiyaye ma da bata karye ba.
Allah ya bata lfy, da Ameen suka amsa, sannan ya nufi qofa ya fice.Dady ne yace Allah sarki mamana Allah ya bata lfy. Waeni tukunnana a ina taji wannan ciwon ko a makarantar ne? Ammi ce ta sauqe ajiyar zuciya tace nima bansan mataba, kawae ihunta naji dazun ina fita na ganta a kwance, lokacin su Yusuf sun shigo gidan shine fa suka d'aukota sannan suka kira Kabeer yazo ya dubata. Nidae bansan meya sametaba saede idan ta tashi aji dg gareta.
Yusuf ne yace ammi naga ae kmr exams ma sukeyi ko? Wlh Yusuf exm sukeyi, wae km ynz ya za'ayi kenan ko wata za'a samu tana zana mata kafin ta warke? Aa zance na samu Principal d'insu cewar dady.
WASHE GARI.
Mamana! Mamana!! Kina inane hk? Na'am umma gani na zaga bayine, tohh dama unguwa zamuje d'auko hijab dinki, tohh umma.
Tafe suke itada yarinyar tata sunzo daff da fitane umman najmah ta tsunkayo muryar inna laure tana "cewa yauwa bismillah garin Allah km ya waye yanzu za'a fara yawon tazubar din kenan" ita dae umman najmah murmushi tayi batayi niyyar kulataba saeda taji inna laure ta qara volume din muryarta tana cewa ahaka dae za'a qare ana yawon karuwanci god'ae-god'ae ko kunya ba'aji? Kodan dama mutuminda ya fito a barikin mahauk........sauran kalmomin sun maqalewa inna laure a maqogoronta ne lokacinda taji an.........✍ ✍
More comments
More post😘Comments naku shine zae qaramin qarfin gwiwa😍idan kunason long typing ku dinga sambadowa comments
#Vote
#Comments
#Share fisabilillah👏🏻Meenerh ce ✍.

YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Historical Fictionlabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...