🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*NAJMAH*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺*STORY & WRITTEN*
*By*
*Meenerh*Bismillahir rahmanirrahim
Jan hnkl wannan shine Novel ɗina na farko idan kunga kuskure ko typing error kuyimin afuwa🙏🏼
*PERFECT WRITERS* *ASSOCIATION* 🌞
( '''WE AREN'T PERFECT BUT, WE'RE ALWAYS''' '''TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR''' '''READERS''' 💪)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A* ✍️
*COMMENTS YAYI LOW DA YAWA🤧😤**
*عن أبي هريرة رضي الله* *عنه، قال* : *قال رسول الله صلّى الله عليه وسلم: من حسن إسلام المرء تركه* *م* *لا يعنيه، حديث حسن، رواه الترمذي،* *و غيره* *هكذا* .
*An karɓo daga Abu Huraira, Allah ya ƙara yarda dashi yace: Manzon Allah* *Sallallahu alaihi Wasallam, tsira da amincin Allah su ƙara* *tabbata a gare shi yace: "Yana daga cikin kyawun musluncin mutum* , *ya bar abinda babu ruwan sa" Hadisin ingantacce ne, Tirmidhi ya rawaeto* *shi, tare da waninsa.**FREE BOOK*
📄 *page 49&50**12:00pm*
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT*A hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin, lokaci guda kuma ya lumshe idanun shi, sakamakon wata daddaɗar iska da ta ziyarci ƙofofin hancinsa.
Iskar da ya ɗebe tsawon shekaru har biyu, ba tare da ya shaƙi makamanciyar ta ba, ita kanta ƙasar yayi kewar ta sosai.
Kewar da bazae taɓa misalta ta ba, har kullum ƙasar tana cikin ran shi.
"Nigeria kenan" My Country, my Pride 😍, Ya Allah ka ƙaramana zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da son junan mu Ameen.
Fari tass!! , Dogo, kyakkyawan matashi mae jini a jika, sanye yake da wani Blue black ɗin suit, wanda yayi matuƙar yi misa kyau, ya kuma fito da aenihin kalar fatar sa, yayin da ya ɗora jacket akan suit ɗin, gefe ɗaya km hannun shi yana riƙe da travelling Bag ɗin shi.
"Dr. Muhammad Abubakar Muhammad Tafeeda kenan" (Sultan), "Afwan Fans"🙏🏼 I have decided to change the name from Affan to Sultan, hence "Affan" was d Nickname for "Usman" Don Allah badan ni ba kuyimin Uzuri hilis🙏🏼.
Sannu a hankali yake taka step_step ɗin, cikin tafiyar shi ta nutsuwa, ya sauƙo daga cikin jirgin, yayinda ƙafafun shi, suka dira a ƙasa.
Hamdalah yayi a cikin zuciyar sa, yana mae sake godiya ga Allah Subhanahu wata'ala, da ya ƙaddara dawowar shi, km ya kawo shi lafiya.
Wani irin farin ciki ne, ya sake ziyartar zuciyar shi, lokacin da idanunsa suke kallon tarin al'umma dake gilmawa acikin Station ɗin.
Da ido yake bin kowanne Bil'adam, yana ta tunanin ta inane zae hango ɗan uwan sa.
Shi kuwa Sadeeƙ wani irin murmushi yayi lokacin da idanunsa suka hango masa yayan nasa, ta cikin glass ɗin motar.
Da sauri ya ɓalle murfin motar ya fita.
Ohhh ni "Muhammad" Sadeeƙ shuka ni yayi kenan? Sultan ɗin yayi wannan maganar, lokacin da yake ta faman baza eyes ta ina zaega Sadeeƙ ɗin.
Babu zato babu tsammani kawae yaji an rungume shi ta baya, har saeda suka kusan faɗuwa dukkan su.
YOU ARE READING
NAJMAH by meenerh
Historical Fictionlabarin wata baewar Allah wacce ta taso cikin qunci, wahala ta funsakanci kalubalen rayuwa kala-kala amma dg qarshe sae Allah y hadata d wata baewar Allah mae kyakykyawar xuciya amma acikin gidan akwae wata mata wacce t tsaneta batason ganinta kwata...