1

345 14 4
                                    

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.

TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA SHUGABA JA GABA, SHUGABAN HALITTU BAKI ƊAYA.

ALLAH KA BAMU IKON RUBUTA ABINDA ZAI AMFANI AL'UMMA AMEEN.

★ ★ ★ ★ ★

Ƙarar dirar ɗigon ruwan sama da yake zuba kamar da bakin ƙwarya, bazai hana ƙarar injinan motoci da suke tsaitsaye a titi zuwa cikin kunnen mutum ba... Tsananin ƙarfin ruwan da iskar da ake shi ne ya tilastawa dukkanin masu ababen hawan su tsaya don gujewa samun matsala...

Abin da yafi komai ɗaukar hankali kuwa shi ne ƙarar jiniyar motar asibiti da take tayi babu ƙaƙƙautawa, yayin da hasken shuɗi da ja yake ta walwali a fitilar da ke saman motar...

Motar tana ta ƙoƙarin kunnowa ta cikin cincirindon abin hawa, hakan ya sabbabawa masu ababen hawa motsawa zuwa ga gefen titi don dai wannan motar asibiti ta samu ta wuce don riskar asibiti...

Bayan wannan motar asibitin wata matashiyar budurwar ce take gudu biye da ita tana zubar da hawaye kanta ko danƙwali ko mayafi babu, kana kallonta ba sai an gaya maka ba, kasan tabbas tana cikin tashin hankali...

Jefi-jefi mutane sukan tambayi wannan kyakkyawar matashiya ko lafiya... Amma ga dukkan alamu tashin hankalin da take ciki baya barinta ma ta gane abin da suke tambayarta...

Koda wannan motar tazo asibiti aka shiga da ita, sai ga wannan matashiyar budurwar ta bayyana a kusa da motar tana ta haki gami da sheshshekar kuka...

Yayin da ma'aikatan da suka fito daga motar ko kallo bata ishesu ba, domin tun a hanya suka ankara da cewa tana biye dasu... Buɗe ƙofar motar keda wuya tare da yunƙurin fito da mara lafiyar da yake cikin motar yayi dai dai da lokacin da wannan matashiyar ta fadi kasa sumammiya...

Ko wacece mai tsala wannan gudu haka?
Ko wane mara lafiya ne a cikin motar?
Ko daga ina motar take?

Ku kasance tare da mu don samun amsoshin wannan labari mai ƙayatarwa.

Karku sake a baku labari...

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now