19

45 4 0
                                    

Duk da garin akwai zafi hakan bai hana Ansar ƙurewa a cikin ɗaki ba yana kwance yana ta saƙe-saƙe abin da ya kamace shi, musamman dangane da batun Hafsa, tabbas abubuwan sun dame shi matuƙa ji yake kamar ya tashi cikin tsohon daren nan yaje ya rufe abokanta da duka. Sai dai kuma ina zai same su?

Haka ya cigaba da juye juye yana saƙawa da kwancewa har gari ya waye.

A tunaninsa wayewar gari zata zamo tamkar yayewar damuwar da ta  dabaibaye zuciyarsa amma sai labarin yasha bambam. Domin kuwa da wani sabon fushi ya tashi hatta mamansa da ƙanwarsa khadija sai da suka fahimci hakan. Duk da dai da suka tambayeshi ya nuna musu babu komai. Amma a cikin zuciyarsa shi kaɗai yasan irin abin da yake ji.

"Tunda ka damu bari na gaya maka." Ansar ya faɗawa wani abokinsa bayan dogayen tambayoyi da yake ta yi masa akan wannan yanayi da yaga ya shiga duk da cewa kafin wannan ranar ya ganshi yana ta fara'a abin san barka. "Hafsa ta kasa gane abin da nake so ta gane."
"Me kenan?" Abokinsa Anwar ya tambayeshi.
"Tana mace amma ta zagaye kanta da abokai maza, kuma ta shiga irin ƙungiyoyin nan na nemawa mata ƴanci duka ta bi ta sauya ba irin Hafsa wadda na sani ba."
"Ba yar jami'a bace ba?" Anwar ya tambaya.
"Eh..." Ansar ya bashi amsa.
"To ai babu dalilin damuwa," Anwar ya faɗa yana mai kallon Ansar ido da iso. "Idan dai har ba gani kayi ta wuce gona da iri ba kamata yayi ka kauda kai, irin wannan abotar dole ayita a makaranta saboda akwai group assignments, practicals, presentations da sauransu. Kuma kaga duka ba banbancewa ake ace wannan maza wannan mata ba..."
"Anwar baka gane ba, itafa har musabaha take da maza, sannan idan kana neman..." Ansar ya ɗan tsagaita yana tunanin yanda zai jera kalmomin. "Idan kana nemanta wasu lokutan to wajen abokanan zamanta zakaje kuma kowa yayi musu shaidar mutanen banza ne."
"Eh to in haka ne bata kyauta ba, amma kuma kayi mata uzuri domin kai kafi kowa sanin a ƙasar da ta taso, ni abin da nake tunani shine zama da wayancan yana tuna mata rayuwarta ta ƙasar waje ne shiyasa kuma tunda tafi jin daɗin can sai zama da wayancan masu abubuwa irin na yan can yafi burgeta. Idan nine kai nima shiga cikin wayancan ɗin zanyi sai in ƙoƙarin tsarkake tafiyar tasu..."
"Anwar, baka da hankali wani lokacin kana nufin in shiga cikin yan iska nima in zauna kewaye da mata? Kana nufin nima in rinƙa shan kayan maye kamar yadda suke sha?"
"Ita data shiga cikinsu tayi wayannan ayyukan duka?"
"Ba tai ba, kuma bana zaton zatayi." Ansar ya bada amsa.
"To kaga kaima ashe zaka iya shiga ba tare da ka koya ba."
Ansar bai ce da Anwar komai ba sai kawai yayi tsaki ya tashi ya bashi waje. Anwar ya bishi da kallo yana cike da mamaki.


Hafsa kuwa a wannan dare sai ga message din mukhtar...

Mukhtar: Hello darling!
Hafsa: Besty barka da zuwa 😉
Mukhtar: Ina yayan naki?
Hafsa: Yana can gida yana ɗayan biyu, kodai bacci ko karatu.
Mukhtar: Ba zai zo nan ya hana ki chat ba.
Hafsa: Don Allah ku bar mutumin nan ya huta, kun takura masa da yawa fa.
Mukhtar: Shima ya takura miki da yawa.
Hafsa: Ba komai, nagode Allah da ya bani masoyin da yake kulawa da ni haka. Ni bana ganin laifinsa kawai dai ina son in saita tunaninsa ne ta yanda zai saki wannan tsatstsauran ra'ayin da yake da shi ga addini.
Mukhtar: Kwa ƙarata ke da shi ɗin.
Hafsa: alright.
Mukhtar: Kin ganni yanzu haka a club, muna tare da su Precious, Sumy, kamal da Bash. Gurin yayi kyau sosai, gobe zan nuna miki hotunan.
Hafsa: OMG, I really miss it, you remind me the sweetest Europe life... A wancan lokacin ba a bari na inje club, so I would called on a visit for one of my friend especially Evelyn, sai mu wuce club, kasan club ɗin can... Oh wow abin ba a cewa komai.
Mukhtar: Da zaki je na nan kinga tabbas zai rinƙa tuno miki da rayuwarki da tsoffin abokanki.
Hafsa: Bari zan tambaya a gida, when next zaku je?
Mukhtar: I will let you no Insha Allah.
Hafsa: Kai kullum sai na gaya maka know dabam no dabam fa.
Mukhtar: Indai kin gane ai shike nan.
Hafsa: Hmm
Mukhtar: A cikin daren nan me kika tanadar mana?
Hafsa: Kai da kake club ai sai dai a tambayeka meka tanadar mana.
Mukhtar: I love you dear, hope you felt my warm kisses...
Hafsa: Good night.

Hafsa ta kifa wayarta akan ƙirjinta ta rufe ido, how she wish ace Ansar ne yake bata lokaci haka... Amma shi kullum maganarsa bata wuce Allah da Annabi da kuma future plan, idan akai masa maganar soyayya sai yace sai bayan aure. Though wasu lokutan yana surprising ɗin ta da kalaman soyayya amma ita tana son soyayyar ta zama constantly ne. A nata hangen mutumin da ya kasa baka soyayya kafin ayi aure ya samu tabbacin mallakinka ta yaya zai iya baka soyayya bayan aure ya samu tabbaci akan mallakinka.

Haka ta nausa tana ta tunani, kamar daga sama taji wayarta tayi ƙara, ta ɗauko ta duba, sai taga Mukhtar ne ya turo mata zazzafan message na good night, bata san lokacin da ta ɗago wayar ta sumbace ta ba. Sannan ta sake kifata a ƙirjinta. Idanuwanta suka ciko da ƙwalla lokacin da take tunanin rayuwarta a England ta tuno irin shaftar da suke sha ita da ƙawayenta a kan hanyarsu ta zuwa makaranta, wajen motsa jiki ko kuma club.

Ta sake juyawa ta tuno irin tunanin rayuwar da take tunanin zata samu a Nigeria saboda yanda iyayenta sukaita ƙawata mata Nigeria.

Ta sake kifa kanta akan fulo tana mai tuno irin rayuwar da tayi tunanin zatai idan sun haɗu da Ansar.

"Nigeria, Ansar and Peace are all fiction."

Haka tayi ta tunani kala kala har bacci ya ɗauke ta.

Zamu dakata anan
Sai kuma a rubutu na gaba.

Zamu dakata anan Sai kuma a rubutu na gaba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now