9

51 5 0
                                    

Kwanci tashi haka shaƙuwa tsakanin Ansar da Hafsa tayi ta ƙaruwa, duk da cewar tsakanin su akwai banbancin ɗabi'a amma a hakan sukan yi ƙoƙarin ganin sun daidaita tsakaninsu, musamman ma ita Hafsa, tunda ta fuskanci cewa Ansar yana da tsauri a al'amura da suka shafi addini sai take ƙoƙari wajen ganin tana iyakar yinta wajen ganin bata saɓa masa ba. A ɓangaren sa shima abubuwa da dama yana ƙoƙarin kawar da kai akan wasu abubuwan.

A ƙarshe register da sukai ta fara zuwa makarantar share fagen shiga jami'a sai asararta akai domin kuwa Sadiya tuburewa tayi tace ance akwai wahala kuma kullum tun safe sai magriba don haka ba zata iya ba, shi kuma Ansar yace shi ya yarda zai je, don haka ya halarci makarantar duk da cewa baya son abin da yake a can, domin kuwa Ijmb science yake shi kuwa yafi son ɓangaren literature ko Islamic studies.

Amma mahaifin sa da mahaifin Sadiya Alhaji Sambo sai suka fi ƙarfinsa. Inda a ƙarshe kafin ya kammala suka samu gurbin karatu ta hanyar jamb a jami'ar Bayero da ke Kano. Wani abin burgewa shi ne cikin zama guda suka samu nasara sai dai dukkaninsu basu samu abin da suke nema ba, inda ita maimakon medicine ta samu Biochemistry shi kuma sai ya samu Microbiology.

Duk wani abu daya danganci harkar kuɗi game da karatunsu Alhaji sambo ne ya ɗauki nauyi, tare da cewa har yanzu alaƙarsu da Alhaji Nasiru bata koma kamar yadda take a baya ba. Sabo da shi Alhaji Nasiru har yanzu yana ganin kuɗin da Alhaji Sambo yake ta'ammuli dasu a matsayin kuɗin haram. Don haka ko abu aka kai gidansa indai har daga gidan Alhaji Sambo ne to shi ba zai ci ba, sai dai ba zai hana iyalansa ci ba, kamar yanda idan sutura ce ba zai saka ba. Shi a tasa fahimtar yana ƙidaya cewa duk wani kuɗin yan siyasa to kuɗin haramun ne.

Ansar da Hafsa tun kafin su fara zuwa jami'a tuni sunyi nisa a nasu karatun da yake koya mata, musamman tunda tana fahimtar larabci sai abubuwan suka zo musu da sauƙi. Harma ya zamana ta kere shi a wasu abubuwan inda cikin ƙasa da shekara ta kammala haddar Alƙur'ani mai girma kamar yadda ta kammala littafin bulugul maraam da riyadh-salihin duk tare da Ansar. Dama kuma kafin su fara tayi littafai irinsu Arba'unan Nawawi da Umdatul Ahkam.

Ranar su ta farko a jami'a ko ina tare suke zuwa, documentation, laboratories registration, registration na library, na medical da sauran zirga-zirgar sabbin ɗalibai duk tare sukai.

Abin yana yiwa Ansar ciwo idan lokacin lecture yayi kasancewar ba abu ɗaya suke karanta ba sai ya zamana guraren da suke lecture ya banbanta, amma hakan baya hanashi wani zubin ya ƙyale nasu ajin ya halarci na Hafsa.

"Yaya Ansar wannan abin da kake fa bai dace ba, baka tunanin cewa rashin halartar ajinku zai baka matsala?
"Bana tunanin haka, tunda abu ɗaya muke karantawa a ajin farko, babu wani bambanci kuma abin da ake buƙata shi ne kawai mutum ya samu ya iya..." Ansar ya bawa Hafsa amsar tambayar data gaya masa. Yana mai sanya hannunsa yana karkaɗe ƙurar dake jikin jakarsa wadda take rataye a kafaɗarsa. Kalarta kuma ta saje da kalar fatar jikinsa domin kalar ruwan ƙwai ce.
"Amma wani hanzari ba gudu ba" Hafsa ta ambata, "kasan dai suna attendance ko?"
Ansar ya maida jakarsa baya yana murmushi sannan yayi ajiyar zuciya yace "Na sani, amma ba abin da hakan zai janyo tunda wasu abubuwan kawai ana yine don a tsoratar da mu."

Hafsa bata gamsu ba, don haka sai kawai ta kaɗa kafaɗunta alamar babu abin da ya shafeta.

Ansar da ganin haka sai yaci gaba da cewa "Babban abin da yasa nake tare da ke koda yaushe shine saboda ina so in killaceki, ina so in zama tamkar kariya tsakaninki da samarin wannan zamanin domin komai kamun kan mace indai suka ɗana mata tarko zai wahala ta tsallake sai tsirarun da Allah ya tseratar..."
"In dai wannan ne nima zan iya, ca nake na fika sanin kaina, na fika sanin wacece ni, na fika sanin abin da ya dace da ni idan ana magana akan kaina, rayuwata da lafiyata... Its in your blood, ku mazan nan kun cika tunanin mata basu da wayo, haka fa Abbana ya sakani a gaba harda kuka akan cewa don Allah idan nazo jami'a kada in biyewa mutanen banza... Ni kuwa gani nake babu wanda zai gaya min abin da yafi dacewa da ni. Ina da hankali, ina da ilmi, ina da tarbiyya... Thats enough..." Hafsa duk wannan bayanin da take idonta cike yake da kwalla.

Ansar ya matso kusa da ita yana mata inkiya kada mutane su gane me yake wakana a tsakanin su, amma hakan bai hana hawaye zubowa daga idonta ba.

"Hakan da muke nuna miki soyayya ce, ita mace koda yaushe tana buƙatar wanda zai nusar da ita hanya..." Ansar ya faɗa.
"Kana nufin dai kace mace kamar mota take sai da driver?" Hafsa ta tambaya tana mai kafe Ansar da ido.
"Yawwa kin gane mai nake nufi ashe..."
"Kaga, mata ba haka suke ba, suna da yanci, suna da yancin yin rayuwa, Allah bai haliccesu da raunin da sai maza sun basu kulawa zasu rayu ba."

Ganin cewa a fusace take sai Ansar yayi murmushi yace "Haka ne kam."

Tayi shiru jim kaɗan tayi gaba kawai ta ƙyaleshi.

Tafiyarta keda wuya sai ga wata budurwa wadda itama bata gaza shekara sha bakwai ba, tana zuwa tayi sallama, Ansar ya amsa.
"Ya naga idonka cike da kwalla?"

Ansar yayi murmushi ba tare da ya bata amsa ba. Sai kawai ya samu guri ya zauna a wani abin zama wanda ya kewaye wata bishiya. Da zaman Ansar itama wannan matashiyar sai ta zauna.

"Baka son zuwa aji, kuma kasan rashin zuwan ka abu ne da ba zai ɓuya ba, sabo da irinku malamai suna saurin gane ku, saboda kana da ƙoƙari sannan kuma kaga siffarka ba irin tamu bace kai fari ne tas."

Ansar yabi kyakykyawar baƙar budurwar da kallo daga bisani yayi murmushi. Lokacin da itama take murmushin wanda ya bayyanar da haƙorin makkan da ta sanya. Wani haske kamar walƙiya Ansar ya gani da yake garin akwai ɗan duhu saboda hadarin da ya gangamo.

"Maryam, inga note ɗinku na yau." Ya faɗa lokacin da yake ɗauko nasa note ɗin daya kwafa a ajinsu Hafsa.

Ta miƙo masa tana murmushi, ya kauda kansa kamar bai ganta ba, ya karɓi littafin yana gwada note ɗin guda biyu yana ƙara wasu abubuwan a nasa.

"Wannan ai son kai ne, kamata yayi idan kaga abin da ka rubuta babu a nawa littafin nima ka shigar min da shi. Amma kawai sai ka rinƙa cika littafinka da points kana barin nawa da iyakar wayanda ka tarar." Maryam ta faɗa tana wani karangaɗewa cikin shagwaɓa.

Cikin alamun tambaya Ansar ya kalleta cikin rashin gane me take nufi. Sai kawai ya miƙa mata littafinta yana mai miƙewa game da cewa sai anjima.

Mikewar da zai yi sai ya hango Hafsa nesa kaɗan da shi tana kallonsa ranta a mutuƙar ɓace. Shi kuwa sai yayi kamar bai gane ta ba ya kama hanyarsa ya wuce.

Hafsa ta bishi da kallo tayi tsaki kawai.

Zamu dakata anan.
Sai kuma mun sadu a shiri na gaba.

Fatan dai kuna jin daɗin labarin.
Hausawa suka ce wasa farin girki...

Your comments and votes are highly encouraging.

Your comments and votes are highly encouraging

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now