4

88 7 2
                                    

Da shigowar Alhaji Sambo sai Hafsa ta tashi daga gaban Ansar ta nufi mahaifinta Alhaji Sambo ta rungumeshi ta ƙanƙameshi da tsananin ƙarfi...

Shi kuma sai ya fashe da dariya yana shafa gashin kanta wanda yake kalar golden, duk da cewa asalinsa baƙi ne, lokacin data chanja kalar gashin tabbas ta tsorata matuƙa domin bata taɓa ganin ɓacin ran mahaifinta irin wannan ranar ba, domin har ɗaga hannu yayi kamar zai mareta, amma sai kawai taga idonsa ya ciko da kwalla sai kawai ya jawota jikinsa ya ƙanƙame ta, shi kuwa yayi hakane saboda kada taga kwallar da zata zubo daga idanunsa, ai kuwa hakan ne ya faru, domin ƙwallar ce ta fara zubowa bayan ya rungume ƴar tasa, da ya fahimci kwallar ba mai tsayawa bace, sai kawai ya saketa, ya juya baya yanda ba zata ga fuskarsa ba, ya daka mata tsawa yace "Get out of my sight..."

Ta tsaya ta ɗora hannunta akan bakinta, tana zazzaro ido, yau Daddy ne yake mata tsawa haka, shin abin da tayi yana da muni haka?

"I said outtttt!" Tsawarsa ta sake katse tunaninta, nan take kawai ta fara tafiya da baya da baya har ta fice daga ɗakin, bata wuce ko ina ba, sai ɗakin mamanta inda ta kwanta kan cinyar maman tata ta fashe da kuka...

Haka suka wanzu, kafin daga bisani ya saketa, yana mai kissing ɗinta a goshinta, sannan ya juya yana kallon Ansar ya saki baki don mamaki.

"Yaya Ansar, kai ne ka girma haka harda ƙasumba?"
Alhaji Sambo ya fada cikin raha. Ansar ya shafa ƙeya yana mai sunkuyar da kansa, kai kace kunyar a ƙeya take. Ya kasa cewa komai ban da murmushi kawai da yake.

"Daddy, tun ina yarinya kake ban labarin yaya Ansar, kuma komai nayi idan nayi kyau sai kace beautiful like Ansar... And today I saw him... But to my surprise he is not that beautiful... He is handsome but not as good looking as I am..." Hafsa ta faɗa tana turo baki kamar wata yar mitsitsiyar yarinya.

"Laaa," Hajiya Sadiya ta furta tana murmushi, "Ai kuwa ya fiki kyau, har fatarsa tafi taki haskawa, kawai abin da zaki nuna masa shi ne idanuwa..."
"Mom, skin is not considered as part of beauty, if it's then I prefer black than white."
Hajiya Sadiya tayi murmushi tace "Its like a proverbial blind man, da akace masa ga ido yace wari yake...".

Hafsa da Alhaji Sambo duka suka kyalkyale da dariya.

Kai tsaye Alhaji Sambo ya zarce inda Ansar yake zaune ya kamo hannunsa ya jashi wani bangare a ɗakin, suka buɗe wata ƙofa suka shiga, sunkai kusan minti goma a cikin ɗakin kafin daga bisani Ansar ya fito.

Babu kowa a harabar ɗakin bayan fitowarsa, sai Hafsa kawai wadda take ƙoƙarin yin parking ɗin gashin kanta wanda yake ta bata wahala. Tana ganinsa sai taja mayafi ta rufe kan nata. Sannan ta miƙe ta koma kan kujera. Ta dauƙi wani mini-remote akan kujerar, ta nuna wani dining table da shi tana mai danna wani madanni, take teburin ya matson inda take. Ta sake aikata haka ga wata kujera, itama sai ta matso opposite da inda tata kujerar take. Suka sanya table ɗin a tsakiya. Daga nan ta yiwa Ansar inkiya da ya zauna, shi kuwa sai ya ɗanyi jim, ya ciro ƙaramar wayarsa rakani-alwala, ya duba lokaci daga bisani yayi ajiyar zuciya yace "Ina sauri, I have a lot to do at home".

"Hmmm, Okay..." Ta juyar da fuskarta zuwa nahiyar da ɗakin Alhaji Sambo yake ta ɗan kwalla masa kira "Daddy!" Ta zarowa Ansar  ido, "naga alamar sai na kirashi zaka zauna ko?" Ta fada tana mai saka baƙin glass a fuskarta irin manyan nan.

Dariya taso kwacewa Ansar, sai ya bata haƙuri cikin raha sannan ya zauna. Yana mai kallonta.

Duk lokacin da ya kalleta sai yaji zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi, hakanan baya iya jurewa su haɗa ido... Kwarjini take masa sosai, to kodai itama an gaya mata sirrin da aka gaya masa... Wannan yarinyar ba kalar matar da yake so bace, gaskiya bazai iya auren wannan ba domin ta waye da yawa... Tunani kala-kala ya rinƙa tsere a cikin ƙwaƙwalwarsa.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now