13

38 6 0
                                    

Duk da gagarumin hadarin daya gangamo ya haddasa duhu a cikin zuciyar Ansar, hakan bai hanashi ɗaukar littafi don rage raɗaɗin abin da yake ji ba...

'Ko me Hafsa take tunani akan Maryam?'
Shi ne abin da zuciyarsa take ta saƙa masa, shi ne abin da yake ta kaikawo a cikin zuciyarsa, shi ne abin da yayi sanadiyyar tattaruwar hadari mai mutuƙar duhun gaske a sararin zuciyarsa.

Abin da  yafi bashi mamaki shi ne yanda yaji zuciyarsa tana karkata wajen tunanin maryam da kuma kyautatawar da take agareshi. Cikin hanzari ya kautar da wannan tunanin daga zuciyar sa, ya rufe idonsa ya ci gaba da kallon sama yana ƙoƙarin zuwar da wani tunanin wanda zai maye gurbin wannan tunanin da yake.

"Yaya Ansar, tunda ka dawo ba ka ci abinci ba" Ƙanwarsa Khadija ta ambata lokacin da take leƙowa ɗakinsa.
"Okay, zubo min to, saura kuma ki zubo min yaji da yawa irin kwanaki"
Khadija tayi murmushi sannan ta nuna masa abincin a gaban sa tana mai cewa "Gashi har yayi sanyi, nafi rabin awa da kawo maka amma kana can kana tunani, Yayana please irin wannan tunanin mara amfani ya kamata ka daina yinsa, I know love is king and so strong but..."
"Kinga jeki don Allah, Na gode, dama burina shi ne ki kawo abincin, kuma kin kawo."

Babu musu khadija ta juya ta barshi a nan. Ansar ya janyo wannan abinci kusa da shi da a zummar ci amma bisa ga mamakinsa sai yaga ya kasa cin abincin. Da ƙyar ya samu ya iya yin wasu malalatan loma guda biyu.

"Wahidiy
Sadaka
Iya ko ɗan dago-dago
Iya almajiri yana bara
Iya allazi kalaƙa bayin Allah"

Almajiri ne cikin jerin almajiran da suke bara ya leƙo gidan yana bara, yana mai kafe Khadija da idanuwa lokacin da take wanke-wanke a tsakar gidan.

"Almajiri" Khadija ta kirashi, kafin ya shigo tayi maza ta shiga ɗakin Ansar ta ɗauko abincinsa ta miƙawa almajirin. Wanda ga mamakin ta sai kawai taga harya zo tsakiyar tsakar gidan yana zazzaro ido kamar mara gaskiya. Kasancewar ta ga yaro ne ƙarami sai ta mantar da zuciyar ta akan kutsowa cikin gidan da yayi.

Almajirin yayi godiya ya bita da kallo ya ƙi tafiya, cikin mamaki tace masa "Shi kenan ai, ko kana buƙatar wani abu ne kuma bawan wannan."

Almajirin yayi murmushi yace "A'a, a ƙauyenmu muna kallonki a film ɗin india, akwai wani film da aka yanki mijinki a wuya aka jefashi cikin ruwa, kuma ainihi shi ɗin kurma ne amma a ƙarshe sai bakinsa ya buɗe dama ya kurmance ne saboda garwashin wuta da aka zuba masa a baki... Don Allah wai da gaske mijin naki sharifi ne? Naga a Film ɗin wuta bata ƙona shi ba ..."

Ita dai Khadija kawai ta saki baki tana kallon almajiri wanda a nata tunanin har yanzu yana buƙatar kulawar iyayensa amma gashi an turo shi bara. Irin wayannan a abin da take kyautata zato sune idan suka girma suke juyewa zuwa yan fizge, ɓarayi, da yan fashi da makami, dama tun suna yara wayanda suka fi kamata ace sun ja su a jiki sune sukai watsi da su, to don me su kuma zasu ji ƙan al'umma alhalin jin ƙai a wajensu wata kalma ce da babu ita, tausayi baya cikin jerin gwanon kalmomin da suke wanzuwa a kundin kalmomin ƙwaƙwalensu...

Firgigit ta bar wannan tunanin ta dawo zuwa ga hankalin ta don ganin halin da wannan almajiri yake ciki, ai kuwa sai taga babu almajiri babu dalilin sa, rashin ganin almajirin ba shi ne abin da yafi ƙona mata rai ba, abin da yafi ƙona mata rai shine rashin ganin wayar ta ƙirar android...

Ta bazama tayi hanyar soro don duba almajirin, tana zuwa soro sai kawai ta ji an daka mata tsawa, jikinta na ƙyarma ta durƙusa, tana cewa "Baba yi haƙuri, wani... Wani... Wani..."
"Karki kawo min zancen banza anan fa, don me zaki yo hanyar waje haka? Kuma doka ta kika karya da zaki ce inyi haƙuri, ai gafarar Allah zaki nema tunda fita kike son yi haka ko hijabi babu... Khadija anya lafiyarki ƙalau? Ina miki kallon mai hankali ashe kema in kika samu dama irin yaran zamani za ai..."

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now