18

47 6 0
                                    

Idan ran Ansar yayi dubu to tabbas ya ɓaci baki ɗaya.

Ya kalli mazajen da suke gaisawa da Hafsa sai a lokacin ya fara gane fuskokinsu, sune dai wayannan da suka zo har ajinsu suka yanka masa kashedi cewar kada ya sake kula Hafsa. Nan take zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi yaji kamar yaje ya rufe su da duka, a ƙarƙashin zuciyarsa kuma yana tunanin yanzu idan yaje ya rufesu da duka menene hujjarsa, a haka dai kawai yaji gangar jikinsa tana jansa zuwa inda suke, ya nufesu a lokacin da suka juyo suna kallonsa dukkanin su suka ɗaure fuska babu alamar fara'a a tattare da su.

Hafsa ta bazamo cikin gaggawa ta tare shi a hanya tana mai shan gabansa, yayi ƙoƙarin kauce mata amma sai kawai ta riƙe kafaɗunsa guda biyu ta jijjigashi.

"Me yasa kake haka ne? Wai don Allah yaushe zaka waye ka daina wannan ƙauyancin? Nan fa University ce ba Islamiyya ko makarantar Allo ba." Hafsa ta faɗa cikin faɗa duk da dai bata ɗaga murya yadda zasu jiyota ba.

"Hafsa, ki tuna sunanki mana, sunan wannan matar ce wadda mahaifinta shi ne na uku a daraja cikin wannan al'umma yayin da mijinta yake da daraja ta farko, shin hakan bai isa ya sanyaki kiyi ƙoƙarin koyi da ɗabi'unta ba? Shin kin manta cewa Allah babu ruwansa da jami'a don haka duk inda kake mutuƙar kayi zunubi to zunubi ne...?"

"Wa'azi zakai min? Kai ba zaka fara yiwa kanka ba, ka manta ayar da Allah yake cewa ku ji da kawunanku, wanda ya ɓata bazai cutar da ku ba mutukar kun shiryu..."

"Wata rana sayyadina Abubakar ya hau kan mumbari yayi raddi akan masu yiwa wannan ayar wannan fassarar... Ca nake kin karanta a tarihinsa cikin tarikul khulafa na Suyuɗi. Kinga yanzu sai muga da ke da Sayyadina Abubakar wanene yafi fahimtar Qur'ani.
"Kuma kin yarda kenan ke akan ɓata kike idan hakane kuwa kinga baki da hujja a wajen Allah face ki gaggauta tuba sannan ki gyara..." Ansar yana magana ne cikin lumana harma yakan saka murmushi.

"Ansar" Hafsa ta faɗa lokacin da ta ƙara kusantarsa "Abin da nake ba laifi bane, wayannan abokai na ne, kuma babu wani abu da muke da ya saɓawa addini, muna tattaunawa ne akan ci gaban rayuwarmu... Be wise please."

"Wayewar da zata halatta cuɗanyar maza da mata ba wayewa bace tsantsar gargajiyanci ce, baki da labarin cewa a America da suka fi ko'ina tutiyar wayewar cikin kowane mutum biyar zaki iske guda a cikinsu yana aikata zina da abokiyar aikinsa ko karatunsa? Kuma kina sane da cewa suna sa yawaitar ya'yan shege?"

"Kana nufin muma mazinatan ne kenan?" Ta tambaya cikin zaro ido.

"Ba haka nake nufi ba, ina son nuna miki wayewar ƙarshen abin da take jawowa kenan." Ya bata amsa. Su kuwa abokanta har yanzu suna can gefe kawai sun zuba musu ido.

Wani gajere a cikinsu sai tsuma yake yana tsalle yana kaiwa iska duka kamar yana shirin Ansar yayi wani abu don ya cin masa.

"Yaya Ansar" wannan karon muryar Hafsa tayi ƙasa-ƙasa "bansan me yasa baka yarda da ni ba, ina maka rantsuwa da Allah babu abin da zai sameni a abubuwan da kake zato, na gaya maka ina da wayo ina da dabara, kuma suma wayannan abokan nawa da kake gani tare da su muke rigima akan yaƙi da rape, sex harassment da sauransu, abin da ya kamata kayi shi ne kaima ka shigo, yawaitar irinmu a cikinsu zai sanya tafiyar ta ƙara armashi..."

"Hafsa koda yaushe ina nuna miki cewa sufa maza ba ababen yarda bane musamman irin wayannan, mace tamkar barewa take, su kuwa maza tamkar zakuna suke, kuma koda yaushe a yunwace suke, don haka baiwar gudu da Allah ya bawa barewa shi ne abin da mace zatai amfani da shi don kare kanta daga maza, wato ta guje musu ta guji zama da cakuɗuwa da su."

"Yaya Ansar kayi haƙuri amma baka son gaskiya ne kawai, kawai soyayya ta rufe maka ido, shifa kishi ba hauka ba ne, kawai ka ɗauki karan tsana ka ɗorawa mutane haka kawai." Tana faɗin haka kawai ta juya ta barshi a wajen a tsaye, yana kallon tufafinsa wanda ya ɓaci da abinci.

"Kayi haƙuri Ansar." Hafsa ta faɗa lokacin da taje gab da riskar abokananta da ƙawayenta. "Wata rana zaka gane abin da nake nusar da kai."

Zuciyar Ansar tayi mutuƙar duhu, yaji kamar ya fashe da kuka don takaici amma sai kawai ya cije ya juya ya nufi hanyar komawa inda abokan karatunsa suke. A zuciyarsa yana ta saƙe saƙe da tunane tunane akan hanyoyin da ya kamata ya bi don ganar da Hafsa gaskiyar lamari.

Tabbas yasan cewa ta haɗu da irin samarin nan masu daɗin baki wayanda mutuƙar zaki sauraresu to zuciyarki koda takai karfin dutse sai sun shigar da saƙon da suke son shigarwa ciki, kuma mutuƙar zaki juri saurara da karɓa a ƙarshe sai sun juyar da ke zuwa kalar da suke so.

Tabbas mazaje tamkar zakuna suke yayinda mace take tamkar barewa a cikinsu, mutuƙar bata nesanta da su ba tabbas a ƙarshe zasu cimmata kuma su lalata rayuwarta daga bisani su tafi su ƙyaleta.

To wai mutanen da an guje su ma ba a tsira ba balle kuma ace an kusancesu. Tabbas Hafsa tana buƙatar kulawa daga gareshi akan wayannan mutanen. Ko ba don amanarta ta da take wuyansa ba. Tunda shi zata aura kuma a matsayin ƙanwa take a wajensa don haka ya zama dole yasan yanda zai yi ya shawo kanta ya ganar da ita irin matsalar da take shirin jefa kanta ciki.

Take ya ɗauko wayarsa, ya shirya saƙo cike da bayanan da suke zuciyarsa tas ya tura mata, ya ci sa'a tana online. Bayan kamar minti goma sai yaji tayi reply.

Na gode, amma maganarka har yanzu tana cike da gilli da tsanar mutanen da nake tare da su, abin da nake so ka fahimta bafa kai kaɗai ne mutumin ƙwarai ba, yanda kake jin kasan ya kamata suma haka suke jin sun san ya kamata.
Allah yasa mu dace.
A gaida su Khadija.
Still love you!

Ansar yana gama karantawa kawai ya dafe kansa yana mai ajiyar zuciya. Shi kam ya kasa gane kan wannan yarinyar. Nan ya shiga tunanin mafi kyawun hanyar da zaibi don ganar da ita.

Yayin da itama a can take ta tunanin tsaurinsa yayi yawa kuma take ta neman hanyar da zata bi don ganar da shi.

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Sai kuma a rubutu na gaba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now