11

37 6 0
                                    

Tun kafin asuba Ansar ya shiga banɗaki yayi wanka ya sanya kayansa masu kyau game da fesa turare kamar yadda mahaifinsa ya koyar da shi, domin mahaifinsa in akwai abin da yafi tsana to shine yaga mutum ya tafi masallaci ba cikin kwalliya ba. Akwai wani lokaci da hatta liman sai da Alhaji Nasir ya gaggaya masa magana akan yana zuwa masallaci da kaya a duƙunƙune, duk da dai hatta Ansar sai da ya bayyanawa mahaifin nasa cewa lallai hakan da yayi abu ne mai kyau amma bai biyo ta hanya mai kyau ba.

Bayan Ansar ya dawo daga masallaci sai ya zauna yayi zikirai bayan kammalawa kuma sai ya miƙe ya ɗauko littafinsa na boko ya fara karantawa kafin gari yayi haske ya fice zuwa makaranta.

Ji yayi wayarsa tayi ƙara, ya miƙe ya zareta daga cajin daya sakata, sannan ya buɗeta don ganin abin da ya shigo.

Iron man, fatan ka tashi lafiya, dama cewa nayi bari na kiraka kada ka makara.
Maryam

Ansar yayi murmushi ba tare daya bata amsa ba, sai shi kuma ya kamo sunan Hafsa ya tura mata nasa saƙon.

"Aikin kenan, kullum cikin danna waya." Alhaji Nasir mahaifinsa ya faɗa lokacin da yake bakin ƙofar ɗakin nasa.

Ansar bai tanka masa ba, sai kawai ya ajiye wayar a gefe ya kuma miƙe ya ɗauki baƙar jakarsa, ya buɗe wata drawer ya ɗauki kuɗin makaranta yayi sallama da mahaifinsa, har ya fita ya dawo, ya shiga wajen mahaifiyarsa da kanwarsa suka gaisa sannan ya fice.

Haka ya tsaya a bakin titi yana jiran abin hawa, bayan kamar minti goma sai ga driver na gidansu Hafsa tare da ita. Ya tsayar da motar gaban Ansar, Ansar ya shiga motar suka gaisa da driver.

Hafsa ta miƙo masa hannu, kawai ya bita da kallo yana mai girgiza kai game da cije leɓe.

“Whats wrong with you?” Hafsa ta tambayeshi lokacin da take matsowa kusa da shi.
“Ke, bana son shashanci please” ya faɗa yana ƙirƙirar murmushi a fuskarsa “Akwai abubuwan da basu dace ba sai bayan aure, Allah ba ruwansa da zamani da kuma yawan mutanen da suke aikata laifuka. Don samarin yanzu da yammatan yanzu sunyi normalizing soyayyar shan minti hakan ba zai sauya soyayyar daga haram zuwa halal ba, sai dai ma haramcin ya ƙaru domin aikata haram tare da ƙudurce halaccinsa laifine mai girma, kai bari ma dai yana cikin abubuwan da suke warware musulunci...”.

“Naji wannan, sai kuma wannan karatu zakai min?” Hafsa ta tambayeshi tana kanne ido guda ɗaya.

Kawai Ansar girgiza kai yayi baice mata komai ba, ganin haka yasa ta ƙara matsowa kusa da shi tace “ina magana kayi shiru.” ta faɗa lokacin  da take ƙoƙarin haɗa fuskarsa da tata.

Ansar ya sanya hannayensa guda biyu ya kare fuskarsa, da yaga kusan da take da shi yayi yawa sai kawai ya daka mata tsawa, ai kuwa take ta fara kakkarwa tana mai zare ido tana kallonsa.

“I am just playing fa” ta faɗa lokacin da take turɓune fuska idanuwan cike da ƙwalla.
“Bana son irin wannan wasan, idan na ɓata miki rai kiyi haƙuri.” Ansar ya faɗa lokacin da yake kallon screen ɗin wayarsa yana murmushi.

Wani abu ya tokare maƙogwaron Hafsa taji kamar ta fizge wayar ta jefata waje ta tagar motar, irin ƙatuwar motar nan gingimari tazo ta bi ta kanta, kuma a nemi sim ɗin a rasa...

“Hakan ba zai taɓa faruwa ba...” Ansar ya faɗa yana kallon fuskarta ido da ido.
“Abin da yasa nake son hakan ya faru shine yanda kake nuna wayarka ta fini...”.
“Nifa ba dake nake ba, maganar assignment ne wata yar ajinmu take son wai bayan na bata ta kwafa in tsaya yi mata bayani saboda malamin zai iya cewa kowa sai ya amsa tambayoyi akan abin da ya rubuta...”

Hafsa dai kawai ta bishi da kallo, daga bisani kuma kamar wadda akaiwa wahayi sai tayi murmushi tace “Naga saƙonka da safe, nagode.”

“Ohhh, ai inaga in daina turo miki saƙo, saboda na fuskanci indai magana ta danganci soyayya bakya bani amsa, sai mun haɗu saiki hau borin kunya...”
“Ramawa nake, kuma ina so ka gane cewa soyayya ba'a text message take ba, a aikace take.”
“In haka ne kam, kina da damuwa, ita soyayya irin wannan da kike magana ai bata halatta ba sai bayan aure. Ni da an biye min ma da aure aka fara yi mana kafin karatun nan, tunda naga ke a matse kike...”
“Hahaha, ba don kada kace bani da kunya ba, ko kace har yanzu akwai ɓurɓushin europe a tare da ni aida na faɗi wata magana...”
“Yi shiru ba sai kin faɗa ba, nasan yanzu sai ki sakar mana layi.”

“Wai ba zaku makara ba kuwa, tun ɗazu nayi parking kunƙi fita gashi takwas ɗin har saura minti uku yanzu”. Driver ya faɗa yana mai kallonsu ta madubin cikin motar.

Cikin mamaki duka su biyun suka saki salati, kowa ya ɗauki jakarsa suka nufi inda zasu ɗauki karatun.

Hafsa taga Ansar yana biye da ita sai kawai taja ta tsaya. "Yayana please don Allah karka biyo ni, ni wallahi kasa an fara surutai a kaina a makarantar nan."

Ansar ya bita da kallo domin da tayi masa maganar kawai gaba tayi bata tsaya jiran amsarsa ba.

Nan ya tsaya yana kallonta har sai da wasu makararrun yan ajinsu suka zo sukai gaba da shi amma duk da haka bai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa ba, idonsa cike da kwalla, gani yake kamar wani abu zai samu Hafsa, ji yake kamar ya ita ɗin wata barewa ce da ya bar ta ta shiga cikin garken zakuna...

Kansa ya ɗauki zafi, wani irin abu ya rinƙa zarya a jijiyoyin jikinsa, tunani kala kala ya rinƙa yi masa kaikawo, abokan tafiyarsa tun suna magana suna jin sa shiru suna ɗaukar yana sane kamar ƴanda ya saba wasu lokutan har suka gano cewa lallai akwai matsala a tattare da shi.

Haka ya shiga ajin ana karatu amma kawai sai ya kifa kansa, daga bisani bacci ya ɗauke shi.

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Me kuke tunani dangane da Ansar da Hafsa?

Me kuke tunani dangane da Ansar da Hafsa?

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now