8

57 8 6
                                    

Fitar su harabar gidan keda wuya suka iske Alhaji Sambo yana ƙoƙarin ɗaga wata ƙatuwar ƙofar ƙarfe data danne wata mata da alama macece mai manyan shekaru.

Ansar a razane ya kalli Hafsa yana mai zaro ido yace "mamanku?"

Bai jira ta bashi amsa ba yayi tsalle daga inda yake ya nufi inda Alhaji Sambo yake kici-kici da wannan ƙatuwar kofar, yana ƙarasawa ya saka hannunsa guda biyu suka yunƙura tare cikin tsananin jarumta dukkaninsu suka tattare ƙarfinsu don ɗage wannan ƙofa amma ina, yayin da ƙafafuwan wadda ƙofar ta danne har yanzu suna hahharbawa.

Kan kace me security ɗin gidan sun ƙaraso inda suma suka sanya hannu, amma duk da haka da ƙyar aka iya ɗauke wannan ƙofar, sai ga wannan mata kwance cikin jini. Ansar ya juya ya kalli Hafsa wadda take ta faman zubda hawaye ta rasa inda zata saka kanta.

Ba'a wani ɓata lokaci ba sai ga motar asibiti tazo, inda cikin hanzari aka sanya wannan mai tsautsayin a ciki yayin da Alhaji Sambo da kansa ya shiga motar, tare da umartar Ansar da Hafsa da su zauna a gida.

Da kyar Hafsa ta yarda ta zauna... Ansar ya tsaya yana bata baki.

Har dai ya shawo kanta tayi shiru. Suna zaune a harabar gidan sai tsohuwar wayar Ansar tayi ƙara alamar kira. Cikin hanzari ya ɗaukota ya mike tsaya ya karata a kunnunsa.

"Innalillahi wa innailaihi raji'un"
Itace kalmar da Hafsa taji ya furta lokacin da yake sakin wayar da take hannunsa. Hafsa ta zazzaro ido tana mai dafe ƙirjinta wanda yake bugawa da tsananin sauri tunani kala-kala yana mata kaikawo a kwakwalwarta.

"Yaya Ansar, lafiya kuwa?"
Ta tambaya amma ga mamakinta hankalinsa gaba ɗaya yana bayanta, ya saki baki sannan idonsa yana cike da alamomin tambaya...

Hafsa ta rasa me hakan yake nufi, tayi masa magana a karo na biyu amma abin da ya faru a farko shi ne dai abin da ya sake faruwa... Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa...

Hafsa ta juya taga wai me yake kallo, itama kawai saita saki bakinta tana mai kallon ikon Allah. "To menene abin mamaki anan?" Hafsa ta tambaya lokacin da take juyawa tana mai kallon yaya Ansar.

Sai a lokacin Ansar ya dawo hayyacinsa.
"Kina nufin kice babu mamaki a cikin wannan al'amari?"
Ansar ya tambaya yana mai matsawa da baya kamar mai shirin guduwa.

"Nifa na kasa gane me kuke haka?"
Mahaifiyar Hafsa ta tambaya.

"Me yake dai, ai shi ne mai abin mamakin, ni kaina mamaki yake ba ni..." Hafsa ta amsawa Sadiya mahaifiyarta.

"Abin mamakin shi ne naga yanzu abu ya faɗo miki kun tafi asibiti kuma naganki still anan..." Ansar ya faɗa muryarsa na rawa.

Duk da suna cikin tashin hankali hakan bai hana Hafsa kyalkyala dariya ba. Don sai da ta kwanta saboda dariya.

"Wai shi ne kayi tsuru-tsuru haka? Koka zata fatalwa ka gani ne?"
Maman Hafsa ta tambaya da fara'a bisa leɓɓanta.

"Waccan ba mama bace, yar aiki ce, kuma mutuniyar kirki ce walahi bata rabo da carbi kullum cikin ambaton Allah take, kuma tana da ƙoƙarin kare mutuncinta don a matsayinta na yar aiki ko ni ko mama babu wanda ya isa ya taka ta, shiyasa muma muke son ta saboda she is so bold and confident..." Hafsa ta faɗa tana mai ƙoƙarin tare hawayen da zai zubo da bayan tafin hannunta.

Itama maman Hafsa sai hawayen kawai ya fara zuba daga nata idanun.

Ansar ya tsaya ƙiƙam yana tuhumar kansa akan rashin zubar da kwalla da yayi.

"Tsayuwa babu abin da zata ƙara, mu zauna kawai" inji Sadiya.

Suka zazzauna kowa yayi shiru, amma lokaci zuwa lokaci musayar kallo tana shiga tsakanin Hafsa da Ansar, wanda Hajiya Sadiya tana ankare don haka sai ta sake tashi ta bar ɗakin.

Ansar a zuciyarsa kuwa yana ganin tashin da tayi a matsayin kuskure, don me zata tashi ta barshi shi da Hafsa alhalin tasan dukkaninsu sun manyanta kuma shaiɗan zai iya gindaya komai a tsakaninsu, yanzu idan shaiɗan yayi galaba akan zuƙatansu me zai faru...?

"Allah ya kiyaye, amma abin bazai kyau ba." Sautin Hafsa ya katse Ansar.

"Kamar yaya?"
"Ban gane kamar yaya ba, me kaji nace?"
"Kinji abin da na faɗa da farko ne?"
"Naji mana."
"To me nace?"
"Kamar yaya?"
"Abin nufi ki faɗi abin da nace da farko."
"Ai abin da kace kenan, ni ce na fara magana kai kuma sai kace 'kamar yaya?'".
"Alhamdulillah tunda bakiji me nace ba."
"Hmm".

Sai wayar Ansar ta ƙara wata ƙarar nan take ya ɗauketa ya ɗaga.

"Me kake ne baka dawo ba?" Muryar mahaifinsa yaji. Alhaji Nasir.
"Ahhhh, an samu matsala ne shi ne..."
"Matsalar me? Ai matsala kullum a cikinta ake, kawai ka taho gida. Ku babu dama a samu damar fita sai an ɗagawa mutum hankali... Awarka nawa da fita?..."
"But Baba shi ne yace fa..."
"Lallai baka da kunya, but kake ce min ko? Wato wuyanka a isa yanka ƙarfinka ya kawo zakai jayayya da ni ko? Ku yaren yanzu me yasa baku da tarbiyya ne. Hakafa kwanaki..."
Sai Ansar kawai ya katse kiran yana ajiyar zuciya.

Bai gama nutsuwa ba saiga kiran ya kuma shigowa...

"Yaya Ansar kawai kaje gida, zan yiwa Abban bayani idan ya dawo..."
"Nagode"

Ansar ya tashi da sauri lokacin da yake ɗaukar wayar. Yana mai nufar ƙofar fita daga harabar gidan zuwa parking lot daga nan kuma zuwa waje. Ya sanya ƙafarsa ɗaya kenan zai fita sai ya juyo ya kalli Hafsa. Ta sakar masa wani murmushi mai mutuƙar ƙayatarwa. Ya mayar mata yana mai ɗaga hannu. Ɗaya hannun kuma yana rike da laptop ɗinsa sabuwa.

Ta sanya hannunta akan bakinta ta sumbaceshi ta nuno masa, ga mamakinta sai taga ya ɗaure fuska yayi tsaki ya fice.

Sai kawai ta ɗora hannunta akan goshinta tace "O My God".

Me hakan yake nufi? Ansar ya tambayi kansa da kansa, wannan yarinyar idan banyi a hankali ba lalatani zatayi da alama. Wato irin abin da taga anayi a fina-finan turawa shi ne itama take ƙoƙarin yi, koda yake dama a can ta taso dole a rinƙa yi mata uzuri. Cewar wata zuciyar. Habawa ina wani uzuri, ai Allah ba ruwansa da inda mutum ya taso. Wata zuciyar ta bashi amsa.

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba idan Allah ya yarda.

Me kake tunanin zai afku a gaba.
Ko yaya jikin yar aiki?
Ko menene dalilin neman Ansar cikin gaggawa a gidansu?

Comment and vote are needed!

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now