25

30 1 0
                                    

"Alhamdulillah, tunda ba su illata kin ke ba", Mahaifiyar Hafsa ta faɗa tana mai shafa kan ƴartata wadda ke kwance akan cinyarta, biyo bayan bata labarin abin da ya faru da ita.

"Bari na yi maza na kira Bank officer ɗinki in ji ko sun fasa bankin na ki tunda akwai alamun tambaya akan abin da ya faru..." Alhaji Sanda mahaifin Hafsa da ke zaune a kujerar da ke fuskantarta da mamanta ne ya faɗa lokacin da ya ke laluben lambar wayar Bank officer ɗin.

"Dad, what do you mean by "alamun tambaya?" Hafsa ta tambaya tana bin mahaifin na ta da kallo, tana kuma tunanin cewa yanzu fa akwai wani lokaci da ya shuɗe da shi wannan mahaifin nata da take ganin cewar ya fi kowa girma a duniya yake mataki irin nata... Koda yake ma da can jariri ne, sai dai da kallo ɗaya babu wanda zai tunanin cewa akwai lokacin da the whole Alhaji Sanda yake lulluɓe cikin zanin goyo, mata suna kallonsa suna ɗaukarsa suna addu'ar Allah ya raya...

"Haba ƴata... "Muryar Mahaifin nata ta katseta. "Mutanen da idan suka kwaci waya ba ruwansu da ka cire musu password, da kansu za su je su yi hacking komai, kuma su yi abin da suka ga dama... To amma ke kinga a lokacin suka karɓa directly suka ce lallai sai kin buɗe musu..."
"Baba wataƙila kuɗin hacking ɗin ne da yawa shi yasa sai sukai amfani da wannan damar don cire security ɗin kan wayar sai ayi abin da ake ai da ita, ni babban tsorona ma shi ne abubuwa na da suke ciki, da abubuwa masu ɗimbin tarihi... Bayan nan  kuma ga hotunana da bana son wani ya gansu..."
"Ji yarinya da shirme don Allah, ni abin da nafi ji shi ne, lallai ba wayarki ko kuɗin bankin ki kaɗai suke son sacewa ba, sai dai lallai suna son samun wani abu ne na dabam, ina son lallai duk wani abu da ya biyo bayan satar ko kwacen nan ki sanar da ni, musamman abin da kika fuskanci yana da alaƙa da wannan fashi da akai miki..." Alhaji Sanda ya faɗa lokacin da yake saka wayarsa a kunnensa... Bayan ya gama wayar kuma ya juyo ya kallesu yana mai zazzaro idanu.

"Lafiya, Dear?" Mahaifiyar Hafsa ta tambayeshi.
"Babu abin da suka taɓa a bankunanta." Sanda ya ba da amsa.
"Alhamdulilah..." Ta faɗa za tai murna... Mahaifinta ya kallota ya galla mata harara, daga nan ya ja gwauron numfashi ya ce "Wallahi ina jiye mana tsoron kada abin da za ai da wannnan wayar ya fi sharri sama da neman kuɗi a rasa. Lallai akwai abin da aka taka, kuma ake nema..."

Da  jin haka sai jikin Hafsa da mamanta yayi sanyi, sukai cirko-cirko sukai tsuru-tsuru aka rasa wanda zai ce wani abu.

"Koma dai menene, Allah ya fi su." Hafsa ta furta tana mai miƙewa ta nufi hanyar ɗakinta, ta shige ta kwanta akan gado, tana ta tunane tunane, da kuma tunanin irin sirrikanta da suke cikin wayar... Wasu hotunan ba ma anan ta ɗauke su ba, ta ɗauke su ne tun zamanta a turai, kuma sau da dama takanyi yunƙurin gogewa, amma idan ta tuno hotuna ne na tarihi sai ya bar su. Babban abin da take gudu shi ne, ita ƴar gidan babban ɗan siyasa ne, don haka kuskurenta guda zai iya jefa tafiyar siyasarsa cikin hatsari.

A haka har dare yayi, bayan tayi sallar  Isha'i ta jero Shafa'i da Wutiri, sai ta koma kan gado ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya sai ta ji ƙaramar wayarta ta fara amsa kuwwa alamar an bugo. Cikin hanzari ta miƙe ta je ta ɗakko wayar... Ta duba ta saki murmushi saboda ganin wanda ya kirata, dama kuma bayan shi babu wanda keda wannan lambar sai wasu tsirarun ƙawayenta da kuma mahaifanta. Ansar shi ne sunan da ya fito akan screen ɗin.

"Hello" ta faɗa tana lanƙwasa murya.
"Assalaamu Alaikum, na gaya miki bana son hello din nan."
"Wa salaam... Na manta"
"Wa salaam? Haka aka koya miki a musulunce?"
"Na gaya maka an kwace min waya?"
"Wannan ke ya shafa, ni dai ina ƙara jaddada miki ki bi duniya a sannu, domin ba ta da tabbas, kuma duk yanda mutum ya kai ga wayo da ɓoye abu dole watarana dubunsa za ta cika."
"Ban gane me kake nufi ba..."
"Kuma wa kika turawa hotunan?"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Hafsa ta faɗa tana mai dafe ƙirjinta wanda ya fara bugawa da ƙarfi..."
"Tambayarki nake..." Muryar ce Ansar ya tambayeta cikin murya mai kama da tsawa.
"Wallahi Tallahi kwace wayar akai..."
"Rufe min baki, jahilar banza kawai, wadda ba ta amfani da ilminta, ace hotuna har da na batsa... Iyayenki ba su san ciwonki ba, ba su san ciwon kansu ba, ba ruwansu da musulunci sai bokon banza da wofi, kuma..."
"Kaga Mallam dakata, abin ya fara yawa..." Hafsa ta dakatar da mai maganar. Sannan ta ci gaba da cewa "Ƙarya ne kace akwai hotona na batsa a wannan wayar, idan kace ƙananun kaya dai zan yarda, amma menene na dole sai ka haɗa da ƙarya... A haka kake cewa kai malami ne... Kuma iyayena ba sa'anninka ba ne, don haka faɗa da cacar baki tsakaninmu ne mu biyu, kada ka ƙara sakosu a ciki indai ba so kake in saɓa maka ba..."
"Daga lokacin da kika fara bin wayannan yan iskan na tabbatar da cewa kin bar hanyar gaskiya, kuma kin saki reshe kin kama ganye, nasan ko yanzu kasuwa ta tashi sun ci riba don nasan babu abin da ba kwa yi..."

Saboda fusata Hafsa ba ta san lokacin da tayi jifa da wayarta zuwa ga madubin ɗakin ba, wayar ta tafi tana keta iska tana wulwulawa yayinda mai magana ta cikin wayar yake ta faman kyalkyala dariya, wayar ta daki madubin ta tarwatsashi wata ƙara ta karaɗe gidan gaba ɗaya, ita kuma Hafsa ta sulale ƙasa rikicaa sumammayi.

A dai dai lokacin babanta da mamanta suka shigo suna jijjigata suna yayyafa mata ruwa, amma shiru babu alamar motsi.

Zamu dakata a nan, sai kuma a rubutu na gaba.

Tare da ni
Naseeb Auwal

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now