22

28 1 0
                                    

Gari yayi tsit, ba ka jin ƙarar komai sai ƙarar takun sawayen wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya, fuskokinsu a rufe, ga dukkan alamu marasa gaskiya ne, haka suka wanzu suna tafiya suna masu raba idanuwansu dama da hagu don ganin abin da ke kaiwa da kawowa.

Su biyar ne, huɗu a jere, yayin da ɗaya daga cikinsu yake gaba.

"Junior. Nifa na kasa ganewa wannan tafiyar  ta mu, idan ba ka gane gidansu ba kawai ka zo mu juya... Yanzu cikin tsohon daren nan wanene zai ganmu bai kawo wani abu a zuciyarsa ba..." Ɗaya daga cikin huɗun da suke jere a baya ya faɗa lokacin da yake sassarfa don tarar da na gaban, ko juyowa na gaban bai yi ba balle ya bawa mai maganar amsa.

"Nima dai naga tafiya muke kamar wasu barayi. Wai don Allah Junior menene amfanin wannan operation ɗin?" wani dabam cikin su ya sake faɗa yayin da yake cire sigari daga kofar da take bayyane a takunkumin da ya rufe fuskarsa, kofar kuwa tana sadar da wannan sigari zuwa ga matsakaicin bakinsa wanda yake fitar da zafafan haruffa. 

"Ba za ku gane ba ne, da kun san irin raɗaɗin da nake ji a cikin zuciyata akan wannan nacaccen Ansar ɗin, da ba za ku tambayeni irin waƴannan tambayoyin ba... Ji nake yau idan na dira a gidansu kawai in kawar da shi har lahira..." Junior ya faɗa yayinda idanunsa suke zubar da wani zazzafan hawaye.

Dukansu suka tsaya sakamakon jin ambaton kisa da Junior yayi domin dukansu ba su yi tsammanin abin da ya fito da su kenan ba, su abin da sukai tunani shi ne wannan fita ce irin fitar dare da suka saba yi zuwa clubs da gidajen rawa.

"A Shawarance idan har wannan ne dalilin da yasa ka fito da mu to ina baka shawara kawai mu koma."
"Mu koma kuma? Please Let's go, can't you respect my feelings?"
"It's not matter of respecting your feeling my friend... Ina jiye mana abin da zai je ya dawo..." Mai maganar bai kammala rufe bakinsa ba sai sauran suka ƙarfafi maganarsa.

Dukansu suka ja suka tsaya har da shi Junior, daga nan kawai Junior yayi ƙwafa gami da ajiyar zuciya ya buga ƙafarsa kawai ya juya. Suka bishi a baya kamar kaza da ƴaƴanta.

★            ★              ★

Bayan sun koma club sun fasa zuwa gidansu Ansar, sai suka zauna suna shawarwarin yanda za su ɓullowa mafi girman matsalarsu, kuma mai hana su jin daɗin rayuwarsu.

Roget, shi ne aminin Junior wanda ba shi da kamar sa, domin hatta ƴan makarantar su da yawa sun zata Roget ɗan ajinsu ne, saboda koda yaushe yana tare da Junior a cikin makarantar in ka ɗauke wasu ƴan tsirarun lokuta da wani uzurin ya ke hana su shigowa. Roget shi ne ya kawo maganar da a ƙarshe duk suka yarda da ita.

"Dukkanku na raina tunaninku." Roget ya cigaba da cewa "Ga amsa ƙiri-ƙiri dangane da tambayoyinku amma kun tafi kuna ta kewaye da shure-shure cikin duhu." Ya ɗan yi shiru yana gyara naɗin tabar wiwin da take hannunsa bayan ya miƙawa Junior wadda yayiwa zuƙa ɗaya.

Junior ya buɗe baki hayaƙi yayi ambaliya ya wanke gaban fuskarsa cikin wani yanayi mai kauri kai kace gobara ake daga cikin bakin nasa, daga nan wata ƙaƙƙarfar matashiyar guguwa ta keto ta cikin bakin nasa biye da muryarsa biyo bayan tarin da yayi saboda ƴar kwarewa da yayi yace "Ina amsar? Mu bamu sameta ba, da ace mun ganta ko mun hangota aida tuni mun jima da aiwatar da ita."

Roget yayi dariya wadda dalilinta wasu ƴammata da suke gefensu sai da suka tsorata, sannan yace "Mun san abin da Hafsa take so, mun san abin da ta tsana, mun san abin da Ansar ya ke so, mun san abin da ya tsana... To kawai ƙoƙari zamu yi ita mu maida ita abin da ba ya so, shi kuma mu ƙara masa himma da shafa masa kashin kaji akan abin da ba ta so..."

"Amma kasan gayen ne babu yanda za ai mu iya juyashi fa." Junior ya katse Roget.

"Kawo kunnenka ka ji." Roget ya matsa, yayin da Junior ya kusanto da kunnensa. Ai kuwa sai ya gaya masa wasu maganganu nan take suka kyalkyale da dariya suka rungume juna.

Daga nan Roget ya tashi ya je wajen matan nan yayi musu magana, sun ɗauki tsawon mintuna suna ja-in-ja sannan daga bisani suka biyo bayansa.

Su biyar ne kamar yanda adadin su Junior yake, koda suka zo inda Junior suke zazzaune sai kowacce ta zaune akan kujera tana fuskantar ɗaya daga cikinsu.

Junior ya miƙe, ya kalli Roget ya ɗan yatsine fuska yace "Kasan fa ni bana harka da these sort of people da kowa da kowa yake iya samunsu... I prefer the fresh and protected ones..."

Roget yayi murmushi sannan yace "Amma dai kasan har a gurin Allah ka fi mu laifi, tunda wayannan su suka kawo kansu, wayancan da kake magana kuma yarda sukai da kai a ƙarshe ka ha'incesu..."

Wata daga cikin matan ta dubi Junior ranta a mutuƙar ɓace tace "That's why I hate you..."

Junior ya zira hannu zai ɗauko wani abu a aljihunsa, sai Roget yayi masa inkiya, sai kawai ya cije leɓe yayi ƙwafa, ya tashi ya nufi mashãya.

★          

Zamu dakata a nan, sai kuma a rubutu na gaba.

Kar ku manta da voting domin a nan muke ganin motsinku tare da comment wanda shi ne farin cikinmu.

Naku, Naseeb Auwal.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now