24

29 2 0
                                    

Duk da yawaitar hayaniya hakan bai hana masu ababen hawa damun mutane da horn ba, ababen hawasun cunkushe kowa yana ƙoƙarin shi lallai sai ya wuce...

Hafsa tana cikin mota tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, sai a lokacin ta gwammace ina ma dai ace driver ta bari ya taho da ita, tabbas ta san da shi ne ya san yanda zai yanke ya bi wata hanyar dabam. Babu abin da idan ta tuno take ƙara tsorata sai abin da ya taɓa faruwa da su ita da mahaifiyarta farkon dawowarsi Nigeria, inda sukai kiciɓus da masu kwacen waya. Duk da dai ita abin da take hangowa shi ne, ba masu kwacen waya ya kamata a kirasu da shi ba, kamata yayi a rinƙa kiransu da ƴan fashin waya, domin a yanda take gani a shafukan yanar gizo, Allah ne kaɗai yasan irin jinin al'umma da suka zubar.

Cunkoson ababen hawan bai fara raguwa ba sai bayan awa guda, Hafsa ta yi ajiyar numfashi tana murna sai kawai taga wasu ƙatti sun tsaya akan motar tata... Jikinta ya fara kakkarwa... "Miƙo wayar nan" cikin ƙatuwar murya babban cikinsu ɗan kimanin shekara ashirin ya faɗa.

Ta zazzaro ido tana kallonsu kwakwalwarta tana lissafa maganar da yayi mata tare da auna labaran da ta ke ji a kafofin yaɗa labarai, game da rasa rayuka da muggan ciwuka da masu fashin wayar suke yiwa mutane...

"Kar ki ɓata mana lokaci mana..." Wani ɗan ƙarami a cikinsu wanda in gari banza ne tsaf zata mangareshi shi ne ya daka mata tsawa, take ta duburburce... Ta sanya hannunta akan ɗaya kujerar tana laluben wayarta, ai kuwa caraf hannunta ya kai kan wayar... Ta miƙa musu... "Cire key ɗin wayar..." Babban ya sake daka maa mata tsaya, kanta ya sara... Ta cire ta miƙa masa... "Ke ina wasa da ke? Ki cireshi gaba ɗaya daga kan wayar, in kuma ba haka ba mu cire na ki kan daga gangar jikinki..."

Kwakwalwarta tai tunanin ta ankarar da zuciyata cewa lallai akwai abin da ake son yi da wayar cikin gaggawa, amma sai tsoron da ke cikin zuciyarta ya hana wannan tunanin haɓaka... Ta cire ta miƙa musu... Babban ya duba ya tabbatar an cire sannan ya kalleta yana murmushi cikin hura hanci ya ci gaba da cewa "Ba kya son bin Yar'adua kenan, kin fi ganewa rayuwa tare da su Goodluck Jonathan sabon shugaban kasarku ko?"

Hafsa ta kasa magana sai gyada kai kawai ta yi, a zuciyarta tana tunanin ashe za a iya yiwa mutum kwace a bainar mutane babu wanda zai kawo ɗauki ko agaji.

Tana tsaye har ta daina ganinsu, a lokacin ne ta ankara wani matashi ya tsaresu yana ƙoƙarin ƙwato mata wayar, tana kallonsu ta madubi, rintse idonta tayi saboda ganin wani sara da akai masa a kafaɗa kamar a film, sannann ƴan fashin wayar suka sulale sula bar titin suka kutsa ta cikin badala suka shige cikin gari.

Sai a lokacin wasu mutane suka fara tasowa wasu suna duba lafiyar wannan matashi da aka jiwa rauni, wasu kuma suna tambayar Hafsa shin yan fashin basu taɓa lafiyarta ba... Ita kuwa haushi ya rufeta, a zuciyarta kuma tana tunanin don me cikin taron mutane irin wannan ita kaɗai za a kwacewa waya?

Da ta ga masu zuwa jaje sun yi yawa sai ta ɗauko gilashi ta sanya ta sha kunu, ta ja motarta tai gaba, zuciyarta kuwa cike da fargaba da baƙin cikin rashin wayarta, ta rinƙa jin kamar ta koma tayi duk mai yiwuwa don ƙwato wayarta, amma da ta tuno sheƙin makaman hannun waƴannan matasa, sai ta ji ta karaya, kuma ta ji lallai gwara da ta miƙa musu wayar domin lafiyarta gaba take da wayar.

Ansar ya mutuƙar jin mamakin ganin wasu hotuna da Hafsa ta turo masa ta whatsApp wayanda sam-sam shigar bata dace da ita ba, hotuna ne birjik ciki harda masu motsi na Hafsan tana rawa tana karkaɗa sassan jikinta, Ansar yana ƙoƙarin kiranta a waya don yi mata magana sai yaga ta goge hotunan gaba ɗaya, daga bisani kuma ta rubuta... Sorry, wrong messages ne, ba kai na yi niyyar turawa ba...

Ansar yayi ajiyar zuciya, idanuwansa cike da kwalla yana tausayawa Hafsa bisa rayuwar da yaga tana ƙoƙarin kefa kanta, a gefe guda kuma yana tausayawa kansa bisa tuno irin son da yake mata da kuma burin iyayensu na lallai sai sun auri juna.

Ya ɗauko wayar ya kirata amma sai aka ƙi ɗagawa, ya sake kira, ya kuma ya ƙara maimaitawa, a ƙarshe sai aka kashe wayar.

Ansar ya haɗa kai da gwiwa ya ji wani irin tiriri yana tashi daga kwanyar kansa, wani tafasashshen mai yana kwarara a zuciyarsa, ya durƙusa yana mai sujjada ga Allah yana zubar da hawaye yana roƙon Allah da ya ganar da Hafsa hanyar gaskiya ya kuma shiryar da ita da bata kariya daga sharrin dukkanin masu sharri. A haka har bacci ya ɗauke shi.

A baccin sai yayi mafarki ga Mahaifinsa Alhaji Nasir yana shafa kan Hafsa wadda take kwance a gadon asibiti ana ƙara mata ruwa... Ansar ya zo kanta ya tsaya yana mata fifita, sai ya ji muficin (abin firfitar) yayi masa nauyi a hannu... Sai kawai yayi jifa da shi, ya koma gefe ya zauna yana haki.
"Amma dai anyi ragon namiji." Babansa marigayi Nasir ya furta... "Ka tashi ka kula da matarka, babu wanda zai amfani gyaruwarta sama da kai, haka nan babu wanda zai cutu da lalacewarta sama da kai..."
"Amma Baba, ai ba matata ba ce." Ansar ya amsa, "Zan iya cewa..."
"Kaiii!" Babansa ya daka masa tsawa, "Lallai-lallai ko za ka rasa rayuwarka wajen bawa wannan yarinyar kariya sai ka yi, ban yarda na sake jin wata magana daga bakinka ba mutuƙar ta ci karo da abin da muka ɗoraka akai, fita ka bani waje..."

Firgigit Ansar ya farka... Duk ya bi ya haɗa gumi.
"Rabbi yassir, ya karim..." Kalmar da ya iya furtawa kenan.

Za mu dakata a nan.
Sai kuma a rubutu na gaba

Tare da ni
Naseeb Auwal

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now