15

32 3 0
                                    

Hazo akan hanya, hazo a sama, hazo a ƙasa, hazo a iska da take kaɗawa.
Ƙura a sama, ƙura a ƙasa, ƙura a jikin gidaje da ababen hawa.
Sanyi a sarari, sanyi a ɗaki, sanyi a cikin jikin da jini yake zagawa.

Wannan duka ya faru ne sakamakon sanyin da ake fama da shi.

Tafe yake yana tunanin hanyar da ya kamata ya bi wadda zata fi zame masa mafi sauri, kuma mafi ƙarancin cunkoso. Kasancewar sa sabon matuƙin babur bai cika son bin hanyar da take da cunkoso ba.

Sabon babur ne wanda babansu Hafsa ya bashi, tare da cewa da farko mota ya bashi amma Alhaji Nasir ya tubure cewa ba za a bashi mota ba, a ƙarshe dai babur ɗin ma da ƙyar Alhaji Nasir ya barshi ya karɓa.

Haka ya ci gaba da tafiya sanyi yana ratsa sassan jikinsa, musamman kuma bai saka irin kayan sanyin da kowa yake sakawa ba. Hasalima dai rigar daya saka rigar yan ball ce ƙirar ƙungiyar ƙwallon ƙafan Real Madrid.

Tun yana hanya yaji anata kiransa, a waya amma sai kawai ya ƙyale da zummar cewa idan ya ƙarasa gida sai ya duba yaga wanda ya kira shi.

Kafin ya koma gidan man sai ya tsaya don yasha mai, ya manta shaf da wancan kira da ake tayi masa. Sai da yaga wani ɗan lukutin mutum yana waya yana ta rantse-rantse cewa yana kan hanya sannan ya tuno. Ai kuwa nan take ya zira hannunsa aljihun wandonsa ya zaro wayar.

Gani yayi ƙanwarsa khadija ce ta kirashi. Ba shiri kuwa ya bi kiran nata.
Ta ɗaga wayar tayi shiru tana jiran yayi sallama. Shi ma kuma jira yake tayi sallamar.
"Asslaam Alaikum" Ansar ya fara bisa fahimtar abin da take nufi. Tunda shi ne ya kira to shi ne mafi cancanta da ya fara yi mata sallama, domin shine sama da ita, kamar yadda ƙa'idar sallama ta nuna, babba shi zai yiwa yaro sallama, na kan abin hawa shi zai yiwa wanda yake ƙasa sallama, mai tafiya zai yiwa na zaune sallama. To mai kira a waya ma shi zai yiwa wanda ya kira sallama.
"Wa'alaikum Salaam..." Ta amsa da alama tana cikin tashin hankali domin muryarta ma rawa take.
"Lafiya?!" Ansar ya tambaya a firgice.
"Eh... Amma dai... Amma kaga... Subhanallah..." Tana maganar kuka yana sarƙe ta.
"Khadija kiyi magana don Allah, lafiya kuwa?" Ya sake tambaya a wannan karon.
"Baba ne... Bai da lafiya... Sai suma yake, na kiraka ɗazu baka ɗauka ba amma dai mama ta kirawa liman sun tafi asibiti da shi, suna asibitin murtala... Wai emergency."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ansar ya faɗa lokacin da yake katse wayar.

Ko man bai tsaya ya sha ba, sai kawai ya nufi asibitin da wani masifaffen gudu, saboda tsabar gigicewa ma ba hannunsa ya biba, wani hannun yafi dabam, yana gudu a wannan babur yana kaucewa ababen hawa masu tahowa kamar a film.

Duk inda ya wuce sai kaga kawai an bishi da kallo.

Yana gab da zuwa asibitin ne wani cunkosan ababen hawa ya tsare shi, ai kuwa sai ya yarda babur ɗin a tsakiyar titi ya cigaba da gudu akan duga-dugansa. Gudu yake matsananci kamar ransa zai fita, duk wannan sanyi da ake ya daina jinsa. Bai tsaya ba sai da ya ƙarasa asibitin yana zuwa akace yayi haƙuri ya tsaya. Ana wasu aikace-aikace a cikin ɗakin marasa lafiyar.

Shi kuwa can Alhaji Nasir bayan yan allurori da akai masa, sai wannan suman da yake ya tsagaita.

"Allah kasa wannan raɗaɗin ciwo da nake ji ya zamar min kaffara, ta yanda zan koma ga mahalicci na bani da laifi ko na sisin kobo, Juwaira, nasan rayuwata tazo ƙarshe don haka ina mai umartarki da kici gaba da kula da kanki da yaran nan..." Tari ya sarƙe shi.

A daidai lokacin ne wani mai duba marasa lafiyar ya shigo tare da wata takarda a hannunsa, daga bisani yace "Aje a siyo wayannan sai dai akwai tsada gaskiya kayan zasu iya kaiwa dubu talatin..."

Hajiya Juwaira tace "Babu komai ai lafiyar gaba take da komai, ta buɗe jakarta tana ƙoƙarin ƙirgo kuɗin."

"Ba ni zaki bawa ba," mutumin ya faɗa yana murmushi. "wajen siyar da magani zaki je ki basu, amma ki fara zuwa inda za a gaya miki nawa ne." Bai jira taba ya fice.

Ta juya zata fita sai kawai Alhaji Nasir ya riƙo hannunta yayi mata inkiya da tayo ƙasa da kanta, ai kuwa tayi kamar yadda tace, ya sumbaceta a goshi, sannan ya dafa kan nata yana shafawa gami da yi mata addu'ar albarka. "Kada kiyi asarar kuɗinki, tabbas lokacin tafiyata yayi, ki gaggauta kirawo min Ansar, akwai muhimmin abin da nake so na gaya masa... Bani da lokuta da yawa kiyi maza ki kirashi yana baƙin ƙofar wannan baƙin ɗaki mai cike da zaluncin wannan baƙar nahiya ta baƙaƙen fata... Nace kiyi maza ina son in ganshi."

Ai kuwa Juwaira ko hijabi bata saka ba saboda firgici haka ta nufi hanyar.

Alhaji Nasir ya bugi gadon da yake kwance da ƙafarsa kasancewar muryarsa bata fita sosai, Juwairiyya ta juyo ta kalleshi, sai kawai yayi mata inkiya da ta sanya hijabi. Ai kuwa nan take ta saka. Ta fice kuma a gaggauce.

Taje wajen mai gadin ƙofar ta nemi alfarmar cewa mara lafiya yana son yaga ɗansa, da fari mai tsaron ƙofar yayi mata gardama sai kawai ta zube ta riƙe ƙafafuwansa tana mai fashewa da kuka, shi kansa abin ya ratsa zuciyarsa duk da cewar matashi ne kuma kana ganinsa kasan yana shaye-shaye domin bakin nan yayi baƙiƙƙirin idon yayi jajur.

Wannan matashi ya sanya hannu ya taso ta, yana mai zubar sa hawaye. Ya buɗe ƙofar.
Juwairiyya tana leƙawa Ansar ya mike yana mai dafe ƙirjinsa ya taho da sauri.
"Mama lafiya? Jikin ne dai har yanzu?" Shima a wannan lokacin idanuwansa zubar da ƙwalla suke.

Ba tace masa komai ba, sai kawai ta kama hannunsa ta jashi zuwa cikin ɗakin inda gadon da aka kwantar da mai gidan nata yake.

Suna zuwa suka tarar idanuwansa suna kallon sama ko ƙiftawa baya yi.

"As.. As.. Assalam A..a..alaikum..." Ansar ya faɗa cikin kakkarwa da rawar murya.
"Wa alaikum salaam," Alhaji Nasir ya amsa sama sama. Yayiwa Ansar inkiya, ya sakko da ƙansa dai dai kan nasa. Alhaji Nasir yayi gyaran murya a hankali saboda baida kuzari.

"Ina baka haƙuri bisa rashin tara dukiya don ku gaje ta, amma ina alfahari da irin tarbiyyar da kuke da ita, tabbas nasan ko bayan mutuwata abubuwan alherinku zasu rinƙa riskata kuma su sanyani farin ciki sosai. Ka kula da Khadija ƙanwarka, ka tabbatar ka damƙata ga hannun miji nagari, sannan ka kula da Hafsa domin haƙiƙa amanace ita a gareka, idan har ka kuskura ka barta ta fanɗare to tabbas zakai mafi girman da na sani... Ka kula da addininka, karka sake wani dalili yasa kayi shirka..." Tari ya sake sarƙe Alhaji Nasir.
Yaci gaba da cewa "Ka riƙe khadija da mamanta da kuma Hafsa amana... Nayi imani kuma na shaida babu abin bautawa sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne..."

A dai dai wannan lokacin idanuwansa suka ƙafe suna kallon sama.

Zamu dakata nana
Sai kuma a rubutu na gaba.

Zamu dakata nanaSai kuma a rubutu na gaba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now