5

73 6 4
                                    

Tun a hanya Ansar yake ta tunani kala kala, babu abin da yafi tayar masa da hankali sama da yanayin da yaga wannan yarinya Hafsa, tunani ya rinƙa kaikawo a ƙwaƙwalwarsa akan irin yadda iyayen Hafsa suka cusa mata tunani da soyayyar abin da bata taɓa gani ba... Tabbas duk abin da iyaye suka so ɗora ɗansu akai to tabbas indai sun biyo hanyar da ta dace zata sada su ga abin da suke so wannan ɗan nasu ya zamo...

Har ya hau abin hawa bai daina wannan tunanin ba, yana tsaka da tunani kawai sai ji yayi an daka masa tsawa, ɗagowar da zaiyi sai yaga wasu matasa ne su uku biyu sun tsaya a gaban keke napep ɗin daya hau, yayin da ɗaya yazo bakin ƙofar abin hawan ya tsaya yana muzurai da jajayen idanuwansa.

"Ahh! Black, kana duniyar dama?"
Ansar ya faɗa yana dariya gami da miƙawa matashin hannu.
Matashin ya kalli Ansar cikin alamun mamaki da alama tunani yake ko yasan Ansar ko bai sanshi ba...
Ansar ya katse tunanin matashin ya ɗora da cewa "Ina abokinka dogo? Ai dogo baida mutunchi, ko jiya saida nayi juyin duniya ya kawoni gidanku saboda wannan harƙallar amma mutuminka sai yace shi so yake kawai kayan nan indai an tabbatar an sauke komai na kansu kawai a bashi, wai ya fika sanin kan sabgar..."

"Kut..." Matashin ya saki wata ashariya, "Lallai dogo babu amana a tsakaninmu, kasan rabona da shi tunda muka shiga cell? Kawai dai yanzu kaga operation muka fito, mu haɗu an jima a majalisa ta bayan kududdufi sai mu tattauna, koya kace?"
Matashin ya faɗa yana wani tutturo baki gami da janye jikinsa daga jikin abin hawan.

Driver yayi maza yaja abin hawan sukai gaba.
"Da ace baka sanshi ba, da babu abin da zai hana su zubar da jini, da kuma yi maka kwace..." Driver ya faɗa.

"Ban sanshi ba, kawai dai nayi masa yan dabaru ne, wasu lokutan dabara kawai muke buƙata don tseratar da rayuwarmu da gangar jikinmu" Ansar ya faɗa yana murmushi. Mamaki ya kama direban, a zuciyarsa yana jinjina hikimar Ansar.

Haka suka ci gaba da tafiya, titin duk ya lalace, jefi-jefi kuma zaka tarar an zubda shara tayi tsiri a gefen titin maimakon a samar mata da wajen da ya dace. Ga ruwan kwatami da yake ƙoƙarin fitowa ya gangaro kan kwaltar sabo da rashin samun ingantacciyar hanya. A hakan zaka iske wani ƙaton ya kwaɓe wandonsa a gefen titi yana fitsari... Wani lokacin haka zaka ga har a cikin mata masu talla akwai masu juriyar kwabe wando don biyan buƙatarsu a gefen hanya, ba tare da sunyi tsarki da ruwa ba, kuma a hakan zaka ga sun dawo kan kayansu yayin da wani zai zo siyar abu kuma su sanya wannan ƙazantaccen hannun su ɗebi abin da mutum yake so su bashi.

Ƙarar horn ɗin motoci da sauran ababen hawa itace abin da zaka fi ji, sai ƙarar hayaniyar mutane wanda lokaci zuwa lokaci zakaji wani matashi don an samu kuskuren tuƙi yana narkawa wani dattijon ashariya son ransa, dattijon da a haife ya haifeshi.

Bayan gajeriyar tafiya Ansar ya ƙarasa inda yake son zuwa, wato gidansu. Bayan ya sallami mai abin hawan ne sai kuma ya juya don shiga gida. Yaci sa'a kuwa mahaifinsa yana soro kamar yanda ya saba zama koda yaushe.

Ansar ya tsaya ya cire takalmansa, sannan yayi sallama, ya ɗan jinkirta, Alhaji Nasir yayi masa inkiya cewa ya shigo, cikin nutsuwa ya sanya ƙafarsa ta dama ya shiga, kai tsaye yaje gaban mahaifinsa ya zauna, ya zira hannu a aljihu ya ɗakko rafar dubu har guda uku miƙawa Alhaji Nasir...

Wani kallo da mahaifin nasa yayi masa yasa shi da kansa yaji cewa yayi laifi.

"Don me zaka zo min da kuɗin ƙazanta? Dama baka da hankali?"
Alhaji Nasir ne ya faɗa cikin faɗa.

"Ba haka bane" Ansar ya fara bayani. "Abokinka Alhaji Sambo ɗan kasuwa ne, kuma wannan kuɗin baida alaƙa da amintakarsa da yan siyasa... Baba wallahi har a wajen Allah zan shaidi Alhaji Sambo bazai taɓa irin muggan laifukan da kake raya cewa yana aikatawa ba..."

Alhaji Nasir kawai ya tsaya yana kallon Ansar, yana tunanin kalmomin da yake furtawa. Koda wasa Ansar bai taɓa yi masa magana haka kai tsaye ba, sauda dama yakanyi dana sanin yiwa Ansar faɗa, domin mafi yawan lokuta Ansar ba mai laifi bane, kawai mahaifin nasa ne ya kasa fahimtar wani abu. Sai kuma bayan gaskiyar abin ta bayyana a gareshi sai ya dawo ya bashi haƙuri, wani lokacin ma har yakan ji haushin Ansar akan don me yasan ba shi ne yayi laifi ba amma zai tsaya ayita yi masa faɗa akan laifin da bai aikata ba... Shi kuwa Ansar sai dai yayi murmushi kawai sannan yace "Babu kyau jayayya da iyaye..."

Alhaji Nasir ya kalli Ansar wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, sannan yayi ajiyar zuciya daga bisani yace "Zuciyata ba zata nutsu da wannan kuɗi ba, ka kaisu ga mahaifiyarka, tunda ku kun gamsu da halaccin kuɗin amma ni dai kada ku kawo min koda ruwa da kuka sarrafa da wannan kuɗin..."

Duk da mahaifin Ansar ne, amma Ansar yaji babu daɗi, a zuciyarsa kuwa ya rinƙa zargin mahaifinsa da tsaurarawa da yawa...

"Bakaji me nace ba?"
Alhaji Nasir ya faɗa wannan karon da ɗaga murya.

Ansar ya amsa sannan ya miƙe ya shiga gidan yana riƙe da kuɗin.

★ ★ ★
Tun da Ansar ya fice yabar Hafsa a tsaye bata motsa ba har kusan tsawon minti goma sha biyar, kawai ta tsaya tana kallon ƙofar daya bi ya fice, haka ta wanzu kafin daga bisani taji an daka mata tsawa.

"What the hell are you doing here?"
Muryar mamanta Hajiya Sadiya ta katseta daga tunanin da take...

Ta juyo idonta cike da kwalla, ta kalli maman tata, abin da maman ta gani ya baya mamaki...

"Me nake gani haka? Waya taɓa min ke?
"Mom, nobody but you and Dad."
"O my God, garin yaya?"
"You put something fiction into my life, kuma kun gina rayuwata a kansa, dama tunda na sauka a Nigeria naga alamar duk abin da ake gaya min ba haka bane, tun daga kan riƙo da addininsu da tarbiyyarsu na gane kawai zugugu ne irin naku... Ina riƙon addini a wajen mutanen da basu san haƙƙin ɗan'adam ba? Ina riƙon addini a wajen mutanen da basu san hatsarin dake cikin zubar da jini ba? Shin akwai sauran imani a wajen mutanen da akan abin duniya zasu iya salwantar da rayuwar mutum? Shin kun bani labarin duka wayannan halaye na mutanen wannan ƙasar? Ashe Nigeria ɗin da kuke bani labari ƙirƙirarku ce? Ashe yaya Ansar bai ma san da ni ba? Tana gama faɗin haka kawai sai ta fashe da kuka. Ta cilla fuskarta kan kafaɗar mahaifiyarta.

Mahaifiyarta ta kalleta, tana mai wani gajeran murmushi don bawa yar tata kwarin gwiwa, daga bisani ta jata wata kujera mafi kusa dasu ta zaunar da ƴar tata, sannan ta kwantar da kan ƴartata akan cinyarta tana mai goge mata hawayen dake zuba daga idanunta, sannan ta kalli ƴar tata, tana mai ci gaba da wannan murmushi sannan tace da ita, "Kowane tsuntsu kukun gidansa yake, don haka kamar yanda nan suke da nasu laifukan haka inda muka baro suke da nasu laifukan. Sai dai kice rashin tsarin nan ya sanya abin yafi lalacewa fiye da inda muka baro, kuma Ansar ɗinki yana sane, har yanzu yana miki kallon yarinya shiyasa baya so ki sanya kanki a damuwa, domin har yanzu lokacin da zai fara nuna miki soyayyarsa bai zo ba..."

"As you said, kowane tsuntsu kukan gidansa yake, don haka nima sai a ƙyaleni inyi kukan nawa gida..." Cewar Hafsa.

"Okay to ɗauke kanki daga cinyata, sai in baki waje kiyita kukan" mamanta ta faɗa tana murmushi.
"No mom, I mean, yanda kuke soyayyarku kuda daddy bance kun tsufa ba, ya kamata nima ku barni in fara soyayya ni da Yayana kada kuce nayi ƙanƙanta... Wane girma ne kuma ya rage min?" Hafsa ta faɗa cikin yanayi na alamar da gaske take.

"Za'ace baki da kunya, kina wannan maganar a gabana, lallai baki da kunyar ma" mamanta ta faɗa.

Hafsa tana kwance akan cinyar maman tata sai kawai ta yatsine fuska ta kifa fuskarta akan cinyar mamanta har bacci ya ɗauketa.

Zamu yada zango anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Mun gode!

Comment da votes suna jiranku...

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now