12

45 5 0
                                    

Fili ne fatal iyakar ganin mutum, baka iya ganin komai iyakar ganinka sai ciyaye wayanda iska ta tilasta musu yin rangaji, ilahirin sararin samaniya yayi baƙiƙƙirin sakamakon hadarin daya mamaye ta, jefi-jefi kuma walƙiya tana haskawa game da tsawa mai tsananin rikitarwa...

Ansar ne a tsaye yana nazartar wannan fili wanda idan ka ɗauke Ansar babu abin da ya kai koda ƙugunsa a tsayi cikin ilahirin wannan fili.

A hankali sai wasu ƙananun bishiyu suka fara fitowa suna girma da bunƙasa.

"Ansar... Ansar... Ansar..."
Sautin da Ansar yaji kenan ana kiransa cikin ƙasa da murya. Take Ansar ya hau waige-waige don ganin wanda ke kiransa, amma babu alamar akwai wata dabba a wannan filin in dai ba tsirrai ba. Bugun zuciyarsa ya ƙaru yayin da tunani ya rinƙa ambaliya yana cakuɗewa a cikin ƙwaƙwalwarsa.

"Ka taimake ni, Yaya Ansar zan mutu..."
A wannan lokaci muryar Hafsa yaji cikin shashshekar kuka. Na take ya nufi inda yake jiyo amsa amon sheshshekar kukan cikin matsanancin gudu tamkar ƙafafuwan sa zasu fita.

Daga nesa da shi yana hangota ana janta a ƙasa kan wayannan ciyayi, yayin da jikinta yake ɗaɗɗaure, farar rigar da ta saka kuwa ta ɓaci da jini, gashin kanta ya bazu, har ya rufe fuskarta ma baki ɗaya...

Nan take Ansar ya ƙara himma wajen wannan gudu da yake. Har a wannan lokaci ana tsawa da walƙiya da kuma wata dariya da yake ji anayi cikin wata ƙatuwar murya, a sannan ne ya fara hango wani mutum wanda ke tafe akan doki yana riƙe da sarƙar da aka ɗaure Hafsa da ita yana gudu yana janta a ƙasa, ita kuwa sabo da wahala ko ihu bata iyawa.

Ansar ya ƙara himma wajen wannan gudu da yake, yana kaucewa bishiyun da har yanzu suna tsirowa daga wannan fili.

Ɓat, sai yaga Hafsa da mutumin da yake janta a ƙasa sun ɓace, amma duk da haka bai daina jin wannan sheshshekar kukan ba, yayi yunƙurin buɗe baki yayi magana amma sai kawai yaji bakin yayi nauyi ya kasa buɗewa.

Sai kawai ji yayi an ƙwalla masa kira cikin wani yanayi mai firgitawa, yana waigawa sai kawai yaga Hafsa tana kokawa da wannan mutumin mai janta wanda har yanzu Ansar bai iya ganin fuskarsa ba...

Cikin zafin nama Ansar ya daka uban tsalle da nufin turmushe wannan mutumin amma sai mutumin ya ɓace tare da Hafsa.

Ansar ya faɗi ƙasa ya turmusu cikin ciyayi. Yana kwancen duk ya daddauje, sai kawai yaji ana ƙyalƙyalewa da dariya a sararin samaniya. A fusace ya ɗaga kansa, sai yaga wannan mutumin sanye da malafa ta yanda fuskarsa ba zata ganu ba.

Mutumin ya ƙyalƙyale da dariya, kafin Ansar yayi wani yunƙuri yaga mutumin ya ɓace, sannan kuma hafsa tayo ƙasa zata faɗo, faɗowar da ya tabbata idan ta faɗo sai dai wata ba ita ba. Take ya miƙe don zuwa ya taro ta, amma sai kawai yaga waƴannan ciyayin sun ɗaɗɗaure shi... Yayi kici-kicin amma ya kasa ƙwacewa ai kuwa sai kawai ya ƙwallawa Hafsa kira.
"Hafsaaaaaa!"

Firgigit ya farka daga baccin da yake, duka yan ajin yaga sun juya suna kallonsa wasu kuma suna ta ƙyalƙyala dariya, malami kuma da yake tsaka da yin lecture sai kawai abin ya fusata shi ya tattara kayansa ya bar ajin.

Sabo da kunya sai kawai Ansar ya sunkuyar da kansa ƙasa.

"Baka da lafiya ne?" Maryam ta matso kusa da shi tana mai tambayarsa.
"Babu komai..." Ansar ya bada amsa.
"Ya zaka ce babu komai?"
"Kinga malama kawai ki tafi ki ƙyale ni."

Wasu daga cikin yan ajin suka zo suna masa sannu, wasu kuma wayanda suke wayayyu sai sukai shiru akaci gaba da mu'amala kamar yanda aka saba.

Bayan kamar minti ashirin da faruwar wannan lamari sai ga Hafsa ta shigo ajin, to da yake akwai wayanda suka santa a ajin da kuma yanda suke da Ansar sai akai tsit a ajin duk idanuwa suka koma kanta.

Hafsa tazo ta zauna a wajen da aka tanada don aje littafai ayi rubutu yayin da shi kuma Ansar yake zaune akan mazaunin, kusa da shi kuma Maryam ce.

"Sannunki," Hafsa ta faɗawa Maryam tana murmushi, a zuciyarta kuwa ita tasan irin haushin Maryam da take ji
"Yawwa Aunty Hafsa."
Hafsa ba tare da ta ƙara yiwa Maryam magana ba sai kawai ta fuskanci Ansar tace "Ina ajinmu ake min magana ta WhatsApp, hope you are okay... Ance kana wani abu kamar farfaɗiya kuma sunana kawai kaketa kira..."
"A'a bacci yake, kawai dai ya farka ne yana ƙwalla miki kira, may be yayi wani mummunan mafarki." Maryam ta bawa Hafsa ingantacciyar magana.
"Malama da kinyi haƙuri naji daga gare shi." Hafsa ta ambata tana murmushin ƙeta, sannan ta sake mai da idonta kan Ansar tace "haka ne?".
"Maryam ta gama gaya miki komai fa." Ansar ya faɗa yana mai kawar da kai da kallon gefe.

Maganar ta yiwa Maryam daɗi sosai amma a wajen Hafsa ji tayi kamar ya zuba mata garwashi a zuciyarta.

'Shin har tana da darajar da zai iya rufe ido idan nayi mata abu ya kareta?' Hafsa ta tambayi kanta da kanta a zuciya.

"Babu mamaki idan hakan ya faru," Ansar ya ci gaba da magana "Sabo da abin da kake so koda yaushe kana ƙoƙarin bashi kariya ne, kema kariyar nake baki shi yasa na ambaci sunanki don rashin samun damar ceton ki daga faɗowa daga sama."

Maganar saita ɗorewa Hafsa kai, shin labarin mafarkin yake bata, ko kuwa farkon maganar yana bata amsar tunanin da tayi a zuci ne? Tabbas dai ita bata san meke damunta ba, don zuciyarta tana mata abubuwa kala kala wannan lokutan. Ko kuwa itama zuciyar ta zama yar nigeria ne oho.

"Maryam, Nagode da kulawar da kika bawa yayana kuma masoyina kafin inzo, ga wannan kawai na baki ba don komai ba sai don kulawar da kika ba shi." Hafsa ta faɗa lokacin da take zaro yan dubu gudu goma miƙaƙƙu tana miƙawa maryam.

"Haba dai, ai yiwa kaine." Maryam ta faɗa lokacin da take miƙewa tana barin wajen kuɗin kuma ta barsu a hannun Hafsah.

Hafsa tayi murmushin farin ciki saboda dama tasan haka kawai zatai Maryam ta tafi ta basu waje.
Duk ɗaukacin ɗaliban da suke ajin babu wanda ya shigar mata zuciya ya tsaya mata a zuciya sai Maryam kawai.

Wayar Hafsa tayi ƙara, sai kawai ta ɗauko, dubawar da zatai sai taga saƙo ne Junior ya turo mata.

Akwai taron walima da zamuyi da misalin ƙarfe huɗu a perfection republic fatan zaki samu halarta.

Hafsa tayi murmushi ta tura masa alamar murmushi.

"Wanene ya sakaki murmushi haka?"
Ansar ya tambaya.
"Mom ce, tace wai ƙarfe huɗu zan rakata wata walima can perfect republic... Kaga da walimar harda maza da da kai zamu je."
"Ku dawo lafiya."
"Ameen"

Hafsa ta faɗa dai dai lokacin da take mikewa don tafiya, ta juyo tana masa murmushi bai ankara ba sai kawai yaji ta sumbaceshi a goshi sannan ta juya ta fice daga ajin.

Ansar ya dafe goshinsa yana mai zazzaro ido cike da alamar tambaya.

"She is still mad!" Ya fada...

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Sai kuma a rubutu na gaba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now