17

34 4 0
                                    

Tun bayan da Hafsa tabar cafeteria ɗin take ta tunani a zuciyarta akan abin da ya wakana tsakanin ta da Junior, tabbas tasan bai kyauta ba, amma sai ta tsinci zuciyar ta tana bashi uzurai akan kuskuren da ya aikata.

Kanta yayi mata nauyi kamar an aza mata gammo, jin ta take ta tsani kowa a zuciyar ta kuwa tana jin cewa dukkanin maza kamar guba suke, kowanne yana da ɗanɗanonsa, wani mai zaƙi, wani mai ɗaci, wani mai bauri, wani mai tsami sai dai kowanne a ƙarshe cutar da ke zai yi a sanda kika sha shi... Ƙwaƙwalwar ta ta jefo mata tambaya 'anya akwai namijin da baya cutarwa ko kuwa sai dai wani yafi wani?' tambayar da ita kanta ta kasa bawa kanta amsa.

★         ★          ★

Ansar kuwa a wannan rana ya shiga makaranta sai dai ya bawa mutane mamaki, domin tun daga mutanen unguwarsu mamakin ya fara, a saninsu tun da akai masa rasuwa ba a ƙara ganin dariyarsa ba, amma yau an ganshi ya fito faran faran yana gaisawa da jama'a.

Duk inda ya wuce sai kaga ya ɗaga musu hannu yana mai dunƙule hannun irin yadda ake gaishe da sarakai domin itace irin wadda ta tabbata a musulunci bawai gaisuwar ɗaga hannu ana baza yan yatsu ba.

Haka ya ci gaba da tafiya, yana bin hanya, wadda geffenta guda biyu kwatoci ne wayanda aka tanada don wucewar ruwa amma sai ka rantse an tanade sune don tara ledoji da tsummokara, hanyar a kwaltace take da wata gajiyayyiyar kwalta wadda tafiyar yan sakanni kaɗan zaka rinƙa cin karo da ramuka wayanda sai ka rantse ado aka ɗauke su domin gwabnati babu ruwan ta da gyaransu. A hakan wasu masu kishin unguwa zasu zo su share kwatamin dake geffan hanyar, maimakon sukai sharar inda aka tanada ko kuma su sanar da gwabnati gami da sharar sai kawai su bajeta a wannan titi da sunan suna yiwa titin ciko, wanda bayan wani lokaci wannan sharar zata bi iska ta lallaɓa ta sake antayawa cikin wannan kwatami da aka rabata da shi.

Tare da rashin kyan wannan hanyar amma mabiyanta kowannensu zaka iske cikin gaggawa yake, wanda hakan ke haifar da yawaitar hatsari a hanyar.

A haka har Ansar ya ƙarasa wani gareji, inda yana shiga mai gyaran babura a garejin ya taso da sauri suka cafke da Ansar.

"Injiniya, nazo karɓar babur ɗina yau." Ansar ya furta lokacin da yake murmushi.
"Allah sarki mutumina, ka ganshi can, sai dai fa na ɗan hahhaushi ba tare da neman izini ba."
"Ba komai, gwara da ka hau ai, kaga bana buƙatar in jira a sake masa service yanzu."
Ansar ya faɗa lokacin da yake ɗauko kuɗi daga aljihunsa yana damƙawa mai gyaran. Yaƙi karɓa amma Ansar sai ya cusa masa a aljihu ya karɓi maƙullin babur ɗinsa yayi masa key baburin ya karɓa sannan Ansar ga tuƙa shi ya hau kan titi ya nufi makaranta.

Yana tuƙin cikin kula da kuma ɗaga ƙafa, haka har cikin kiyayewar Allah ya ƙaraso makaranta.

Sai da ya mallaki abin hawa sannan ya yarda da abin da ake cewa, cewar a kano kana tuƙinka kana yiwa wasu. Domin wasu basu san dokar tuƙin ba, babu irin ma masu haya wayan da suna tsakiyar titi da sunga fasinja zasu gangaro ɓangaren da yake ba don komai ba sai don kawai su ɗauke shi.

Bayan Ansar ya shiga makaranta ne sunyi karatu na farko bai tsaya jira ba ya miƙe ya tafi zuwa ga inda yake kyautata zaton zai ga Hafsa, babban tunanin sa shi ne zai iya ganin Hafsa a inda suke lecture don haka can ya nufa.

Yaje ya duba bai ganta ba, yana tsaye yana lalube lalube sai kawai wata budurwa ta nufo shi, tana zuwa ta ɗan risina kaɗan tace "Yaya Ansar ina kwana!"
"Lafiya lau." Ansar ya amsa cikin fara'a kamar ya san ta.
"Ƙanwar ka Hafsa kake nema ne?"
"Eh."
"Kaje cafeteria yanzu a can take zama, muma ƙawayen ta mun mata magana saboda da yawan ma su zama a wajen ba mutanen kirki bane amma  ita idonta ya rufe..."
"Okay, na gode." Ansar ya faɗa yana mai ƙara himma wajen fuskantar hanya mafi sauri don isar inda aka sanar da shi.

Tun kafin ya ƙarasa ya fara jiyo tashin kiɗa, ya ci gaba da kusantar wajen shigar sa keda wuya ƙamshin abinci ya daki hancinsa, amma sai kawai ya basar ya fara lalube fuskokin mutanen da suke cikin wannan cafeteria. Kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya yayin da su kuma suke gudanar da al'amuran su babu ma wanda ya damu da wani ne ya shigo.

Abubuwan da ya gani ya sanya kansa yayi nauyi, gefe guda akan wata ƙatuwar kujera mai faɗi tamkar gadon kwanciya maza da mata ne a kishingiɗe suna hira a cakuɗe. Daga gefe kuma wata ya gani akan cinyar wani ƙato suna kallo a waya, wata kuwa wani ya gani yana manne da ita a jikin bango kai kace zai shige cikin jikinta. Sai dai kaf cikin waƴanda yake dubawar har yanzu baiga Hafsa ba. Ya ci gaba da dubawa amma bai ganta ba, sai kawai ya juya zai tafi.

Juyawar da zai yi sai kawai yaji an damƙo shi ta ƙeya an jijjigashi anyi jifa da shi kan wani teburin abinci wanda ke zagaye da wasu mata suna cin abinci. Ya faɗa kan teburin nan, abincin ya baje a dandaryar wajen sannan ya ɓata masa kaya da kayan mutanen da suke kewaye da wannan tebur ɗin. Tabbas Ansar ya bugu matuƙa, amma sai kawai ya miƙe, yana mai karkaɗe jikinsa, bisa ga mamakinsa sai yaji sai ƙyalƙyala dariya ake, kuma ana nuna shi.

Abin ya mutuƙar ƙona masa rai, amma sai kawai ya kama hanyar fita. Yana sanya ƙafarsa a waje yaji an ƙara tankaɗashi ya tafi kamar zai faɗi, amma dai Allah ya kiyaye shi. Ya juyo a fusace don ganin wanene amma bisa ga mamakinsa bai ga kowa ba.

Ya ɗanyi jim kamar ya koma cikin inda ya baro ya sanya tafka, amma hakan bai da wata fa'ida don haka sai kawai ya basar yana fara tafiya sai kawai suka ci karo da Hafsa. Yana murmushi ya nufe ta, amma sai yaga ita ta ɗaure fuska. Suka zo gab da gab ya kira sunanta amma sai kawai ta ɗauko waya wadda a dai dai wannan lokacin an kirata ta ɗaga kiran ba tare da ta kula Ansar ba, ta barshi a tsaye yana kallon ta cike da mamaki lokacin da take shiga cikin cafeteria da ya baro.

Sai kawai ya juya da zummar ya bita, abin da ya gani shi ne ya dakatar da shi. Ganinta yayi tana gaisawa da maza suna masayar bada hannu musafaha.

Zamu dakata anan.
Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now