20

47 5 3
                                    

An wayi gari da sabon yanayi, kowa ka duba yanayinsa babu hayaniya, mutane sunata hada-hada yayin da wasu suke rakaɓe a inuwa suna masu gudarwa rana wadda ta ƙwalle sosai tana mintsinin fatocin wayanda suke cikinta tare da zagewa wajen ganin ta dafar da kayan da basa son haskenta.

An wayi gari da azumi. Ɗaiɗaikun mutane wayanda ba zaka iya cewa ga adadinsu ba kuwa basa azumi saboda cewarsu su ba su ga wata ba. Basu bi sanarwa sarkin musulmi ta cewa tabbas anga wata ba.

Ansar yana tafe yana tunanin watan azumi da ya gabata a waccan shekarar tare da mahaifinsa suke siyayya, har ya rinƙa ƙoƙarin cewa mahaifin nasa ya kamata ya rage rabon kayan abincin da yake yi domin shima fa basu wadaceshi a gida ba.

"Idan ban ciyar ba yanzu yaushe zan ciyar? Kana da tabbacin zan kai wani azumin ne? Kuma idan na ƙaddara cewa wayanda suka fini arziki su za su yi sadaka da kyauta suma haka zasu ƙaddara cewa na samansu ne za su yi, suma kuma su ƙaddara cewa haƙƙin gwabnati ne, ita kuma gwabnati taga cewa lallai abubuwa sun mata yawa... A haka sai kaga an rasa alheri mai yawa. Amma idan aka ce nina fitar, na samana zai ga cewa lallai shi ne yafi cancanta da ya fitar da kyauta, shima na samansa zai ga lallai shima ya kamata yayi, gwabnati kuma zata ga cewa abin kunya ne ɗaiɗaikun mutane suna aikata abu amma ita ta kasa..."
Ansar ya gama tuno wannan furuci na mahaifinsa, ya share ƙwallar da take idanunsa.

Ya cigaba da tafiya yana tura baburinsa don ajiye shi a inda aka tanada don ajiye babura. Yana tafe da ƙyar domin kuwa ji yake kamar zai faɗi.

Ya hangi wani waje mutane sunyi cincirindo anata rabon abinci ana make wasu, wasu kuma sun karɓa amma sai a bisu a fizge, idan mutum yayi gardama ma har a fitar masa da jini.
‘Irin wannan masu kuɗin bai dace su rinƙa irin wannan sadakar ba, me zai hana su sanya abi gidajen mabuƙatan a raba? Wani yana da buƙata amma ba zai taɓa zuwa irin wajen nan ba...’.

Haka ya kafe babur ɗinsa aka bashi takardar shaidar ɗaukar babur ɗin sannan ya kutsa cikin kasuwar.

Yana tafe yana nazartar kayan gami da taya wayanda sukai masa, idan ya taya sau ɗaya yaji farashin bai masa ba sai kawai yayi gaba, wasu yan kasuwar sukan ƙwalla masa kira akan cewa ya dawo gaskiyar abin naira kaza ne, sai dai baya dawowa inka ɗauke lokacin da yaga wani agogo ya taya aka gaya masa kuɗin, bayan yayi gaba sai mai agogon ya kira shi yace ɗan beauty, saboda agogon zai yiwa wadda zaka siyawa kyau yanzu na rage maka ɗaya bisa uku na kuɗin. Ai kuwa sai Ansar ya dawo ya siya ya kama hanyar komawa gida.

Yaje inda ya ajiye babur ya miƙa takarda bisa ga mamakinsa babu babur ɗinsa babu alamarsa, ya juyo a firgice ya kalli mai ajiyar ababen hawan zai magana amma sai mai ababen hawan ya bushe da dariya yace "Mallam kayi haƙuri... sorry Alhaji nake son cewa... Babur ɗinka baya nan..." Har yanzu dariya mai ajiyar yake, abin ya bawa Ansar mamaki, sun ɓatar masa da babur kuma suna masa dariya.

"Kaga inda na mayar maka da shi saboda nasan ba daɗewa zakai ba." Mai ajiyar ya kammala maganar yana mai nunawa Ansar inda babur ɗinsa yake.

Ansar yayi murmushi, sannan yace "Amma fa ka kaɗa min hantar cikina, banyi tsammanin yana nan ba... Nayi zaton anyi gaba da shi..." Duka mutanen wajen suka bushe da dariya mai kama da yaƙe. Saboda yunwa da kowa yake ji.

Ansar ya hawo babur yana tafiya a titi cikin kwanciyar hankali, kawai sai wata mota ta biyoshi a baya kamar zatai awon gaba da shi, yayi maza ya sauka ya koma gefen titi, motar mai baƙaƙen gilasai ta wuce shi, amma bisa ga mamakinsa sai yaga wannan motar ta tsagaita wuta. Kuma itama tana sakkowa gefen titin a hankali, da ta saito shi sai ta sake bazamowa da gudu kansa, cikin zafin nama ya murɗa kulotin babur ɗin ya fita a guje ya koma kan titi yana tsala gudu, wannan motar kuwa sai ta biyoshi tana mai ƙoƙarin kayar da shi. Kasancewar titin akwai ababen hawa sai hakan ya hana motar samun damar taɓa Ansar cikin ruwan sanyi.

Ansar da yaga abin bana hankali ba ne sai kawai ya zame ya shige cikin lokuna inda motar ba zata iya bi ba.

Ko su wanene a cikin motar?
Zamu dakata anan sai kuma a rubutu na gaba.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now