16

36 6 0
                                    

Ansar ya kama jijjiga jikin mahaifinsa wani zazzafan hawaye yana zuba a idanuwansa, amma inaa mahaifinsa baya motsi.

Hajiya Juwairiyya kuwa ji tayi kanta yana juyawa tamkar mai yin hajijiya bata ankara ba sai kawai ji tayi ta faɗi ƙasa "yif".

Shi kuwa Ansar bai ma ankara ba sai faman jijjiga mahaifinsa yake yana zubar da hawaye "Baba.. Baba.. Baba.. Don Allah kayi magana Baba, don Allah ka kulani baba... Baba nine Ansar, Baba Ansar ne fa..." Yana faɗa cikin kuka lokacin da yake damƙe da  hannun mahaifin nasa a cikin nasa hannun.

"Kayi haƙuri saurayi, addu'a zakai kasan addu'a yake buƙata..." Wani likita da ya shigo ɗakin ya faɗa lokacin da yake sanya hannu yana rufe idanuwan gawar.

Ansar ya juyo zai kalli wanda ke maganar kawai sai yaga mahaifiyarsa a kwance likitoci kewaye da ita...

Nan take yaji zuciyarsa ta buga, kawai shidai ya tsinci kansa shima a kwance ana masa fifita.

Ga Khadija a gefensa da Hafsa da mahaifiyar su Hafsa dukan su sanye da hijabi.

"Ina Baba?" Ansar ya tambayesu.

Dukkaninsu sukai shiru hawaye yana kwaranyowa daga idanunsu.

"Kai namiji ne, kamata yayi ace kai ne zaka rarrashi yar'uwarka, tunda ta haƙura tayi imani da wannan ƙaddara, ganinka cikin wani yanayi babu abin da zai ƙara mata face damuwa... Kayi haƙuri, tun jiya take tsaye akanka ta kasa zuwa ko ina, ka daure ka tashi wataƙila mahaifiyarka idan ta ganka ta samu ƙarfi itama." Sadiya mahaifiyar Hafsa ce take furta hakan.

Hafsa kuwa ta buɗe baki zatai magana sai kuka ya sarƙe ta, sai kawai ta rungume Khadija.

Cikin ƙarfin hali Ansar ya miƙe, ya shafa kan Khadija ya sanya hannu ya katse hawayen da yake zuba a fuskarta, sannan yace "Addu'a zakiyi masa domin itace abar da yafi buƙata."

Ɗumbin al'ummar da ya gani bayan ya fita ƙofar gidan, sai kawai ya samu waje ya zauna. Nan take kuwa mutane zuka zo sukai tayi masa ta'aziyya. Duk lokacin da aka tmbayeshi ya ƙarin haƙuri, sai kawai yaji sabon raɗaɗin mutuwar ya sake zanuwa a zuciyarsa.

Ɗalibai kuwa sai da ya gaji da karɓarsu harma wayanda bai taɓa magana da su ba, ita kuwa Maryam yar ajinsu har iyayenta da sauran yan gidansu sai da suka zo masa gaisuwa, kuma suka yo abinci kala kala.

Duk wani nauyi na abin da za ai kuwa kama daga kan rumfuna da kuɗin sadaka gaba daya Alhaji Sambo ne yayi.

Tabbas wannan mutuwa ta girgiza Alhaji Sambo, domin lokacin da aka gaya masa mutuwar yana cikin meeting wani abokinsa da yake maƙocin su Ansar ne yayo masa text. Alhaji sambo sai kawai akaga ya kama bencin daya kewaye su yayi wurgi dashi gefe sannan ya hau faɗin innalillahi wa innailaihi raji'un...

Da shi akaiwa Alhaji Nasir wanka sannan dai dashi ɗin aka zira shi zuwa gidansa na kabari.

Gidan da tilas dukkaninmu muna tafe ko mai daɗewa muna da tabbas sai mun je. Kuma abin da zamu girba a can shi ne abin da muka shuka a anan.

Alhaji Sambo ya nemi iyalan Marigayi Nasir su koma gidan sa, amma sai suka ƙi suka ce zasu ci gaba da zama a gidansu.

Har akai arba'in amma kana ganinsu ba sai an gaya maka cewa suna cikin damuwa ba.

Wata rana kamar yadda Alhaji Sambo ya mai da zuwa gidan akai-akai, sai yaje, wannan kuwa bayan sati uku da yin arba'in ne. Sai ya tarar da su a cikin ɗaki guda dukkanin su suna suna zubar da ƙwalla.

Alhaji Sambo yayi musu sallama amma cikin su babu wanda ya iya amsawa saboda tsananin kukan da suke ciki.

"Haba bayin Allah, wannan kukan naku babu abin da zai ƙara masa fa, kun manta Annabi yace ana yiwa mamaci azaba saboda kukan iyalansa akansa?" Alhaji Sambo ya faɗa cikin faɗa. Sannan ya samu guri ya zauna ya ɗauko bakin gilas dinsa ya saka sannan ya ci gaba da cewa, "Abin da yake buƙata shi ne addu'a, kuma itace zai yi farin ciki da ita. Don me zaku bi ku damu rayuwarku, idan kukai kukan nan jikin ku zai mutu, sai ku samu rauni wajen yin ibada, idan kuwa kukai haƙuri kuka jure to sai ku samu ƙarfin yin ibada sannan kuma ku samu lada haƙuri wanda hakan zai zama silar ɗaukakar darajar ku tare da shi marigayi... Don haka abin da na ke so da ku shine kuyi imani da ƙaddara sannan ku yawaita nema masa gafars tare da addu'ar mu ma Allah yasa mu cika da imani..."

Daga wannan rana ne suka fara sakin jiki, amma shi Ansar kafin wannan tunda akai wannan rasuwar ko murmushin sa ba a gani. Tun Hafsa tana yi masa uzuri harma ta gaji ta daina. Musamman saboda zigata da su Junior sukaita yi na cewar ai dama baban Ansar shi ne yake takura masa ya so ta, kuma tunda ya rasu yanzu babu mai sauran takura masa don haka dole ya nuna mata kalar sa ta ainihi.

Suka daina tafiya tare, suka daina magana tare, ya zamana ma kusan koda yaushe tana cikinsu Junior.

A hankali Junior ya rinƙa shiga jikinta da abubuwan da ba ta ɗauke su a bakin komai ba, kamar gaisawa da mata (musafaha) da kuma runguma idan an haɗu. Daga bisani sai kuma riƙe hannun juna ya zama ba komai ba, wanda hakan ya fara ne da wata rana da yaga zobe a hannunta, sai kawai ya kama ɗan yatsan yace bari yaga wannan zoben don ya burgeshi, ta hanashi, a ƙarshe sukai kokawa ta wasa ya murɗeta ya ƙwace zoben daga bisani data damu sai ya bata kayanta yace sai dai ya saka mata, da fari bata yarda ba, amma da taga da gaske yake sai ta bashi dama ai kuwa sai ya saka matan. Bata ankara ba sai taji ya sumbace ta, tayi maza ta matsar da fuskar ta baya ta galla masa harara tace "What nonsense is this?"
"Ohh, you are still unwise..."
"What the fucking wise are you talking about...?
"Hahaha American lady..."

Hafsa kawai ta miƙe ta ɗauki jakarta ta fice daga cafeteria ɗin wadda kusan koda yaushe a ciki suke rayuwa mutuƙar babu karatu a aji.

Zamu dakata anan.

Sai kuma a rubutu na gaba.

Sai kuma a rubutu na gaba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now