26

27 1 0
                                    

Ita dai ta farka ta ganta a asibiti, mahaifanta tsaye a kanta, yayin da wata nurse ke ƙoƙarin cire cannula daga hannunta, idanuwanta cike da ƙwalla...

"Ko kaɗan ban taɓa dana sanin kasancewarku mahaifana ba", Hafsa ta furta lokacin da take kallon mahaifiyarta ido da ido, "Amma tabbas na yi dana sanin biye muku by creating a fictional fake person into my life... ana cewa iyayenmu a zamanin da sun yiwa ƴaƴansu auren dole, wanda ku kanku na san ba shi akai muku ba... To don me ni zaku tilastawa zuciyata tun ina ƙarama wajen ƙirƙirar mata soyayyar mutumin da bai san mutunci ba?" Ta sake fashewa da kuka.

Nurse da take tsaye ta saki baki tana kallon ikon Allah, Hafsa sai a lokacin ta kula da ita, ta kalleta tace "Ke kuma me kike ina? Ki tafi ki bani waje..."

"Hafsa, menene haka?" Alhaji Sambo ya faɗa cikin wata murya mai taushi. Ya ci gaba da cewa "Kinsan ba zamu taɓa cutar da ke ba, kuma ba zamu taɓa barin abin da zai cutar da ke ya raɓemu ba, ki yi haƙuri idan har abin da muka zaɓa miki bai miki ba..."

"A'a Dear," Matarsa ta ambata tana mai gyara zama akan gadon da Hafsa take kwance, "Wannan rigimar yara ce, bai kamata ka tsoma bakinka ba, idan suka kewaye suka shirya ku za su bari da jin kunya..."

Hafsa da ke kwance ta tashi fitgigit ta zauna kamar wadda taga wani abin tsoro "What?? Umma me kike cewa haka? Allah ya kiyaye, ai kuma anyi an gama, bana jin akwai sauran soyayyar wannan mutumin a raina, kamar yanda ya daina ganin girmanku da har zai iya kirana ya ci mutuncinku, to haka nima zan iya cire duk wata soyayyarsa da ƙimarsa daga cikin zuciyata..."

"It seems like you are talking nonsense " Mahaifinta ta faɗa.
"All words I mentioned are full of sense... Baba kasan ina son mutumin before amma yanzu kam na haƙura..."

Zaune take tana tunani, lokacin da take kai komo cikin hotunan album da yake ɗauke akan cinyarta, gefenta Khadija ce ƙanwar Ansar yarta mace guda ɗaya kuma ƴar autarta, wadda ta kwantar da kanta akan kafaɗar mahaifiyar tata lokaci guda kuma tana satar kallon yayanta, wanda ga dukkan alamu yana cikin damuwa.

"Umma kenan an haifi Yaya Ansar a shekarar 1987 kenan?" Khadija ta tambaya tana cike da mamaki.
"Eh mana, an haifeshi 1987 cikin watan February, ita kuma Hafsa an haifeta 1991 cikin March, ba na mantawa kuwa cikin shekarar General Babangida ne shugaban ƙasa, kuma shi ne ya ƙara jihohin Nigeria daga 21 zuwa 30..." Mahaifiyarta ta bata amsa tana ƙoƙarin zamewa daga jikin ƴartata.
"Umma, kina nufin wasu jihohin da ba sa cikin Nigeria shi ne ya karɓosu ko ƙwatosu?"
"Ba haka nake nufi ba. Alal misali, a wancan lokacin akwai jihar Gongola, Sai ya rabata gida biyu ya mayar da ita Adamawa da Taraba..." Mahaifiyar ta bada amsa, a lokacin kuma tana ture kan ƴartata daga jikinta.
"Auho, nagane, ai kuwa ya kyauta." Khadija ta faɗa tana murmushi lokacin da suka haɗa ido da yayanta wanda yake karanta wani littafi da bata san ko me ya ƙunsa ba, a jikin bangon dai ta ga an rubuta 'Tafiya Mabuɗin Ilmi' yayin da a wajen sunan marubucin kuma taga an saka Abubakar Imam.

Khadija ta miƙe zaune sosai sannan ta kira sunan yayan nata, ya ɗago a nutse ya kalleta, sanna ta yi gyaran murya tace "Wannan littafin na hannunka me ya ƙunsa?"
Ansar yayi murmushi, "Ya ƙunshi labarin tafiyar Abubakar Imam ne zuwa ƙasar Ingila don amsa gayyatar da akai musu..."
"Okay, shi wanene Abubakar Imam ɗin?"

Kafin Ansar ya bata amsa mahaifiyarta Juwairiyya ta karɓi tambayar domin dama tana da abubuwan faɗa da yawa dama kawai take nema, ta ce "Yaran yanzu ban san me kuke koya a makaranta ba. Yanzu yarinya babba kamar ke bata san Abubakar Imam ba? Marubucin Ruwan Bagaja da Magana Jari ce ba...?"
Khadija ta buɗe baki za tai magana bisa ga mamakinta sai taga mahaifiyartata ta ci gaba da cewa "In banda lalacewar ilmi ta yaya za ai ace daidai da tarihin ƙasar nan ba a sanar da ku ba, ca nake yanzu ba ma kinsan cewa jihohi nawa muke da su ba, to babu tarihi ta yaya yara za su taso da soyayyar ƙasarsu... Sai faman shagwaɓa wadda a al'adar ƙasar Hausa ma da yawan shagwaɓar a matsayin rashin kunya ake ganinta, ca nake yanzu da ƙyar na yakiceki daga jikina..."
Khadija ta yi murmushin ƙarfin hali sannan ta kalli gefe, kana tace "Umma idan ban ɗora kaina akan kafaɗarki ba akan tawa zan ɗora?"
"Na sha gaya miki, ki tuna mu Hausawa ne, mu a lokacinmu dai dai da sunan ɗan fari iyayenmu ba sa iya furtawa balle har a zo baton shimfiɗawa yaro kafaɗa ya kwanta akai don rashin kunya... Zamani ne dai kawai an zo shi sai yadda aka gani..."

Ansar da yake gefe yana karatu sai ya ajiye littafin da ke hannunsa sannan ya fara da cewa "Umma, ba kowace al'ada ake ɗauka ba, wata al'adar ana ajiyeta saboda ta ci karo da addini, wata al'adar kuma ana ajiyeta saboda ta saɓawa zamani. Jan ƴaƴa a jiki dabam sangartasu dabam."

Juwaira mahaifiyar Ansar ta gyara zama tana saurararsa, lokacin da amon muryarsa ne kawai ke wanzuwa a cikin ɗakin, kai kace kowane abu na cikin ɗakin ya nutsu ne yana saurararsa hatta abubuwan da ba su da rai.

"Kakanninmu Hausawa sun iya bawa yaransu tarbiyya ta hanyar barin tarbiyyar yaro ga al'umma, ta inda su iyaye sau da yawa suke zage damtse wajen ganin lallai sun tanƙwara ɗansu ya yi abin da ya zama shi ne dai dai, kuma duka al'umma sai suka taya su, akai sa'a kuma wayon yara a wancan lokacin ba shi da yawa, ta yanda ɓoyuwar laifuka a wajensu abu ne mai mutuƙar wahala," Ansar yayi murmushi da yaga mahaifiyarsa tana sauraronsa cike da gamsuwa. Ya cigaba da cewa. "Sai muka riski wani zamani wanda yara a cikinsa suna da tsananin wayo, sannan iyayen sun kasa jurewa su bar al'umma ta tayasu rainon ƴaƴansu, har al'ummar ta ginu akan hakan, kowa nasa kawai ya sani... A irin haka sai lamari ya sauya ta yanda tanƙwara yaro ta ƙarfin tsiya babu abin da yake haifarwa sai buɗe kwakwalwar yaro don ganin ya kere tunanin iyayensa, ya kuma ɓoye musu wasu abubuwa da yasan ba dai dai ba ne. Don haka sai ya zamana babu hanyar da iyaye za su bi yau don tarbiyyar yara sama da jansu a jiki ta yanda za su gano duka damuwarsu, kuma daɗin daɗawa tunda yaran nan suna kallon fina-finan India da Turawa, suna ganin irin soyayyar da ake nunawa ƴaƴa, don haka suna ganin saɓanin haka abin da za su fara tunani shi ne; su waƴancan sun fi son ƴaƴa akan iyayensu, ba za su taɓa hasashen cewa akwai bambancin aƙida ba, daga nan sai su fara tunanin su ba a sonsu... Sai wasu tunani su fara shigar musu wanda in ba a kiyaye ba cutar damuwa za ta iya jefasu cikin wani hali wanda ƙarshensa ba zai kyau ba..."

Ansar yayi murmushi sannan ya ce "Bayani ne dogo, amma dai nasan wannan ɗan fashin baƙin da nayi zai bada haske."

"Allah ya ƙarawa rayuwa albarka, ya rayaka, ya baka mata tagari da arziki mai ɗorewa da ingantacciyar lafiya." Mahaifiyarsa ta faɗa lokacin da take ɗaga hannu sama.

"Ameen tare da ke mama, da ƴar'uwata, ya kuma gafarta mana zunubanmu" Ansar ya ɗora daga indata tsaya.

Duka su ukun suka haɗa baki suka ce "Ameen".

A sannan ne kuma Khadija cikin hanzari ta miƙe tsaye tana zazzaro ido game da dafe ƙirjinta tana mai kallon wayar da ke hannunta.

Ansar da mahaifiyarsa suka haɗa baki suna tambayarta "Lafiya?"

Zamu dakata a nan.
Sai kuma a rubutu na gaba.
Tare da ni
Naseeb Auwal

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now