23

48 2 0
                                    

Da sanyin safiya Ansar ya sake ganin kiran Maryam ƴar ajinsu, ya tsaya ya ƙurawar sunan nata ido a zuciyarsa kuma yana ta tunani shin me yasa Maryam ke yawan kiransa.

Da fari yayi kamar zai kirata amma kuma sai ya tuno wayar tasa babu kuɗi, don haka sai ya ajiye wayar gefe gami da yin ajiyar zuciya.

Bayan ya shirya kafin ya fita sai ya nufi system ɗinsa, ya kunna yana son duba email ɗinsa ya ga ko an turo masa saƙo.... Bai ga wani saƙo ba sai saƙonnin social media platforms waƴannan kuwa yasan basa wuce maganar siyasa da musun addini. Ya duba saƙonnin mutane ya babbasu amsa a whatsApp da Facebook daga nan ya rufe laptop ɗin ya mayar da ita inda take ajiye tsakiyar littafai shimfiɗe akan wani tebur na roba. Ya miƙe ya je ya gaishe da mahaifiyarsa daga nan ko duba Khadija ƙanwarsa bai yi ba ya fice saboda lokaci ya fara ƙure masa.

Kasancewar akan babur yake bai ɗauki tsawon lokaci ba sai gashi a makaranta, yana tafe yana sauri sai kawai ya ji alamar ana binsa a baya, nan take kuwa ya kasa kunnensa don jin wanene ke biye da shi, sai ya ji takun yafi kama da na maza, kuma ana takun ne da alamar sassarfa, don haka sai ya rage nasa saurin don bawa mai tafiyar damar cimmasa, duk da haka dai bai juya ba.

"Assalaam Alaikum" Mai takun ya faɗa lokacin da suke gab da jeruwa da Ansar.
"Wa alaikum Salaam warahmatullah." Ansar ya amsa yana mai juyo da fuskarsa don ganin mai sallamar.

Roget cikin shigar jallabiyya da hula wadda ta rufe askin banzan da yake kansa, indai ba farin sani kayi masa ba bai zama lallai ka gane shi ba.

Ya miƙawa Ansar hannu suka gaisa, sannan ya maƙe murya ya fara da cewa "Alhamdulillah, bawan Allah na zo maka da wata muhimmiyar magana kuma naga kamar sauri kake, amma gaskiya duk saurin da kake ya kamata ka ajiye shi domin muhimmancin maganar ya kai duk inda kake tunani, kasan ance mai sonka shi ne yake gaya maka gaskiya..."

"Na'am, ina jinka. Duk da dai ban cika son ɓata lokaci wajen tattaunawa da mutane ba, amma don Allah kayi ƙoƙari ka taƙaita. I have something very important to attend." Ansar ya ba shi amsa.

"Ba damuwa ya ustaz" Roget ya faɗa yana mai shafa ƙirjinsa sannan ya gyara tsayuwa ya zira hannu cikin aljihunsa ya ɗauko wani hoto ya miƙawa Ansar yana cewa "Ai kasan wannan wacece ko?"

Ansar ya karɓa kai idonsa da zai yi sai kawai yaga hoton Hafsa ne, ta saka wasu kaya ƙananu kuma da alama hoton an ɗaukeshi a gidan rawa ko club. Ansar ya kalli Ustazun yayi murmushin ƙarfin hali yace "Yanzu me kake son cewa?"

"Yawwa, kamar yadda ka gani, nasan wannan ƙanwar ka ce, kuma dai ga dukkan musulmi ya san irin wannan shigar ba ta dace da Musulmi ba, haka nan ta saɓawa al'adar Hausawa, don haka nake baka shawara ka ƙara saka ido akan ƙanwarka ka tabbata ka hanata faɗawa irin abin da ƴammatan yanzu suke faɗawa..." Roget ya ɗan tsaya yana nazartar fuskar Ansar amma ya kasa gane wanne karatu aka rubuta akan fuskar.

"Nagode. Akwai wani abin ko shi ke nan?" Ansar ya tambaya yana murmushi.

Roget ya cika da mamaki domin bai ga alamun tashin hankali ko jimami a tattare da Ansar ba. Duk da haka sai yayi ƙarfin hali ya cigaba da cewa "Shi ke nan don wannan shi ne abin da zan iya nuna maka, ragowar ba zasu nunu ba..."

"Ai da ka zo da su ma ba zan kalla ba, domin na santa fiye da yanda ka santa, nasan abin da za ta yi kuma nasan wanda ba za ta yi ba... Nagode."
Ansar kawai sa yayi gaba ya kyale Roget anan yanata faman mamaki.

Ansar yana tafiya amma wannan hoto shi yake tayi masa yawo a cikin kwakwalwarsa, babu abin da ya fi damunsa face gaya masa da akai ai akwai wasu hotunan wayanda sun fi wannan muni... Yana tafe idanuwansa cike da kwalla, ya rinƙa zagaye a makarantar ba tare da yasan inda zai je ba... Ya manta ma akwai wani abu lecture a duniya. Zuciyarsa ta rinƙa saƙa masa abubuwa yana tunanin ta ina ya kamata ya bijirowa Hafsa, me ya kamata ya aikata?

Kwakwalwarsa ta gaza samar masa da amsa wadda zata zo masa da waraka, domin dukka amsoshin da suke zuwa maimakon ya samu sauƙi sai tunaninsa ya kuma nausawa wani gurin inda da can bai je ba.

Za mu dakata a nan sai kuma a rubutu na gaba.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now