6

63 6 5
                                    

Kamar kullum, dare ya tsala baka jin komai sai ƙarar ƙwari da kuma kai kawon halittun dare, sai kuma jefi-jefi zaka ji haushin karnuka gami da kukan mage ko muzuru wayanda suke kai kawo akan katangar gidajen unguwannin mutane masu ƙaramin ƙarfi. Duka wannan abu dake faruwa, Ansar yana cikin ɗakinsa, ya ɗaga kansa sama kawai yana kallon fankar da take juyawa da tsananin gudu, ko kaɗan ƙarar da fankar take bata dameshi ba. Hasalima kana kallon fuskarsa kasan tabbas akwai abin da yake tunani.

Tunda ya kwanta abu ɗaya ne yake ta kai kawo a zuciyarsa, ba komai bane face tunanin Hafsa, idan ya rintse ido da zummar yayi bacci sai kawai yaga fuskarta tana murmushi da idonta cike da kwalla, don haka babu shiri sai ya buɗe idon.

Ya rasa gane me yake tunani a cikin zuciyarsa, don haka sai kawai ya miƙe, kamar yadda ya saba, ya ɗauko wani littafi Americana na Chimamanda Ngozi Adechie ya fara karantawa da farko tunanin ya kau daga zuciyarsa, amma zuwa wani lokaci sai ya tsinci kansa kawai buɗe shafukan yake ba tare da yasan me yake karantawa ba. Hasalima dai idanuwunsa suna karanta abin da yake cikin littafin amma saƙon da ke cikin zuciyarsa shi ne abin da ke tafiya zuwa ga ƙwaƙwalwarsa.

Ba shiri ya rufe littafin, ya kwanta yana mai kifa kansa a ƙasa wai ko zai daina ganin Hafsa, zumbur ya mike yana mai faɗa da ƙarfi subhanallah... Domin ita ya gani tana murmushi a inda ya kwanta. Ya tsaya kawai zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi, tunaninsa ya rinƙa rige-rige daga zuciya zuwa ƙwaƙwalwa, idan wannan ya shiga kafin ya kammala shi wasu sabbin tunanin sun shigo.

"Da wannan tunanin da kake dama sallah ka tashi kayi daya fiye maka." Mamansa juwaira ta faɗa lokacin da take tsaya a bakin ƙofar ɗakinsa.
"Karka sanya damuwa a cikin zuciyarka," taci gaba da faɗa "Hafsa da kake ta kira tana cikin ƙoshin lafiya. Ƙanwarka Khadijah fa duk tana jinka, tana jin me kaketa cewa, sai dariya take tana cewa ita tasan indai kaje kayi ido huɗu da Hafsa to sai haka ta faru, amma ba tayi tunanin abin zai kai haka ba... Ka rinƙa surutai kamar mai aljanu... Wai dama ka iya waƙa haka?"

Ansar kawai ya tsaya yana kallon mahaifiyarsa cikin kunya da tsananin mamaki, shin da gaske surutan yake? Da gaske har rera baituka yayi? In kuwa hakane to yanzu ma wataƙila ta jishi tunda shidai yasan ko wayancan abubuwan data faɗa a cikin tunani yayi su...

"Idan kaga dama" muryar mahaifiyar tashi ta katse masa tunani, "Sai ka tashi kayi raka'atanil fajr." Ta cike maganarta lokacin da take jan ƙofar ɗakin nasa wadda tayi wani sauti sakamakon kartar ƙasa da take yi.

Ansar yayi ajiyar zuciya, sannan ya nufi banɗaki, fitarsa daga ɗakinsa keda wuya sai yayi kiciɓus da Khadija ƙanwarsa. Tayi murmushi sannan yaji ta fara wasu baituka kamar haka...

Tun ranar dana ganki
Zuciya ta zama taki
A idanu in ganki
Burin raina
Hafsa mai kyawu kike
Ga kyau na idaniya
Buri na zuciya
Ke sarauniya
Hafsa...

Ansar ya faki idonta ya kai mata duka amma sai ta zille ta kyalkyale da dariya ta shige ɗakinsu wanda ita da mamanta suke kwana a ciki.

Wani sauti cikin faɗa yace "Ku shashashan ina ne? Cikin dare gab da fitowar alfijr lokacin da kowane mutumin kirki ke miƙe buƙatunsa zuwa ga mahalicci amma ku kunzo kuna shirme da hauka..." Muryar Alhaji Nasir ce mahaifin su Ansar.

Ansar a zuciyarsa yace "Baba kaima ɗaga muryar da kake kana faɗa da wannan lokacin aiba dai dai bane..."

"Me kake cewa? Ina jinka ai." Mahaifin nasa ya kuma faɗa cikin faɗa.

Ansar bai sani ba, da gaske mahaifinsa ya ji shi ko kuwa bai ji shi ba, shi dai kawai yabi bango sum-sum-sum ya shige ɗakinsa. Da shigarsa ya zauna ya ɗora daga inda ya tsaya, amma wannan karon baya barin tunaninsa ya ƙaraso bakinsa.

Bai ɗauki wani lokaci ba, sai kawai ganin Hafsa yayi tazo bakin ɗakin nasa ta tsaya, ya kalleta cikin mamaki, ya mike yana mai dafe ƙirjinsa cikin firgici yace "Hafsa... Me kikeyi anan da wannan lokacin?"

Sai da yaji an doka tsaki sannan idanunsa suka tabbatar masa da cewa ba Hafsa bace mamansa ce a tsaye a bakin ƙofar, ta murtuke fuska.

Cikin jin kunya ya rufe fuskarsa ya zauna yana mai girgiza kansa.

"Mallam, Gaskiya baka da lafiya." Mamansa ta faɗa.

"Gaskiya bani da lafiya." Shima ya maimaita.

"Tashi ka tafi masallaci lokaci yayi."

"Tohm."

Babu musu ya mike yaje yayi asuwaki, sannan yayi alwala daga nan ya gyara shigarsa ya aza hula a kansa ya ɗan taje matashin gemunsa, sannan ya shafa turare, daga bisani ya nufi hanyar fita daga gida.

"Ansar," mahaifiyarsa ta kirashi. "Kada ka sake azo ace min kana ambaton sunan Hafsa a masallacin nan."

"Insha Allah, hakan bazai faru ba."

Me zaku ce akan wannan labari?

Ayi mana haƙuri zamu dakata a nan.
Tabbas votes da comments ɗinku ababen buƙata ne, anan ne zamu ji kuma zamu gane ina zuƙatanku sukafi karkata...

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now