_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......4
Duk yinin yau Khairat bata fito ba,saidai salma ta ringa kawo mata abinci har d'aki,tunda ta dawo daga makarantar ko salma bata nuna ma result d'inta na,yah Meenah kawai ta gani Itama don tasan bazata fad'ama kowa bah, duk yadda shahida tayi akan ta bata ta gani cewa tai wai nata yab'ace idan ankoma hutu za,a sake dubawa.
Shahida bata yarda bah haka ta rabu da ita saboda sanin Khairat badai taurin kaiba.
Kwance take ta gama sallar isha,i tana saman abun sallar salma ta shigo jikinta yayi mugun sanyi, ta samu gefen gadonsu ta zauna kallon Khairat kawai take,zuwa can tace.
"sweetheart wai kina lafiya kuwa?."
Tana daga kwance bata ko d'ago ba tace,
"lafiyar kenan mekika gani."Isowa tayi wajenta ta na tadata zaune,
"wallahi sweetheart baki da lafiya, bafa tun yau kike wannan Abunba I think tun fad'an................"bana son tada abunda ya wuce kinarni na huta pls sweetheart."
"Shikenan kiyi hakuri, daman Abbu ne yake neman mu mu duka,ke kawai akejira."
Runtse idonta tayi tanajin Wata matsananciyar fad'uwar gaba,tabbas maganar result d'inta za,ai kuma tasan Yah Aree ya binciko repiting d'in da akai mata...........yau ita tashiga uku idan ya kamata, babu abunda ya tsana sama da kafad'i exams,ko Su yah shahid idan yaga sun fad'i suna gane kurensu, zai kawar da komi ya baka punishment.
"sweetheart karfa yah Areef ya biyo mu,naga yau cike yake damu bama mu ba wallahi har su Anty ma haka."
Tashi tayi tana jin wata masassara mai zafi na ratsa dukan jikinta,
Ko hijab d'in dake jikinta har k'asa bata cire bah tace,"muje"
Haka suka jera suka tafi,yayinda Khairat duk taku d'aya gabanta yake tsananta fad'uwa, ji take kamar tayi fuffuke ta tashi ko kuma tayi Samara anemeta arasa.
Koda suka zo bakin k'ofar babban falon Abbu sai ta tokare ta k'ishiga, salma tayi tayi ta shigo ta k'iya dole ta kyaleta ita tashiga.
Zama tayi Maah tace,
"Ina Khairat d'in yo."Cikin karyewar murya tace,
"Maah don Allah Kice kar yah Aree karya doki sweetheart,wallahi kingan ta can ta kasa shigowa tsoro take ji."Dariya kawai Maah tayi don yau zata ga yadda za,a kaya Areef zai iya hukunta kannen nashi.
Abbu Ya kwala mata kira,
" *ta Alkairi* shigo kinjiko yayanki bazai maki komi bah."
Dayake haka yake ce mata tun da aka haifeta.kasa shigowa tayi ganin tak'i shigowa yasa ya bud'e deep voice d'insa yace mata.
"wallahi Idan na iso wajen nan jikinkine zaiyyi tsami,dani kike bayani yau Allah kuwa."
shahid yace yana dariya,
"oga sweetheart ce fah."Harararsa yayi yace" to ina ruwanka y'an saka ido."
Anty shahida da Yah meenah Su mujahid duk dariya suke mashi,
Kamar wadda k'wai ya fashe wa aciki haka ta fara bin bango kamar gizo gizo, sosai ta bashi tausayi, Amman baijin zai rangwanta akan wannan saken da tayi,tunda yasha fad'a masu cewar karsu had'a karatunsu da komi, karsu yarda damuwa ko wani Abu ya d'auke masu hankali akan karatunsu.Kusada Anni ta zauna idonta ya cika tab da kwallah, k'iris take jira ta fashe kuka.
Abbu ne yace yah shahid ya bud'e taron da Addua
Yakaranto muka shafa.
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda