_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......24
Wani irin tuntub'e ne nayi daya yi silar fad'uwar pos dina,dama d'an rakiyar tunda yashigo dani wajen yajuya tunda naga inda zanje,duk'awa nai na d'auka inajin d'an yatsana yana jinga babban,d'agowar da zanyi naga wayam inda yake zaune su biyun saura Dr amman shi banganshi ba,murje idona nayi sosai amman ban ganshiba ko iskar da ta d'eboshi ban ganiba,waige waige nake amman ko b'urbushinsa ban ganiba.......jikina yayi wani irin sanyi nabani uku wai k'alau nake kuwa kodai tsoron sa ne yasa naga kamar shine awajen da farko,k'arfafa zuciyata nayi na karasa wajen ina ajiyar zuciya k'asa k'asa.
Tun kafin na zauna yake kallona yana zaune kan kura ga table gabansa an k'awata shi da yan kayan ci kadan,yad'ora kafarsa kan d'aya yarik'e hab'arsa da hannunsa,fesincap ce kansa wadda ba sosai nake kallon cikin idonsa ba,tabbas Dr ya hadu hadedden guy ne,wanda ya iya daidaita wankanshi,jeans ne dark blue sai light blue d'in shirt tabi jikinshi ta kwanta,agogoce d'aure ga hannunsa na hagu sai daukar ido take,kamshi ketashi mai tsananin shiga rai da kwantar da hankali,har lokacin kallona yake nikuma ina tsaye,da hannunsa ya yi man nuni da na zauna,kujerar dake kallonsa jikina yayi wani lakwab haka na jaye hijab dina na zauna ina wasa da yatsuna,nakasa kallonshi,don bazan iya had'a ido dashi yana mun irin wannan kallonba.
Cap din naga ya ajiye gabanshi ya tashi zaune sabanin da dayake kwance cikin kujerar.
"Ina wuni."
Wayyo kamar zan nitse haka nakeji,kunya ta kamani mema yasa tunda nazo ban gaidashi ba,kasa ansawa nayi inata matsar yatsuna kamar zan tsinkasu,kozafi banaji wanda da kalau nake bazan iya sarrafasu irin haka ba.
"Karkijima kanki ciwo,yana zuba lemo cikin cup fuskarshi da murmushi wanda kokad'an baya yinsa cikin class.Mik'omun yayi "bismillah,ance in kayi bako first abunda zaka taryeshi dashi shine abunsha,kafin komi yabiyo baya."
Duk na kasa sakewa gashi sai kallona yake ni kallonne bansaba dashiba,yana ban kunya kuma idaniyata bazata zureba.
Cikin low voice dina da bansan dalilin sanyinta ba nace"sorry sir good evening."
Sautin murmushin sa naji yana rik'e da cup din ruwa saida ya kurba sannan yace"bazan ansa ba tunda nima baki ansa tauba."
D'agowa nai nad'an kallai kafin nasadda kai nace"sorry sir bazan it ansa gaisuwarka ba,bacin ni yadace nafara gaidaka kuma banyiba,I'm sorry na shafa,a ne."
Ajiye cup d'in yayi yana tattara duk hankalinsa kaina,
"Me ya shagaltar dake,nagadai ko kallona ma bakiyiba balle nasaran ko *Muhammad kamees* ne ya d'aukar maki hankali."
Innalillahi wayyo Allahna wannan guy din ya iya bada kunya,jinai kamar inzura aguje.
(😂😂😂basaban ba khairat)Shiru nai inata murzar hannuna nakasa cewa komi,to mekuwa zance mai jinai yace"kinyi shiru,kisaki jikinki bafa sace ki zanba wallahi ban iya satar mutane."
Dariya yaban bashiri murmushi ya kubcemun mai had'e da dariya,rufa bakina nayi nakara sadda kaina inayin abuna.
Inajinsa yana tayani amman nashi babu sauti sosai.
Saida nagaji nadaidaita kaina yace,
"Haka kika iya dariya,
Aikuwa zaki koya man nima naringa yiwa budurwata."
Kallonsa nai bance komiba murmushi dai nake yi.
"Meya hanaki zuwa class 2days,anyi abubuwa dayawa bakyanan."
Nad'an saki jikina nace masa
"Wallahi bana da lfy kwana biyu amman nasamu sauk'i,husna tana mun bayani idan ta dawo."
"Kin tabbata tana yi maki,"
D'aga kai nayi murmushi yayi yace "to bari mugani idan bayanan sunzauna kanki."
Tambayoyi yashiga yiman ina bashi ansa tare da bayani sosai.
Tab'i yashiga yimun yana cewa "good,very nice gaskiya husna ta cancanci kyauta kibata wannan inkin koma."
Wata envelop ce ya mik'omun.
Kallosa nai nace"sir kabarshi ai basai kabata wani abuba."
Gabana ya ajiye yana kallon cikin idona yace"don me basai anbata ba,bayan tayi abunda ya farata man,kefa ta yiwa taya bazanji dadiba."
Sadda kaina nayi nama rasa mezance masa wlh
Dole na k'akaro smile nace"to tagode."Shiru muka sake yi na tsayin lokaci,kuma har yanzu idonsa akaina wlh jinake kmar in bace sabod wannan kallon nashi.
Ga magaruba tataho dandanan hankalina ya tashi,saboda ganin bakwai saura minty talatin."Da alamun dai kin k'osa kibar nan ko,ban tunanin wajen bazai burgekiba aida munje *kalam guiden*."
Yak'e nayi nace"Aa wlh yayi kyau,sosai wajen akwai nishad'i."
Mik'ewa yayi yana cewa"musanman idan akwai wanda ya sace mka zuciya awajen ba."
Ban tashiba nabishi da kallo,shima ni yake kallo wanda bazan iya jure shiba,inda nake ya iso yad'an sunkuyo ta gefen fuskata kamar zai sunbaci kuncina,dandanan jikina ya kama kerma runtse idona nai injin kashin turarensa yana huda gashin jikina,i wonder nakejin something akanshi,mekenan nashiga ukkuna.
Cikin wata murya da tayi masifar tada tsikar jikina yace" *ummulkhair,why kika mun irin wannan satar plsss ko kinsan kin kassarani akanta,na zama zero tundaga lokacin da kika yimun wannan satar,plsss ki maido man kayata in samu relief.*"Tunda yafara magnar kirjina ke bugawa babu k'ak'k'autawa,na k'an kame jikina da nakejin kamar yana zarar raina kamar yana fiddamun duk wani kuzari dayayi saura cikin jikin. Wata ajiyar zuciya nasauke mai mugun sanyi jin yatashi daga inda yake,bud'e idona nai ina jin kamar na fasa ihu akan yanayin danaji.
Pos din ya d'aukarmu namik'e shikuma ya jaye kujerar nafito,tare muke tafiya zuwa inda yayi parking.
"Bakice komi ba."
Fuskata kamar zanyi kuka na kallai nace'pls wlh bansan abunda na satar makaba kayi hkr."
Dariya yashigayi yana shafa kanshi,hannunsa yana rik'e da cap dinsa,
"Gaskiya ba zanyi hkr ba sai kin biyani,idan kuma baki biyaniba zan rama idan na tashi ramawa naki sai yafi zafi,don ko har kuka saina saki."Shiru nai banda ansar bashi,a matsayina na yar jamia wacce ta waye tasan kuma me ake kira da so,to dole nasan me dr yake nufi da kalamansa akaina,nagane komi yke nufi dani nagane kenan yadda na sace mashi zuciya shima yna nufin zai sace tawa.
Hakika zan iyacewa zuciyata babu kowa aciki,empty set take amman kuma inajin can k'asan raina wani gurbi da wajen yake yawan bugawa,muddin naji wani feelings akan DR hakan meyake nufi,basan me hakan yake nufiba nabarwa Allahn daya halittamun wannan zuciyar.Bud'emun gaba yayi nashiga yazagayo yashiga,fita mukai mukai mukanufi school,jana yake da fira anman nakasa sakin jikina nabiyeshi,saboda maganarmu dashi ta karshe itace kemun yawo akai,wani gefen zuciyata inajin tsoron Kamuwa da sonsa,wani shashen yana nuna man idan nakamu da son nashi menene,wanda kikemawar dai akwai babban ginshik'i tsakaninku,duk yadda kikakai ga son kasancewa dashi yariga ya zama haramiyarki.
Rutse idona nayi inajinsa yana ta gayaman wsu kalamai wanda babu tantama dr zai iya yin nasarar sacemun zuciya cikin d'an karamin lokaci,kamar yadda yafad'a man.
Bakin get d'in hostel ya saukeni saida nayi dagaske sannan yabarni nashige..........Allah Allah nake na isa d'aki,don inji shin an aiko nemana,inhar an aiko to tabbas yah yazo,inkuma bai aikoba hakan nanufin baizoba.
Don yanzu takwas harda minty ashirin.Husna na tadda tana bud'e wata katuwar ledar shooping,kayane gasunan birjik kamar ba,asan zafin kudiba aka siyosu,tsayenai ina kallon kayan,nidai nasan Dr bai ban komiba ,haka bai aiko kowaba to waye zai kawo,kodai husna aka kawomawa.
Jinai tace"sai yanzu kenan,da alama Dr yasamu karb'uwa."
Banbi takan kalaminta ba nace"bak'o kikai husna."
Mik'ewa tayi tana jingina d bango tace"aa,ke aka kawowa yayanki ya zo bazan iya lissafa adadin mutanen daya turo nemankiba,inacewa baki fito lecture ba,karshe hardai nace bakidawo d'akiba.
Baiyi minty goma da tafiya ba ga kaya nan ya aiko dasu abaki,hada wasu cards idan kin duba duk zaki gani."
Silalewa nayi k'asa wata zufa na karyomun zuciyata da sauri take bugawa............Mom muhseen✍🏻
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda