19&20

22 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira7531

    🅿️.......19&20

Kwana yayi yanajin gabansa yana fad'uwa,lumshe ido yayi ya bud'e ya najin gajiya na bin duk kanin gab'anshi,shiyasa yake tafiyar a slow kamar maijin bacci,garin akwai duhun dare ga iska mai dadin shak'a da ratsa jiki,ga dukkan alamu ma hadarine don su weather su haka take,ayi sanyi ayi zafi wataran ma ruwa zakaga anwuni anayi.......get din makarantar yashiga duk sai y'an tsiraru ke yawo......muna bakin wani department na hango motar yah jahid,don duk tunanina shine saboda motar irid'a yace.
"Kinga husna labarin gay din nan bazai k'areba bari kiga ni ga yah jahid can yashigo."
"Aikuwa sweetie daga nan zanjuya don idan nace rakaki zanyi toni babu mai rakoni,don wallahi tsoro ake badawa irin wannan time d'in."

Sara mata nayi nace"bakida case sweetie,good night ayi mafarkin yah shahid."
Dariya tayi tace"ok kekuma kiyi na Dr MK."
Murmushi nayi najuya ina tafiya sauri sauri,don daga inda yake hangena nima nake hangenshi akwai d'an nisa babu laifi,hakanan naji kafafuna suna hard'ewa,jikina yacanza gab'a daya gabana yaringa fad'uwa.........innalillahi wa inna ilaihir raju,un na anbata,saboda aduk sanda najini cikin wannan condition din to tabbas dodona nawajen,saboda tsabar tsoransa dana sawa raina jikina har ya saba muddin yana kusa da inda nake tunkan idanuwata suyi tozali dashi jikina zaifara rawa gabana yana faduwa.......jikina amace na isa bakin motar hannuna karkarwa yake,Allah yasani inajin tsoronsa fiye da kima,more excspcialy tsawarsa idan ya kwatsa man ita.
Murda kofar nake tak'i bud'uwa.......shikuwa kallonta kurun yake,kafin yaja k'aramin tsaki yabude mata da kanshi.....ina kerma nazura k'afata na dosana duwawuna na zauna dandanan naji idona yacika da ruwa,kuka keson kucceman bansan daliliba,kodan banson abunda zai kusantani dashi daidai da second banson mu had'u.....tada motar yayi yafice cikin sanyinsa kamar baison tukin,tafiya suke iska na kad'asu don glass d'in tagar wjena sauke yake k'asa,dama kuma sauken na ganshi.
yayyafi akafara iska yafara man yawa,amman banda halin cewa zan kulle rawar sanyi nake tunda amotar ma AC ya kunna kuma k'arshe take.......jinai yadakan tsawar danake tsoron karyamun har muje gida.........."ubanwa yace kisauke man glass,zaki maidashi kosai naci ubanki,stupid girl."
Hannu na yana karma nasaka namaida hawaye suka wankemun fuska,inasharewa karyaga ina kuka nan ma wata masifarce......ina gogewa wasuna zubowa."zanci ubaki wallahi kukan ubanme kikeman dukanki nayi,ko yankar naman jikinki nake,ohhh ga mala,ika aza,ilunki ko dake nake kinaman banza."
Yafad'a cikin tsawa.....daidai sanda aka shek'e da ruwa dama kuma muna gaf da gida.
Bansan sanda wani kukan ya kucceman ba,dukewa nai nasa kaina cikin cinya naita rera abuna.......kuka nake sosai mai cin zuciya......banza yayi mun har muka iso gidan,nibanma saniba najidai ya tsaya ban d'agoba kukan kirun nakeyi.........fita yayi ruwan yafara dukanshi ya lumshe idonshi,yanajin dadinshi kamar yaita tsayuwa cikinshi har ya kare......zagayowa yayi ina nake zaune yabude k'ofar jinai kurun ya kamo hannuna nafito,rufe motar yayi yajani muna nufar cikin gida.......hannunsa cikin nawa ga ruwa yana sauka kanmu har lokacin kuka nake amman can k'asan makoshi,saboda muryar kanta ta dishe.......idona rufe yake nasa hannuna da abayata na rufe fuskata,shike yiman jagora wannan halin damuke naji tsikar jikina tayashi yarrrrr....... Sanda mukaje wajen hawan step din shiga main falon......jinai kirun an sab'eni baidirnine ko inaba sai d'akin yah meenah......idonta biyu lokacin kallonmu tayi tace"yah me yasameta"
Direni yayi kan gado yace"gatanan ki tambayeta" yafice tashi nayi nai jifa da abayata dake k'amshin turarenshi,har lokacin kuka nake sosai jin har lokacin mayataccen k'amshin baibair jikina ba yasa nahau cire doguwar rigar jiina ina cewa,
"Tsinanne wallahi sai kabar jikina,tunda banan aka haliccekaba.......ga hawaye share share.....yah meenah kallona kurun take,ganin nacire kayan ma bandaina jinshiba yasa nashiga wanka.....naita dirjar jikina saida nagaj nafito.......dariya kurun yaya meenah kemun babu sassautawa,haushinta ya kamani shiysa har nayi bacci ban tanka mata ba.

         ************
Koda yaje d'aki takalmanshi kurun yacire  ya zube ga kujerar falon su,kanshi sama idonshi kulle,iskar bakinshi kurun yake fesarwa,kasancewar wannan  dabi,arshi ce idan yana cikin halin damuwa.
Jahid daya fito wanka ya samai awannan hali,sai bai kulashi ba,don yasan halin kayanshi har yagama shirinsa  Areef nanan inda yake,karshe sallah kurun yayai yazo ya kwanta kan kujearat,daya tashi.......jahid kallonsa kurun yake don wannan ba sabon abubane wakenshi,saidai nayau yasha banban dana sauran lokutan,don Areef baya kwanciya da kayan jikinshi,duk runtsi zai canza kaya amman yau gashi ya kwanta dasu,bama manya bane masu sauk'in bacci jeans ne da t shet jikinsa,da wannan mamakin yayi bacci.


💕💕💕💕💕💕💕

Washe gari bantashi ba sai twelve,kasancewar banda lectures sai 2:00 pm Abbu nanan tunda nai wanka n shirya najena gaido Annie har take tambayata meya saman jiya taga Areef yashigo dani.
"Annie turgud'ewa nayi nazo shigowa k'ofar falo,kinsan daman wannan wajen ba,a wuceshi da sauri,sai kurun na fad'i shine ya taimakeni."
Nasan idan ba haka nace bah banda wata karyar data wuce wannan.
"Aikuwa nasani tunda nima yasha kadani,kiringa bi sannu da yarintarki karya gurguntaki,dasauki k'afarko."
"Eh naji sauk'i sosai nashafa man zafi awajen ."
Daga wajen annie wurin maah na wuce, bata falonta na wuce uwar dakarta.......maah ce zaune kan dardumar tsakar dakinta kafafunta mik'e yah Areef ne kwance kan k'afafunta, salma na gefe tana dama mashi fura,gallala nayi ina kallon ikon Allah,dukda bawani abubane  da bantab'a ganiba,amman nai zaton zuwa yanzu yah yagirma da wannan alon na yara,ai sai yabarmamu.....kamar injuya naji amman ganin duk sun ganni yasa na idasa,gefen maah na zauna ina gaidata,nacewa salma"yau bakije makaranta bane."
"Fuskar ta duk ta yamutse kamar tayi kuka,tave"wallahi banjeba yah nebaida lafiya,bazan iya zuwaba."
Kallonshi nayi idonsa rufe ruf,eyelish dinsa sun kwanta kamar na mace,
Can k'asan muryata nace"sannu yah Allah yasa Wake."
KO ma ah dake musadani banyi tunanin zatajiba balle salma dake d'an nesa damu,amman shi dake kwamce kan cinyarta rasss cikin kunnensa,yace"Ameen."
Lab'b'ansa kurun zaka gane kasan yayi magana,duk da haka ni naji jinai maah tace"baki gaidashi da jiki."
Mik'ewa nayi nace"ai nayi mashi bari nake waken Abbu kafin time yayi."
Banjira cewarta ba nafice,ina mamakin salma saboda wani ta kizuwa makaranta,nalura yanzu saboda shi kokadan bata son karatun.....wata zuciyat tace ita tasani.
Waken Abbu mu kayi lunch dina,ganin yana cikin yanayin jin dadi yasa nace"Abbu dongirman Allah kayiwa yah Arref magana yabarni nakoma hostel,wallahi sainafi jin dadin karatun kagafa wataranar har ten nake kaiwa ban iso gidaba,plsss Abbu don Allah kayi amshi magana."
Murmushi yakeyi yace"ta Alkairina kean,kindai aida yayanki kamar wani dodonki ko."
Kaina na k'asa ina wasa da yatsuna nace"Aa Abbu ba haka bane wallahi shine yake mun tsawa,Kuma ni banaso ko had'a ido mukai sai ya hararenifa,wallahi Abbu yah Areef ya tsaneni yanzu."
Girgiza kai yayi yace"Aa ta alkairi karna sake jin haka daga bakinki yayanku bazai tab'a tsanarkiba,kin kasa fahintarsa ne kisaki jikinki dashi kudawo kamar da keda shi."
Icon dandanan ya kawo ruwa,don basusan irin tsanar dayake mun ba,cikin karyewar murya nace"Abbu pls"
Yah jahid ne yashigo yace"ta alkairi ta shirya in sauketa makaranta."
Goge kwallata nayi ina gaidashi,
Abbu yake gaya mashi abunda nakeso.

Murmushi yayi yace"karki damu inhar hakan shine mafita tokiyi don koni ina baki goyo baya zaman hostel din fiye da kima,don inason ganin ta Alkairin Abbu tayi karatu sosai dazai saka tayi passing."
Murushi nayi mai kyau naji dadin kalamanshi nace shikenan zan mashi maganar inkuma baiyarda bafah.
"Abbu yace zaima yarda ai Areef nakine babu mai shiga tsakaninku ko ko jahid."
Dariya yayi yace"sosai kuwa Abbu."
Ahaka nabaro wajen natai nashirya yah jahid ya wuce dani makaranta.





Mom muhseen✍🏻

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now