_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......26
Muryarsa adake yace ma Abbu,
"Zan wuce Abbu."
Kallonsa yayi yace"sai yaushe kenan."
Agogonsa ya kallah yace"wallahi bansan lokacin ba anma ina kyautata zaton zamuyi aikin 2month a paris,kafin nan mu wuce japan muyo 2 month da ko sati biyune,banda tabbacin zamu dawo kan lokaci gaskiya."
Shiru duk akai anan na fahimci tafiyace zaiyyi,kuma bazai dawo nan kusaba.Dady yace"maganar salmar fah."
Fuskarsa na kalla yasake d'aureta tam,yace"Dady munyi maganar daga baya,jahid muje kasaukeni time na tafiya."
Duk tashi akai don yi mashi rakiya zuwa mota,da alama akwai abunda yafaru kowa naga fuskarshi babu dad'i.ina tsaye yaketa sallama da kowa ina gefe guda na rungume hannu.
Maah rungumeshi tayi harda kwallanta,wai zatai kewarshi murmushi nai ina jinjina kaunarta tsakaninta dashi,kamar bazai bar jikintaba haka yaisa ga Annie itama ya rungumeta,su Anty shida da su yah jahid namai dariya wai kuka zai,ina ganin sadda ya hararesu sannan ya mikama yah shahid hannu sukai musaba ha,ya kalli yah meenah yakama kunnenta yace"karatu tukuru."
Duk dariya akai masu salma ya mik'ama hannu,isowa tayi yajata gefe bansan me yace mata ba,naga dai tana d'aga kai sannan ya shiga mota.
Abbu ne yace mashi"Areef ka gaisa da kowa banda ta alkairi,laifin me tayi maka haka."
Shafa kanshi yayi yana murmushi baice komiba,Abbu ya juyo ya yafitoni da hannu.
Jikina asanyaye na nufi inda yake,i wonder banji tsoron da nake jiba idan na tunkareshi,isa nai gani nai yabud'e bayan motar yace"shiga."
Kallon Abbun nake nama rasa mezance mashi daga man kai naiyayi,dole nashiga Anty shida ma tataho "Abbu inazuwa."
Bai musuba tashiga tana dariya,yah jahid na satar kallonta ta mirrow jan motar yayi muka fita,yah jahid da Anty shida kurun suke firarsu anman ni bakina ma yayi nauyi,waimeke faruwane yau gani ga dodona amman narasa inda tsoran ya tafi,yanayin dana shekara uku ko nace hudu banjiba shine nakeji,duk wani yanayi da da nake tsintar kaina cikinsa idan ina tare dashi yadawo,mekenan mamaki da al,ajabi sun rufeni.Har mukaje filin jirgin bance komiba,yah jahid da anty shida suka fita can wajen zama suka samu suka cigaba da firarsu,shiru motar tayi na kasa yin magna gashi lokaci yana ta tafiya,don nasan karfe d'aya zasu tashi,gashi shabiyu da rabi.
Ganin yak'i tankaman don yadda duk yabi yasha mur natabbata in nabiyeshi har yatai bzai ceman komi ba,cikin sanyin muryata nace"yah kayi hkr kazo baka saman ba wallahi............"shot up."
Ba shiri naja bakina nayi shiru.
Cikin muryarsa dakakka yace batare da yajuyoba "Aure dai kikeso dai ko,to ki kwantar da hankalinki nasanar da Abbu kafin nadawo ya aurar dake,idan yaga dama shi masoyin naki sai yabarki ki k'arasa."
Atsorace nake kallonsa daga inda nake zaune,zuciyata bugawa take babu kakkautawa,
"Yah dongirman Allah kayi..........."karki sake kiyi man magiya,kenan don uabanki har kinyi girman kiyimum karya don kije ki had'u da saurayi,to gara da Allah ya nuna man,insha Allah end of this month keda salma duk zaku idashi gidajen mijinku,tunda har taurin kanku yakai haka ga yayarku nan tunda tafara karatunta ba,asameta da wata matsalaba harta gama saiku *kwalaye daku berori da bakusan kankuba.* zakugane bakuda wayau badai aure kukeso ba.
Ai bansan sadda kuka ya kubcemun ba ina kukan ina cewa"yah kai mun rai.......inkika sake magana makeki zanyi fita anan sakara kawai."
Dana zoyin mgana sai ya kwatsa man tsawa duk yadda naso yasaurareni abun yaci tura,,.
Gashi bakina yakishiru inacewa"wallahi ni banda saurayi Allah yagani ni banyi komiba karatuna nake yadda akasani,shine zakace aimun aure wallahi banso inkuma akayishi saina gudu wallahi........jinai kurun ya faskeni da mari.
"Nikike ma musu ni zakiyiwa gardama,khairat duka nawa kike atafin hannuna fa kika girma,karya zan maki kina nufin kocikin biliyoyin mutane kimashiga bazan shaidakiba,balle wajen da babu kowa.
Uhmmm yayi kiyi duk abunda zakiyi intakama kikashe kanki amman tabbas Aurenki da............kasa anbatar sunan yayi yanajin kirjinsa yana duka,zuciyarsa tana zafi,idan kakalli idonsa zakasan zafin da yakeji ga ranshi.
"Fitarmun anan karkija nayi kasa kasa dake awajen anan."Kuka nake wanda bazan iya tuna lokacin da nayi shiba,haka nafito jikina yana kerma kafafuna sun kasa d'aukata,can gefe nasamu na durkushe ina cigaba da kukana mai cin xuciya.........jinake kamar zan sike ni za,ama aure saboda nayi me kawai don na ansa gayyatar malamina,banyi iskanciba banyi fasikanciba babu abunda aka kamani dashi na haramci shine zasu tsigeni daga karatun da nake so fiye dakomi...............kiransu aka farayi na minty biyar har akafara sanarawar rufe jirgi......inanan durkushe kuka kurun nakeyi.
Taku naji abayana ahankali kamshin sa yna sake nufoni,har sanda ya tsaya gabana,durkusawa yayi ya d'agoni tsaye kokrin cire hannuna yake ina bige hannun nashi dake tab'ani,don wani irin haushin sa nakeji,hakan bai hanashi son ganin na bude fuskataba,karshe dole nasaue hannun ina shashshekar kuka idona rufe,duka hannayena ya rik'e da hannu guda dayan kuma yadago hab'ata,kada kaina nayi yasake juyo da fuskar tawa gabanshi,uffan baice ba illa iyaka sakin hnnuna yyi yasaka handchif yana tsane mun hawayena,amman still wasuna biyo baya.
Jinai wani irin feelings ya taso mun form some where,wanda bazan mance iri a ba ranar daya daukan yakai har daki.........tun daga yatsan kafata nakejin wani yanayi har cikin jinin jikina,numfashi nake saukewa zuwa yanzu kukan ya tsaya,saidai ajiyar zuciya kuma har lokacin banbude idonaba,kallon fuskata kawai yake jinai anata neman shi jirgi zai tashi amman shinko ajikinsa,sai lokacin na bude idona ahankali idonsa ya sauya launi yakada yayi ja,amman hakan bai hana wani abu fitowa ba yana shiga cikin nawa idon.
Jinai kafafuna bazasu iya daukata ba,silalewa zanyi kasa yayi azamar rikeni,saidai najini yayi mun wata kyakkyawar runguma.
Fashewa nai da kuka wanda yafi nafarko,bubbuga bayana yake yakasa magana,injiyo yadda zuciyar sa ke duka dagoni yayi yasunbaci goshina,kuncina da tafin hannuna.
Saida na rutse idona kafin ya yimun rad'a ga kunne *INA MAKI FATAN ALKAIRI MATAR MUHAMMAD KASEEM,SAI WATARANA BAZAKI SAKE GANINA BA,KIYI HKRI DANI MUN HARAMTA GA JUNA HAR ABADAN,BAZAN IYA KARYAWA MAAH ALKAWARINTA BA.ZANJE NAYI JINYAR XUCIYATA KIKULA DA KANKI AND PLSSSS FORGET ABOUT AREEF FAROUK,GOOD BY UMMULKHAIR.*Mom muhseen✍🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/322019083-288-k243490.jpg)
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fiksi Penggemarlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda