_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......7
Jingina nayi da k'ofar toilet d'in Ina sauke numfashi k'asa k'asa, jikin k'ofar yazo ya Jingina bayan sa Shima, murya can k'asa k'asa yake magana, tayi rauni sosai sai kayi tunanin kuka yake.
"zamu tafi *sweetheart* saidai abun haushin zamu rabu kina fushi da Ni,pls kiyi hakuri ki fito ko dukana kiyi Wanda zan ringa tunawa da shi."
Kuka ya kucce mun mai tab'a zuciya,kamar numfashina zai fice runtse idonsa yayi yana jin babu dad'i, duk yadda yaso yasake ganinta k'iyawa nayi, haka yafita jiki babu kwari........daman shikad'ai akejira gab'a d'aya gidan aka tafi masu rakiya banda Maah da Khairat.
Ina bayin nan har suka tai saida nasha kukana kamar ba gobe sannan nafito daga bayin,daidai shigowar Maah d'akin.
Zama tayi bakin gadon mu tana kallona bata dai ce komi ba har na gama shiryawa, nazo nayi walha da nake yi na gama sannan na kalleta nace.
"Maah ko wani abun zanyi naga tunda kika shigo baki ce komi ba."
Wani kallon banza tayi mun kafin tace mun, in biyota d'akinta.
Jikina yayi sanyi Allah yasa ba laifi nayi mata ba, Ina tsoran fad'an ta Maah babu sauk'i indai wajen fada ne,duk na tsure tsoro nake kar ta dokeni gashi mai cetona bainan,don wata sa,in idan na mata taurin kai jibgata take kamar jaka, sai shine zai kwaceni.
Zama nayi k'asa wajen k'afafunta, na sadda kaina kamar munafuka.
Sunana ta kira.
" *UMMUL KHAIRI*"
D'agowa nai na kalleta nace,"Na,am Maah."
"Miye matsayina wajenki."
"Maah ke mahaifiya tace."
"idan ance mahaifi me ake nufi kenan."
"ana nufin wanda ya yi silar kawoka duniya, kuma wanda nauyin kulawarka ci da sha da sutura suka rataya akansu, idan baka lafiya akaika Asibiti tarbiyyarka tana kansu."
Wani dad'i ya kama maah lallai duk cikin yaranta babu kamar Khairat wajen komi, Amman sai ta sake Shan mur tace.
"sab'amasu yana nufin mekenan."
"yana nufin ka sab'ama Allah [S W A] kuma duk mai ja dasu bazai tab'a ganin daidai bah."
Jinjina Kai ta sake yi sannan tace.
"madallah da malamin islamiyyarku,tunda har duk kinsan wad'annan bazan sha wahalar yi maki bayani bah, kallani nan Khairat."
Banyi musuba na d'ago Ina Kallonta ina ganin wasu maganganu masu tsananin nauyi cikin idonta, jinai taciga da cewa.
_*"matsayina na mahaifiyarki, na umurceki da cire duk wani Abu dake ranki akan yayanku AREEF,sannan na haramta Aure tsakaninki dashi har gaba da abadan, duk Yarinya ce ke nasan kinsan me ake nufi da haramci,to na haramta maku junan ku, kuma muddin kika take doka ta wallahi ummul khairi BAN YAFE MAKIBA."*_
Iya dauriya nayi bansan ni d'in jaruma ce ba sai yau, ilahirin jikina rawa yake amman nadanne na k'i bari Maah ta gane, idona k'em akanta nace.
"insha Allah nayi maki wannan alkawarin,saidai tambayar da nake da ita itace..........."
"Bana sonjin tambayar,duk motsinki na sani Khairat karkiga ina nuna halin ko in kula akan lamarin ku, wallahi kar nake kallonku, don haka idan na sakejin kun samu sab'ani da juna keda salma billahil azim zanar tsiya zan maku,kiyi k'ok'ari idan ta dawo ku sasanta kanku,sannan kan karatunki, wallahi Khairat idan kika sake barin damuwa tayi gala ba kanki nida kene."
"don haka idan kunne yaji..........
Kaina k'asa Nace,
"jiki ya tsira."Tace,
"good girl,sannan kidawo da walwalarki, bana son wannan d'ari_d'arin da kike bance kuma kidaina yi masa magana ba,ko kuyi fira, Aa zakuyi duk wannan amman muddin kika sakejin wani yana yi kanshi.........basai na ida ba kinsan sauran tashi Kibani waje."Jiri ke neman kada ni na dafa bango zan fita,sai kuma na juyo Nace,
"Maah."kallona tayi alamun tana jina.
Cikin karyewar murya kad'an ya hana kuka na bayyana nace,
"Maah, don Allah kiyi mun hakuri bazan iya cigaba da magana mai tsawo dashi ba,idan nayi hakan bazan iya hana zuciya ta jin wani abuba, kibarshi murinka gaisawar ya isa,sannan kiman afuwar yau bazan iya warware wa lokaci guda ba,amman namiki alkawarin bazan Kai lokacin da salma zata dawo ahaka bah.......plss Maah."
Wani marayan Tausayin y'ar tata ya rufeta,jawoni tayi ta rungume,wanda ba zance ga tsawon lokacin da Maah ta d'auka rabon da ta rungumeni.
Cikin muryar lallashi tace,
"nayi maki wannan uzirin Khairat,badan na cuta maki nai hakan ba, gata ne nayi maki, ko ince nayi maku keda yayyenki, na kausasa kalamaina ne don na tsorata ki akan abunda kikeji kan AREEF,amman bazan iya hana Allah ikonsa akanku ba, kiyi k'ok'arin kiyayewa kinjiko ta alkhairin Abbunta.Wannan kalamin yasa nasamu natsuwa, nasake mata alkawarin kiyayewa,k'arshe ajikinta nayi bacci, ta kwantar dani ta fita................
Mom muhsen ce
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fiksi Penggemarlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda